5.3 ILLOLIN AMFANI DA YANAR GIZO/KAFAFEN SADARWA (INTERNET)
Babushakka illolin da yanar gizo ke haifarwa suna da yawa sosai, don haka sai dai mu ɗan tsakuro kaɗan daga cikin matsalilin da take haifawa kamar haka: -

1. Sau da dama mutane suka lalace a sanadiyyar wannan kafar yada bayanai ta yanar gizo (internet).Yana daga cikin illolin amfani da yanar gizo tawajen kafafen sadarwa na zamani ga mata. Babu shakka mun sani cewa mata mutane ne masu son kyale-kyali da jin dadin rayuwa, kuma a cikin irin waɗannan guruf-guruf din za a iske da akwai matan masu kudi ko kuma ‘ya‘yan masu kudi da basu da wani zance sai irin jin dadin da suke ji a gidan mazajensu ko kuma gidan iyayensu. Wanda hakan yake haifar wa da wasu daga cikin membobin guruf din kishi ko kuma jin ina ma ace sune suke cikin irin wannan jin dadin rayuwar. Da akwai wani guruf da wata daga cikin membobin guruf din take cewa ai ita da mijinta sun fahimci juna sosai da hatta kudin albashinsa idan ya dauko zuwa yake ya zube mata, kuma suna yin kasuwanci tare, kudin kasuwancin sai yadda ta ga dama ta yi da su ba zai ce mata komai ba, duk abin da taga dama za ta yi da kudin, idan yana buƙatar kudi kuma wajenta zai zo ya tambaya. Ai kuwa kafin awa ashirin da hudu membobin guruf din da dama sun lalubi mijinta a facebook suna ta tura masa sakonni da dama suna son sa. To yanzu a nan laifin wa? Ita ta zo tana tallar mijinta, mutane kuma su kaga tabbas ba wanda baya so ya sami irin wannan miji da sai abinda matarsa ta ba shi ya saka aljihu. Wasu matan kuma zaki ga sai su rasa inda za su je a basu shawara sai a dandalin sada zumunta. Idan mace ta yi fada da mijinta ko kuma wani abu ya faru tsakaninta da iyayen miji sai ta zo dandali tana neman shawara ko mafita. Ko kuma ka ji mace tana tambayar yadda ake rayuwar zaman aure, duk a cikin dandalin sada zumunta, wannan ai shi ne kin kwance wa kan ki da kan ki zani a kasuwa. Domin kuwa a cikin irin wannan taro ba za a rasa wanda ya san ki ba ko kuma wanda ya san wani naki. Haba mata ai ciki ba don cin tuwo aka yi shi ba kawai, shi ya sa dai auren iyayenmu ya fi namu karko domin akwai su da iya adana sirrin da ke tsakaninsu da mazajensu. Amma mu namu auren bayan shekara biyu zuwa uku ya kare saboda rashin hakuri da iya tattalin miji , uwa uba kuma adana sirrin dake tsakani.

2. Da yawa daga cikin matan aure yanzu sun gamu da mugayen kawayen da suka saka su a cikin harkar shaye-shaye da neman mata ‘yan uwansu duk a ganin wayewa ce, idan baka yi wannan harkar ba to kai ba ka waye ba. Don haka mata a rage buri da son a san ke ma wata ce ko matar wani ko ‘yar wani ko kawar wani, domin daga karshe ba abin da zai haifar sai da mara ido. Rayuwar duniyar nawa take da har zaki saka kan ki a irin wannan masifar, ki batawa kan ki da ‘ya’yanki suna ki jawowa danginki abin magana. Kowa ya yi da kyau zai ga da kyau.

3. Sau da dama zaka shedi mutum da sheda mai kyau; amma akwana a tashi kaji ance ya zama cikakken zingiki ko takagari wanda bashida aikinyi sai zinace – zinace ko shaye – shaye kuma wannan yana faruwa ne ta dalilin amfani da yafukan internet imma wajen haduwa da miyagun abukai ko kuma ziyartar shafukan batsa kuma yana daga cikin illar amfani da yanar gizo, mutum kai tsaye zai iya fadawa a wani guruf na mashaya jini ko ‘yan sihiri, wata kila shi baima sani ba kawai wajen shige-shige ya jefa kansa a cikin mummunan hatsari.

4. Yana daga cikin illolinta mutum ya zama cikakken makaryaci misali; idan kama amfani da kafafen sada zumunta sai kaga mutum ya dagargaje ya shirga wata irin karya da kai kanka sai hankalinka ya tashi idan kaji ta. Wani zaiyi karya a fanni addini wani ko don ya burge ne kawai yake karya a shafukan internet wani kuma bashi da aiki sai kuƙarin tayar da hankalin al’umma. Misali; lokacin da ake yada magana kan ciwon ibola, masu ƙoƙarin yada wannan basuci nasaraba harsai da sukayi amfani da kafafen internet da shafukan sada zumunta na yanar gizo.

5. A halin da muka tsinci kanmu a ciki a yau, yanar gizo (internet) ta zama wata hanya ta yada miyagun akidu da kuma yada farfaganda don cimma wata manufa imma ta ni kadai ko kuma ta wasu daidaikun jama’a don su cimma wata manufa tasu ta su kadai.

6. A yanar gizo (internet) sau da dama ake lalacewa a sanadiyar finafinan batsa da mujallan batsa da ake samu akan shafukan internet. Muna fatar Allah Ya karemu ya kuma shirya mana al’umarmu baki daya.