TASKAR AJALI!!!
Littafi Na Daya (1)
Part A
BUDUWARCE 'yar kimanin shekaru goma sha tara,ma'abociyar kyawu irin wanda a ganin farko zata ruda dukkan 'da namiji dayayi arba da ita musamman a cikin irin wannan
shiga da tayi ta ratso tsakiyar kasuwa.Riga da wando ne na fatar damisa matsatstsu ta sanya wadanda suka baiyana
dukkan kyakyawar siffar
jikinta,kuma a bayanta ta
ratayi wata zabgegiyar takobi.Kallo
daya zaka yiwa
wannan budurwa ka tabbar da
cewa jaruma ce
domin tana da kira irin ta
sadaukai.Ta daure dogon
gashin kanya mai kyalkyali ya zuba
a bayan
kafadarta har bisa
mazaunanta.Tsananin kyawunta
da kwarjinita ne yasa gaba dayan
jama'ar dake cikin
kasuwar suka tsayar da harkokinsu
suka zuba mata
na mujiya kai wasu ma yan
kasuwar basu san
sa'adda suka rinka tsallake hajarsu
ba suka rinka
binta a baya domin ta tafi da
imaninsu.Bawai maza
ba hatta mata masu siye da masu
siyarwa watsar da
komai sukayi suka rinka bin
wannan bakuwar
budurwa a baya don kawai su san
ko ita wacece da
kuma abinda ya kawo ta cikin
wannan kasuwa.Dama
a guje wannan budurwar ta fado
cikin kasuwar
sannan ta tsaya cak ta dubi gabas
da yamma kudu
da arewa ga dukkan alamu dai
wani ko wata ta biyo
a fusace tane neman inda ta shiga
amma bata gani
ba,don haka sai ta sake nausawa
cikin kasuwar da
sauri ta rinka leke cikin rumfuna da
lunguna lunguna
na cikin kasuwar.Dukka da cewar
taga jama'a sun
biyo bayanta da yawa ko kada bata
damu ba,itadai
kokarinta shine taga wanda take
nema ruwa a jallo
amma ko alamunsa bata gani
ba.Al'amarin daya
dugunzuma hankalinta kenan.Koda
taga ta karade
kasuwar gaba dayanta har tsawon
kusan sa'a daya
da rabi ba labari kuma jama'a sunyi
cincirindi a
bayanta sai ranta ya baci ainun
bata san sa'adda ta
yunkura ba ta kurma uban ihu mai
tsananin
firgitarwa tane mai zare
takobinta.Kafin kace wani
abu tuni an tattake kayayyakin
jama'a tamkar yaki
akeyi kuma kowa ya watse
kasuwar tayi tsit tamkar
mutuwa ce ta gifta.Tsananin shirun
daya wanzu ne
yasa jarumar ta jiyo sautin
numfashin mutum a cikin
wani dogon durum na karfe wanda
ke cike da
ruwa.Saidai wannan ruwan durum
ruwane na
kazanta wanda ake wanke
kwanukan abinci dashi a
kusa da rumfar da ake siyar da
abinci.Koda jarumar
ta jiyo numfashin mutum a cikin
wannan darum sai
ta daka tsalle sama ta dira akan
durum din tana mai
raba kafafunta a kansa duk da
cewar bakin durum
din siriri ne matuka amma ko
girgidin faduwa batayi
ba.Kawai sai ta sunkuya ta tsoma
hannunta cikin
ruwan take taji ta kama gashin
mutum ai kuwa sai
ta fincikoshi sama ya na kwala ihu
sakamakon
tsananin zafi da zugin da yaji.Take
ta kwalashi a kas
yana jike sharkaf ya sake kurma ihu
a lokacin yaji
kamar kashin bayansa ya karye ba
wani bane face
matashin saurayi dan kyakyawa
wanda shekarunsa
bazasu haura ashirin da uku
ba.Koda wannan
saurayi yaga wannan jaruma ta
dirfafoshi rike da
takobi tsirara sai ya zube kasa a
gabanta ya kama
tuba yana cewa tayi masa rai.A
lokacin da jikinsa ya
kama kyarma a daidai wannan
lokaci ne mutanen
kasuwar suka fara dawowa,nan da
nan suka taru
wajen sukayi musu kawanya suna
kallon abinda ke
faruwa cikin al'ajabi.Budurwar
ma'abociyar kwarjini
ta iso daf da saurayin ta dora kaifin
takobinta akan
wuyansa take gumi ya karyowa
saurayin sa'adda yaji
kamar ya saki fitsari a wandonsa
sannan ta dubeshi
tace,ina abinda ka sata a cikin jakar
guzurina?Jikin
saurayin na kyarma ya zura
hannunsa cikin aljihun
wandonsa ya fiddo wata guntuwar
jemammiyar fata
wacce ke nannade yamika
mata.Cikin hanzari
budurwar ta amshe ta bude jakar
guzurinta tasa a
cikin sannan ta cire kaifin takobinta
daga kan wuyan
saurayin koda ganin haka sai
saurayin yayi doguwar
ajiyar zuciya kuma fuskarsa ta
fadada da murmushin
murna bisa ganin cewa jarumar ta
kyaleshi bata
kashe shi ba kawai sai ya mike
tsaye zumbur ya
juya da baya ya falfala da gudu
izuwa wani bangaren
daban na kasuwar yana cikin gudu
ne yaga wannan
budurwa jaruma tsulum a gabansa
cikin tsananin
kaduwa yayi tirjiya a gabanta ya
dubeta cikin alamun
tsananin tsoro yace,tundai na baki
abinda na satar
miki kiyi mini rai don girman
iyayenki kada ki kashe
ni.Koda jin haka sai jarumar tayi
masa murmushi
lokaci guda kuma ta murtuke
fuskarta tace,ba
kasheka zanyi ba amma dole ne ka
amsa wadansu
tambayoyi daga gareni tunda kana
biye dani tun
daga birnin Misra har izuwa nan
birnin
Yamein,kasashe uku muka ketare
ta cikin teku duk
jirgin da nashiga kaima saika shiga
ashe akwai
abinda kakeso a wajena?Ina da
kudade masu yawa
a cikin jakar guzurina amma ko
dinare daya baka
dauka ba sai ka dauki abinda yafi
dinaren daraja
kuma yafu duk wata dukiyar a
wannan duniya.Dole
ne nasan dalili kuma nasan wanda
ya turoka
watakila sanin hakan ya kaini ga
samun nasarar
gano inda nake nema.Koda wasa
kada kayi tunanin
guduwa daga hannuna ko kuma
kayi mini karya bisa
abubuwan da zan tambayeka
domin yin hakan
daidai yake da siyar da
ranka.Kasani zan iya
shaftare makogwaron bil'adama da
kaifin takobina
kamar yadda kullum ake yanka
kaza ko naman miya
a kasuwa,ni da kai duk nasan cewa
muna jin yunwa
don haka ka biyo ni muje mu nemi
abinci muci
domin mu sami nutsuwa.Koda
gama fadin hakan sai
jarumar ta juya ta nufi cikin kasuwa
cikin razana da
dari dari saurayin ya bita a baya
kamar ace kyat ya
saki gudawa a wando,su kuwa
jama'ar kasuwar
wannan karon sai aka rasa wanda
zai sake bin bayan
wannan budurwa saboda an
razana da ita ainun bisa
ihun da tayi a wancan karon wanda
ya zamo
sanadiyar tarwatsa kasuwar gaba
daya.Kai tsaye
jarumar ta nufi rumfar wata mata
mai siyar da abinci
jama'a suka rinka ratsewa
¶Abubakar Haleefah Physicist¶
suna bata hanya har suka shiga
cikin rumfar ita da
saurayin suna shiga sai gaba dayan
jama'ar dake
zaune bisa kujeru suna cin abinci
suka tarwatse
suka gudu suka bar abincinsu
alhalin basu gama ci
ba,wasu ma anan suka bar
takalmansu da yan
kayayyakinsu.Ita kuwa matar mai
rumfar sai ta
durkusa kasa bisa guwiwowinta a
gabanta.Matar
tace kiyi mini zan baki gaba dayan
cinikin yau.Koda
jin haka sai jarumar tayi sauri ta
kama kafadun
matar ta tashe tsaye ta dubeta
cikin alamun
tausayawa tace,ni ba yar fashi bace
abinci mukazo
mu siya muci kuma sauran
kwastomomin kima da
suka gufu basu biyaki kudade ba
sakamakon firgita
dani zan biyaki kudin abincinsu,ki
kwantar da
hankalinki ni ba mai cutarwa
bace.Koda gama fadin
hakan sai Jarumar taje ta zauna a
kan wata kujera
dake karkashin wani tebur mai
kujeru biyu
kacal,shima saurayin sai ya zauna
tare da ita amma
har a sannnan akwai alamomin
tsoro a tare
dashi.Mai abincin ta dubi Jarumar
tace,ya shugabata
wane irin abinci zan kawo miki?
Jarumar tayi
murmushi tace suna na Yazirina bin
Salmara karki
kara bani girma domin nida sarauta
ko wata
daukaka,shinkafa da kaza zaki
kawo mini amma shi
abokin tafiyar tawa bansan abinda
yake so yaci
ba.Cikin nutsuwa mai abincin ta
dubi saurayin tace
kai kuma fa?Saurayin yayi
murmushi cikin yake yace
suna nan Mujahid Ibini As Sudusi
nima ki kawo mini
irin abincin da abokiyar tafiyata ta
bukata.Koda jin
haka sai Jaruma Yazirina ta yiwa
Mujahid wani irin
murmushi na mugunta tace wato
kaga banza ta fadi
ko zaka kwashi bati shine kai ma
kace a kawo maka
kaza to kasani bayan cin kaza
akwai cin kwakwa a
gaba.Cikin razana Mujahid ya zaro
idanu yace me
kike nufi da cin kwakwa?Yazirina
tace karka damu
lokaci zai baka amsa.Nan da aka
kawo musu
shinkafa da kaza dafaffiya kowa
farantinsa daban
kuma aka kawo musu ruwan inibi a
cikin tambula da
kofuna guda biyu suka kama kintsa
cikinsu.Muhajid
ya bude cikinsa yayi ta zuri har
saida ya koshi yayi
gyatsa amma duk da haka bai rage
ko fiffiken kazar
ba duk da cewar kazar katuwa ce
sosai,sai mutum
yana da matukar cin abinci yake iya
cinye rabin
wannan kaza.Ita kuwa Yazirina
kaso daya cikin kaso
hudu na kasar ta cinye shinkafar
ma cokali uku tayi
kawai,itama kanta tayi mamakin
yadda Mujahid ya
cinye gaba dayan abincinsa.Nan
take Yazarina ta
bude jakar guzurinta ta fiddo da
kudi ta biya abincin
da suka ci ita da Mujahid sannan ta
biya na
kwastomomin da suka gudu kamar
yadda tayi
alkawari,kawai sai ta dubi Mujahid
tace zo mu
tafi.Maimakon Mujahid ya bita da
sauri sai ya tsaya
yanason ya tambayi mai aminci
yace ta bashi wani
abun daga cikin kudin da Yazirina
ta bata,kawai sai
yaji Yazirina ta kamo wuyan rigarsa
ta baya ta
fincikoshi.Ba shiri ya bita a baya da
sauri suka fice
daga cikin rumfar,Koda ganin haka
sai mai abinci ta
daka tsalle sama ta kama rawa
saboda murna bisa
ganin cewa kudaden da Yazirina ta
bata yau yakai
adadin cinikinta na mako
guda.Al'amarin daya baiwa
Mujahid mamaki kenan ya dubeta a
dan tsorace
yace wai shin ina kike son zaki kai
ni ne?Ni fa ban
san ko ina ba a garin nan kuma
bansan kowa
ba.Koda jin haka sai Yazirina ta juyo
a fusace ta
cakumi wuyan rigarsa da hannu
daya ta dagashi
sama sai gashi kafafunsa na wutsil
wutsil a sama
tamkar sillan kara ta daga,sannan
ta daga kanta
sama ta dubeshi tace,Kai tsohon
barawo kada ka
rainan hankali,gaba daya kasashen
dake nahiyar nan
kasan cikinsu da wajensu kamar
yadda kasan
yunwar cikinka saboda
kwarewarka a iya sata.Kana
zaton bansan ka bane?Kaine ka
sace hular sarautar
Sarki Atman Bin Ka'ab na birnin
Kisra.Kaine ka sace
dukiyar attajiri Katadata bin Al
Aswad na birnin
Sham kuma kai ne ka sace lemar
sarauniya Iklaira
bin Aslam ta birnin Hindu kuma
Boka Kaisu Bin
Alkama ya baiwa dukkan
wadannan abubuwan
uku,ya biyaka ladanka yau kusan
shekara biyar
kenan kana aiki a karkashinsa yana
baka sa'a akan
sana'arka ta sata.A halin yanzu duk
fadin duniya
babu wani barawo daya kaika
shahara,dauka da tarin
dukiya.Tana gama fadin hakanne
sai ta dire shi
kasa.Lokacin da Jaruma Yazirina
tazonan a
jawabinta sai gumi ya tsatstsafowa
Mujahid saboda
tsananin mamaki da firgitar da yayi
saboda yanzu
ne ya tsorata sosai da Al'amarin
Yazirina ya gane
cewa tabbas ta cika shu'umar
bokanya domin in
bata kasance haka ba babu yadda
za'ayi tasan duk
wannan sirri nasa....
08161272634
TASKAR AJALI.1
LITTAFE NA DAYA
PART B.
type AA MISAU.
POST SULEIMAN ZIDANE KD.
WHATSAPP 09064179602

ta baya ta
fincikoshi.Ba shiri ya bita a baya da
sauri suka fice
daga cikin rumfar,Koda ganin haka
sai mai abinci ta
daka tsalle sama ta kama rawa
saboda murna bisa
ganin cewa kudaden da Yazirina ta
bata yau yakai
adadin cinikinta na mako
guda.Al'amarin daya baiwa
Mujahid mamaki kenan ya dubeta
a dan tsorace
yace wai shin ina kike son zaki kai
ni ne?Ni fa ban
san ko ina ba a garin nan kuma
bansan kowa
ba.Koda jin haka sai Yazirina ta
juyo a fusace ta
cakumi wuyan rigarsa da hannu
daya ta dagashi
sama sai gashi kafafunsa na wutsil
wutsil a sama
tamkar sillan kara ta daga,sannan
ta daga kanta
sama ta dubeshi tace,Kai tsohon
barawo kada ka
rainan hankali,gaba daya kasashen
dake nahiyar nan
kasan cikinsu da wajensu kamar
yadda kasan
yunwar cikinka saboda kwarewarka
a iya sata.Kana
zaton bansan ka bane?Kaine ka
sace hular sarautar
Sarki Atman Bin Ka'ab na birnin
Kisra.Kaine ka sace
dukiyar attajiri Katadata bin Al
Aswad na birnin
Sham kuma kai ne ka sace lemar
sarauniya Iklaira
bin Aslam ta birnin Hindu kuma
Boka Kaisu Bin
Alkama ya baiwa dukkan
wadannan abubuwan
uku,ya biyaka ladanka yau kusan
shekara biyar
kenan kana aiki a karkashinsa yana
baka sa'a akan
sana'arka ta sata.A halin yanzu duk
fadin duniya
babu wani barawo daya kaika
shahara,dauka da tarin
dukiya.Tana gama fadin hakanne
sai ta dire shi
kasa.Lokacin da Jaruma Yazirina
tazonan a
jawabinta sai gumi ya tsatstsafowa
Mujahid saboda
tsananin mamaki da firgitar da
yayi saboda yanzu
ne ya tsorata sosai da Al'amarin
Yazirina ya gane
cewa tabbas ta cika shu'umar
bokanya domin in
bata kasance haka ba babu yadda
za'ayi tasan duk
wannan sirr