TOP 10 HAUSA NOVEL WEBSITE
Wadannan jerin sunayen shafuka ne sanannu da ke rubuce-rubucen littafan hausa a yanar gizo, kamar haka:
1.    http://benaxiromar.com shafi ne da ya shahara wajen rubuce-rubucen kagaggun labarai wanda marubuciyar mai suna Benazir Umar ke fitarwa daga cikin irin hikimar da Allah Ya yi ma ta domin itama ta bada nata gudummawa a cikin al’ummarta da kuma harshenta na hausa. Ga masu sha’awar saduwa da ita kuma zasu iya tuntubarta ta facebook dinta ta wannan adireshi https://web.facebook.com/babubakarumar?_rdc=1&_rdr
2.    www.hauwajabo.blogspot.Com ko www.jabohauwa.WordPress.Com ko kuma http://hauwajabo.over-blog.com/  wadannan shafukan sune wadannan mallakar Hauwa M. Jabo, Hauwa’u macece mai kamar maza wajen ganin cewar ta bada gudummawarta ga al’adarta da kuma harshenta, bazan manta ba lokacin da take karantu a Iraq tana nuna min irin sha’awarta a fannin rubuce-rubuce, Hau’wa Jabo ta gida shafukan don ganin cewa ta farantawa masoyanta tare da nishadantar da su daga cikin irin hikimomin da Allah Ya bata. zaku iya tuntubarta a shafinta na facebook Authy Hauwa M.  Jabo
3.    http://sadijegal.blogspot.com.ng/ ko https://sadiyajegal.wordpress.com/ Sadiya Labaran Jagal marubuciya ce da ta kware wajen rubuce-rubuce a shafin yanar gizo inda itama ta nuna bajintarta ta bude shafi domin bada nata gudummawa a cikin harshenta  
4.    http://aishaummi.blogspot.com.ng/ Aisha Ummi itama jarumar gaske ce wajen jajircewa ga bada gudummawarta ga harakar rubuce-rubuce da kuma kokarin nuna irin nata hikima da hazaka ta fannin rubutu a shafukan yanar gizo.
5.     http://novels24.blogspot.com.ng/ wannan shafi shafine da wata mawallafiya ke rugurguza da bararraje irin nata fasahar rubuce-rubuce a cikinsa marubuciyar ta kware sosai wajen nishadantar da masu karatu haka kuma Nadiya Tafeeda tana da kokari wajen bada gudummawarta ga al’adar hausa da kuma hausawa.
6.    https://www.okadabooks.com/ Okadabooks shafi ne da aka kirkira domin saukakawa marubuta da masu karatu inda zasu iya sayar da littafansu a cikin sauki sukuma masu sha’awar karatun littafai zasu samu damar bincikar irin littafin da suke bukatar karantawa a saukakake, babu shakka wannan shafi ya taimaka sosai wajen ganin marubutan mu hausawa sun bada nasu gudummawa a cikin cigaban yaduwar hausa a cikin duniya.
7.    www.lafazinso.tk wannan shafi, shafi ne da ya amsa sunansa lafazinso domin shafi ne da aka sadaukar dashi a sanadiyar soyayyar inda shafin ya kunshi kalaman soyayya, maganganun hikima kan so, wakokin soyayya, da kuma littafan soyayyah. Za a iya saduwa da su shafinsu na facebook www.facebook.com/lafazinso ko twitter @lafazinso
8.    www.sharhamakinfo.com wannan shafi, an ginashi tun a shekarar 2009 daga Shahararren Marubucin nan mai suna Sharahbil Muhammad Sani haka kuma anyi bajikolin littafan soyayya a cikin shafin tare da wasu darrussa wanda daga baya shafin ya canja salo zuwa wani kashe.
9.    Al-haq elibrary  wannan shafi shima ya samu tubali ne daga Sharahbil Muhammad Sani inda ya ginashi a matsayin wani dakin karatun littafan addini wanda kuma ya yi shine da harshen hausa
10.  www.gidanmarubuta.blogspot.com wannan shifi an ginashi ne domin bada labaran marubuta tare da littafansu za a iya samunsu a shafinsu na facebook https://web.facebook.com/gidanmaturubuta/