KIMIYYAR NA’URA MAI KWAKWALWA

(KWAMFUTA)




















SHARAHBIL MUHAMMAD SANI
Website: www.sharhamakinfo.com  
Tel: 08103139272

Copyright © Sharhamak, 1437AH/2016CE
Hakkin Mallaka © Sharhamak, 1437AH/2016CE

Ba a yarda a yi amfani da wannan littafi ba ko wani sashe daga cikinsa ta hanyar sarrafawa ta kowace irin siga sai tare da rubutaccen sako mai dauke da kwanan wata da kuma sa hannun amincewa daga marubuci (Sharahbil Muhammad Sani).
An fara rubutawa a farkon shekarar 1435AH/2013CE an Kamala a shekarar 1437AH/2016CE

An buga a Nigeria a kamfanin
Signtech Digital Press Limited
Shago mai lamba 66/67 Daura da Nagari Science College Birnin Kebbi
Tel: 08032054591



Zanen Bango/Tsara Littafi
SHARAHBIL MUHAMMAD SANI
Ziyarci shafin mu domin amfana da abubuwa daban-daban www.sharhamakinfo.com
I-mel: sharha089@gmail.com  

 

GODIYA
Godiya ta tabbata ga Allah maɗaukakin Sarki, kuma aminci ya tabbata a bisa zaɓaɓɓen jakada, Shugaban Annabawa Muhammad ɗan Abdullah wanda aka saukar ma fiyayyen littafi (Alƙur’ani) domin ya zamo shiriya da kuma waraka ga muminai.
Yarda da aminci su ƙara tabbata a bisa iyalan gidansa, da sahabbansa, da kuma muminai har ya zuwa ranar ƙarshe.
Ina ƙara godiya ga Allah da Ya yarda Ya ba ni dama, ilmi da fahimta ta yin rubuce-rubuce da kuma samun nasarar rubuta wannan littafi mai suna “Kimiyar Na’ura mai ƘwaƘwalwa (Kwamfuta)”Iyayena ke da alhakin duk abin da na zama a rayuwa, kuma ina alfahari da su. Su suka ƙasance masu yi mini tarbiyya. Da alhakinsu ne na kai ga wannan matsayi, don haka ina roƙon Allah Ya yarda da su, Ya kuma saka musu da mafificin alherinSa.
Ina so in godewa ma fi ƙaunatuwar malamai a rayuwata, musamman mahaifina wanda a sanadiyyar shi da kuma damar da ya bani na samu cim ma nasarar samun ilimin kwamfuta a aikace. Ina miƙa godiyata ga Malam Atiku Shehu Faruq da Alkhafiz Yusuf Abubakar Suru da kuma Malam Sa'idu Muhammad a dalilinsu Allah Ya fahimtar da ni wani kaso mai yawa daga cikin yadda ake bauta maSa, da kuma kaɗaitaShi Shi kaɗai. Ina roƙon Allah Ya yarda Ya sãka musu da alheri.
Ina miƙa gaisuwar bangirma ga masõyana da irin ƙoƙarin da suke na bibiyar littafai na da kuma fatan alkhairi da nake samu daga gare ku ta hanyar saƙo, ko kira ta wayar hannu. Ba abinda zan ce da ku sai dai in ce Allah Ya sanya alkhairi a cikin rayuwarku baki ɗaya amin.
Ba zan rufe ba har sai na miƙa godiya ta ga dukan Ƴan uwana maza da mata daga iyalin Muhammad Sani Nuhu, saboda abin da suka nuna gare ni na soyayya, fahimta da kuma ƙarfafawa.
SHARAHBIL MUH’D SANI
18th Jimadal Sani, 1436AH
8th April, 2015CE

*****       *****       *****
*****       *****       *****
*****       *****       *****

SADAUƘARWA

Na sadauƙar da wannan littafi nawa ga Allahu Subuhanahu Wata’ala da kuma shugaban halitta Muhammad ɗan Abdullahi, (Tsira da aminci su ƙara tabbata a gare shi, tare da iyalan gidansa da sahabbansa da kuma mabiya tafarkinsa har ya zuwa ranar hisabi). Tare da fatar Allah Ya sanya ma wannan littafin nawa albarka, ya zama mai amfani a doron ƙasa, Ya kuma sanya wannan kyakkyawan aiki a mizani na lada gareni, amin.



*****       *****       *****
*****       *****       *****
*****       *****       *****