Kyakkyawar Yarinya ce, cikin motar, direban ta na tuki a hankali, wanda a nata bangaren wayace a hannun ta tana faman latsa, a dai dai lokacin ne direban ya yi (Horn) bakin gate din wani katafaren gida. Mai gadi ya yi hanzarin budewa, direban ya shiga da motar ciki sosai sannan ya yi (parking) ya fito hadi da saurin zagayowa ya bude gidan baya ta fito. 

Yarinyar wacce taci sunan ta Farida za ta yi kimanin shekaru Shatara zuwa ashirin cif! Kyakkyawa ce a jin farko, ta na da kyawun siffa uwa uba iya tafiya, fannin magana sam-sam bata da yawan magana, magana ma ce kake wuyar ta ta ke ji idan kaga tana wani dan dogon zance da Dad din ta take magana ko kuma Mom din ta, sai dai tafi yawan magana da Yayan ta. Haka ko a cikin mutane take yana da wuya kaji maganar ta, tun kawayen tana damuwa har suka yi sabo da halinta, idan ana magana cikin kawaye sai idan anyi maganar da zata bada dariya, ko shi din iya kacin ta murmushi.