Kwana Ashirin Da Daya
Yarinya ce kyakkyawa ke tafiya akan
hanya, yarinyar wacce taci sunanta Hanifat, tabbas idan kagan ta zakace da ita
‘yar asalin larabawa domin tin gurin tsarin diresin ta bambanta da sauran mata
‘yace mai tsantsan ladabi da biyayya a gun nagaba da ita.
Yarinya
ce mai yawan hakuri da kuma tawali’u ga dukkan abinda ya faru da ita ‘yace mai
tausayi ga kuma rikun amana, agurin kyawtawa iyaye kuma ba sai nace komai ba.
“Yan Mata Jimana, ko bakya jina ne? ki saurareni kiji me nake
fada” a dai-dai wani gungu ne na gayu ta iso, da yake na sanarda ku cewa
‘yace mai tarbiyya sam bata kula suba. Ganin hakan Gayen ya tashi a inda yake
zaune ya bita ya cigaba da surutan sa, ita kuwa sam bai ishe ta kallo ba.
Hanifat ke ce wa, “Dallah malam kayi hakuri, idan har kana so
kayi magana dani ba akan hanya ya dace da ka tsaiyar dani ba, idan har kai mai
mutincine ta kuma lura”
“To na naji amma naso na san sunanki” Fadan Musbahu ke nan
Hanifat ta tambeshi tana mai cewa, “Sunana kuma?
Musbahu ya ce, “Eh mana”
Dawane dalilin kuma kake neman sanin sunana? Samira ta ce
hakan.
Musbahu ke cewa, “ban gane ba, eh to naji bara kiji dalilin”
Dan Allah kayi hakuri baran tsaya ba, kuma Dan Allah kayi
kadaina biyana hakanan” Kaji ‘yar digan mutin ci Samira kenan.
“Haka kika ce? Bamatsala ni zan koma sai wani karon. Bye for
you”. Musbahu ke wannan zancen agareta.
Ya
tafi abinsa da ficewan sa, ya garzaye sai gun abukansa. “Musbahu ya
akayine”?ba asami nasara bane”? Ishaq ya ce hakan. “Babah kawai share,
wallahi ni ban taba haduwa da ‘ya dibgaggiya kamar wannan yarinyarba, to wazata
munawa cewa ita ustaziyace?, ai wannan zancen kawaine wallahi” Ishaq ya
bude bakin sa yana cewa, “Musbahu karka damu ai wannan ba wani abu bane, Just
kept silent don’t worry, Insha Allahu za ka ga me zai faru da ita” “Haba Broz
gaskiya kake fada kuwa? Duk da ya ke nasan kai bakkada wasa wallahi.Fadan
Musbahu kenan. Nan ta ke suka lale gaba dayan su suka wace a dabar.
BAYAN WATA DAYA, “Yaro! Dan Allah zo na aika ka agidan nan, aika Yaron
keda wuya, zance da ku tin yaron bai fito ba, sai ga Mahaifin Hanifat ya
fito. Musbahu ya gurfana yana mai cewa, “Baba banka da wuni, ina fatan kuwa
lafiya” Mahaifin nata ya amsa masa da cewa, “Lafiya kalau wallahi, amma daga
ina haka; Musbahu ya amsa ya na cewa, “Eh! Dama na ga ‘Yar gidan ka ce, sai
naga abin da yafi da cewa na zo na tarar da kai na sanar da kai.
Faman susan kai ya ke idan kaganshi kace da gaskiya ya ke yi.
Mahaifin nata hakan ya matikar faran tar da ransa, bashakka da kaga wannan
tabbas ne kabashi shaidan cewa dane mai halin kirki, dane kuma Nagari, saboda
irin halayen sada suka nuna azahiri.
“Da yake dai ban tambiyika sunan naka ba, Mahaifin Hanifat ya
ce hakan. Sunana Muh’d Awwal fadan Musbahu ke nan, kai Allah ya saukake mana
idan kaga mutum azahiri zakace tabbas na Nagari ne amma ina ko me yake nufi
Allah shine masanin wannan, amma muzuba kawai mugani shine abin da zai iya sa
mu fahimci ma’anar da yake acikin zuciyar sa.
Lallai Muh’d Awwal… eh! amma kaganta ne? ku ka… kamun
Mahaifin nata ya idar da maganar sa, ya yi hanzarin katse shi da cewa, “Haba
Baba taya zanga yarinya batare da na ganka ba, ai wannan kamar ya nuna rashin
tarbiyya da kuma rashin gimamawa ga iyaye, ai hakan sam bai dace ba, har na
tsayar da yarinya akan hanya sam Baba wannan baidace agareni ba, kuma ya zamu
zubarda mutinci na iyaye da kuma zubar da mutincin kaina da nata kaga kuwa
hakan sam baidace ace kamar ni na aikata wannan ba. kasha zancen Musbahu.
Mahaifin Hanifat ya ce “Kai amma ka na da sanin ya kamata” ya sake yana cewa, “duk
da ya ke basai na tsayar da kai ina yi maka dugun bincikeba, bara na je na kira
maka ita kugaisai”. Kaji zance Mahaifin Hanifat kenan. Amma kash wani
hanzarin ba guduba Mahaifin Hanifat ku na ce daku Alh. Isma’il ya yi
kuskure Babba da ya ke sam bai kawo tinanin cewa ya tambiye shi da cewa shi dan
waye ne, amma ma’iya cigaba da muji me zai iya aukuwa nan gaba.
Bayan ya kira mar da Hanifat suka gaisa sam-sam bai yi wani
daukan lokaci ba yay mata sallama ya tafi abinsa, duk da ya ke kasan hausawa
kan ce mai lababe baya tayar da hanninsa.
Akwana a tashi, hakan ne suke a tare har soyayyar ta kai su
da dayan baya iya juriyar rashin ganin dayan dan uwan sa, soyayyar su tayi
matikar karfin gaske, zan iya ce da kai/ki Hanifat da ta zirfafa a so.
Bayan wa’ansu kwanakin masu yawan gaske, Hanifat ce ta re da
Ishaq a zaune acikin wani dan lambun gidan na su, firan na su yayi matikar
nisa, acikin firar ne Ishaq ya ke cewa, “Hanifat ina so nasanar dace da wani
abin wanda nasan ke bakyada masaniya akansa” Hanifat ta ke cewa, “Ishaq menene
kuma wanda idan gance ka da banda masaniya akansa?” “To yakan yo kisan wanda
ike a zahiri amma ai nasan bakyada masaniyar wanda ike a badini, dan haka sai
ki saurareni kawai kiji nenake nifi, ko kuma mezan fada. Hanifat take cewa, “Ina
saurara”.
Budan bakinsa ya fara da cewa, “Hanifat ina mai
sanardake cewa shi so wanda yake na gaskiya azahiri zaki iya ganewa amma
sam a ganina bada lora da irin sonda nake maki, “Ban bangane ba, kamar ya kake
nifine? Hanifat tace hakan.“Au to ke me kike nifine? Ya kamata ace kitsaya ki
saurareni mana, wani sa’ilin kya iya fahimtar maganata”. Duk dayake Hanifat
battada masaniya me yake nifi da wannan zance, amma kawai ta yimar wannan ne
badan komaiba, kawai tana sone da wasa mar da kwakwalwa ne.
Zatun shi ta dago hannu ne, nan take ya sauya maganar,
ya cigaba ya cewa, “Hanifat Kaunar ki ce tamamaye zuciya bashakka kece wacce na
baiwa amanar kaina, Hanifat ki rikani amana, karki kasance mai zubarda mutinci
na, kuma karki kasance mai zubarda soyayyata.
Bashakka ke ‘yace tagari kuma ke ‘yace wacce takasance
mai riko ga addini, ‘yace ke mai asali, ma’ana ce ‘yar jincice Nagari. Hanifat
na kasance mai baki ragamar soyayyata, kikasance mai tallafi a gareni. Kaunarki
ce kawai a zuciyata, sam-sam ni bansaka wata ‘ya mace wacce zata maye gurbinki
ba, kece kadai a gabana. Fatana kikasance mai tallafi agareni. Yake ‘yar digan
mutinci, har kullin soyayyarki dada yaduwa takeyi a zuciya bashakka kece wacce
nabaiwa rayuwa ina sonki ina kuma kaunarki har kullin kaunarki ce azuciya dare
da rana. Alokacin
da yake wannan zancen bashakka idan ka ganshi tillas ne tausayinsa ya kamaka.
Hakan ya matikar kara chusa soyayya azuciyar Hanifat gabadaya
tausayinsa ke kwararowa, ta rasa irin amsar da zata iya bashi, kawai ta yi wani
ajiyar zuci ta dan duna kanta a kasa. Jim kadan take cewa, “kar ka damu
Insha Allahu zan kasance mai share kukanka, nakasance mai riko da soyayyarka,
harkullin zankasance sanadin farin cikinka, ina sonka ina kuma kaunar ka, har
abada.
BAYAN MAKO UKU “Umma Ishaq ne yace ko zai iya ya turo Mahaifahsa?
Kusa da Umman ta take a zaune a lokacin da take wanna zance. Hanifat manyam
mata ku kunya bakyaji dan kanki kike wannan zance”.To Umma meyene na kunya
kuma?” Hanifat ta ce hakan. Mahaifiyar ta tayi murmushi ta ce, “Idan Abban ki
yazo zan sanar dashi. Murmushi kawai Hanifat ta yi.
BAYAN KWANA BIYU “Ishaq kasan meke faruwa ne? inji
Hanifat. A’a me ke faruwa kuma?Ishaq ya mayar mata da tambaya shima. “to
albishirin ka, Hanifat tace hakan. “Goro” fadan Ishaq, kasan ka aikani da
natambaya ma cewa ku zaka iya aikowa da iyayenka”. Eh! Haka ne ya akayi ne? “To
Abba ya ce ka iya turowa, abinda ya yace dama yana da niyyar yima wannan
zancen. “ko da gaske kike” “zanfada ma karya ne” amsar Hanifat kenan. A’a bance
ba.gaba daya su kayi murmushi. Cikin wannan suke sai ga mahaifin nata zai fita,
ya yi daidai alokacin Ishaq na gidan. Cikin hanzari da kamun kai Ishaq ya
durkusa ya na cewa, “Abba barka da wuni” Mahaifin na ta Alh. Isma’il ya ce,
“Alhamdilillah na jidadi kwarai da natarar da kai, domin akwai wata ‘yar magana
danake so nayi dakai, idan kaje gida dan Allah ka toru iyayen ka domin ina sone
nadan yi tafiya cikin wannan makon. Zance Mahaifin Hanifat kenan.“Ba matsala
Insha Allahu zan sanar da su, duk dayake Abba yay tafiya amma nayi waya dashi
ya sanar dani cewa dayardan Allah zai dawo acikin wa’annan kwanakin”.“Dama
Abban naka baya a gari ne?” Eh! Wallahi dama ya dade dayin tafiyar don inaji
yanzin yana da wata tara da yin tafiyar, dama ya tafi Malaysia ne”. sai faman
susan kai ya keyi sai kace dashi makaryaci da yake ai karyarce ya ke yi. “Au
nima din Malaysia zan je amma ba damuwa tinda ya sanarda kai zai dawo acikin
wa’annan kwanakin badamuwa.
Bayan ya wuce Ishaq ya tashi ya kalli Hanifat yayi murmushi,
wai ita kunya taji, Hanifat ta rufe fuskarta ta zura aguje ta nufi shiga gida,
Ishaq sai faman kiranta yake yi amma taki ta dawo, ya gyada kai ya fice abinsa.
Bayan rabuwarsa da Hanifat Ishaq ya nufi dabarsu da zuwan
shi, cewa yake “H!!! Hello guys!, ya yi wani nannade yatsusa kace dashi
kuri’ace zai dangwala, kume suke nufi da wannan kawai sai suka lale. Musbahu ya
ce, “Takare ya akayine two days kadena shizowa bila”. Musbi kasan yanda
abubuwan suke fa kasan ina process na yarinyarnan” Musbahu ya katse hanzarinsa
da cewa, “wace kenan?” Ustaziyyar mana ko kamantane? Kai!! Babah ina kyautata
zatun ka kaso mana princes? Musbahu ya fadi hakan.“Takwala kasan meke faruwa
kuwa? Hadani da kwalbar sirof daya kasha labari babah” Ishaq ya ce hakan.
Kaicu dama bazaka iya shaida na dan adam ba, domin wani sa’ilin zaka iya
shaida da cewa lallai wannan mutum - mutum ne Nagari kuma mutum ne mai tawali’u
da sanin ya kamata. Amma kawai kana yine abinda ka gani azahiri don haka fatamu
Allah hadamu da mutanen kirki kuma Nagari ya kuma samu kasance ashedemu da
hallaiyya Nagari amen.
Bayan ya aza kwalba daya ta sirof ko kuma zan’iya ce daku
Totolin domin shine abin yayi gun samari ahalin yanzu, duk daya ke kar na
cikaku da surutu bara na dura a inda muke dumin cigaba.
Me Ishaq ya fara da cewa bayan daukar caji, “Musbi kasan
abinda muke aciki ahalin yanzu?” a’a so nake nasani mana, fadan Musbahu. Cikin
kankanen lokaci Ishaq y asanar da Musbahu duk yanda suka yi da ita kai harma da
iyayenta baki daya.
“Hmm wani ajiyar zuciya ne Musbahu yayi, ya kara da cewa,
Bashakka akwai yaki agabammu. Yanzinnan meye mafita agaremu?”Dayake ishaq
ashirya yake ga dukkan abinda zai fada, kuma yanada mana sananiyar duk abinda
ya aikata bazai bashi ruwaba a nashi Nazarin/Tinani.
Bude bakinsa keda wuya yake cewa, “Musbi karka damar da
rayuwarka da ya ke nagayama da cewa ni mai baka mamaki nan gaba, amma ina neman
alafarma daya gunka”.
Nana take Musbahu yake cewa, “wane irin alfarma kakeso duk
duniyar yanzunnan za’ayima my Friend, don’t worry just tall me.
Ishaq ya dan taboshi ma’ana ya dan taro kunnesa yaji, Bayan
kamala maganganun da ishaq ya sanar dashi, nan take suka dauke kuwa suna faman
tsalle ce kake wa’anda aka yi wa busharar da Aljanna tun anna duniya. Bashakka
daganin irin wannan ka’iya dago hannin cewa tabbas ba alkhari bane suka
kulla.Duk da ya ke muma kammu bamada masaniyar menene manufar wannan, amma
ma’iya cigaba da biyan kididdigi domin gano menene manufar
wannan.
Idar da wannan zancen keda wuya Ishaq ya dakku wayar sa
acikin aljihun rigarsa na gaba ya dinga wani latse-latsen wanda yake wata kila
zamu iya gano menene sanadin yin wanna. Bayan ya kammala Ishaq da Musbahu su ka
lale irin wannan wanda suka saba. Kai gaisuwar ma idan ka ganta kace dasu fada
suke yi, domin irin yanayin gaisuwar.
Rabuwansu ke da wuya sai ya zarce a gidan su Fatima da
isarsa, yayi da ce da fitowan ta. “A’a manya-manya ba’ammana hijiraba, duk da
bilar ma zance kadaina ziyara, ina fata lafiya ya kawo ka” Eh! Tima
0 Comments
Post a Comment