BABI NA HUƊU

4.0 MA’ADANIN TATTARA BAYANAI

Ma’adanin tattara bayanai da umurni wato (Storage Mediadon amfani da su zuwa gaba. Dukkanin kwamfutuci suna amfani da ma’adanin tattara bayanai domin adana (software) wanda sai da shi ne sannan (hardware) ya yi aiki. A matsayinka na mai amfani da kwamfuta, ka na ajiye ko adana bayanai iri daban-daban a cikin kwamutarka ko kuma a cikin ma’danin tattara bayanai.
Ma’adanin tattara bayanai, wani abu ne da za mu iya ganin shi a zahirance, ba ɓoyayyen abu ba ne da za a ce ba a iya ganin shi ko kuma a taɓa shi ba, abu ne da ake iya adana ko ajiye bayanai da kuma umurni. A duk lokacin da mai amfani da kwamfuta ya adana bayanai a cikin ma’adanin bayanai, a taƙaice dai ya adana fayil kuma wannan matakin ana kiransa da suna rubutu (writing).
Idan fayil ɗin a buɗe yake wannan matakin ana kiransa da suna karatu (reading).
Waɗan da muka fi sani su ne:
LAMBA
SUNA
HOTO
1.     
(Hard Drive):- Wannan ma’adanin matsakaici, wanda ya yi kama da wanda ke ƙasan shi, ana ce masa (hard drive). Wannan (hard drive) yana zuwa ne tare da kwamfuta, sannan kuma kodayaushe yana cikinta.
Yana adana dukkan shirye-shiryen da kwamfuta zata iya buƙata don ta yi aiki. Bugu-da-ƙari, masu amfani da kwamfuta suna adana bayanai a cikin shi.







2.     
(Floppy Disk):- Wannan ma’adani matsakaici, za a iya saka shi a cikin kwamfuta sannan a adana bayanai a cikinsa, sannan a fitar da shi. Za a kuma iya tafiya da shi duk inda  ake da buƙata.











3.     
CD ko DVD:- Irin wannan ma’adanin bayanai yana karɓar bayanai sosai fiye da (Floppy Disk). Wannan ma’adanin bayanai ya zo da bambancin siffa ko siga. Wannan yana nufin muna da CDs da kuma DVDs waɗanda za a iya adana bayanai kawai a kansu, amma ba a iya goge bayanan da aka saka a cikinsu. Bugu-da-ƙari, akwai waɗan da ake iya adanawa sannan kuma a goge bayanan idan an buƙaci yin hakan.
4.     
(USB Flash Drive)Wannan shima yana ɗaya daga cikin ma’adanin bayanai da muke da su, wanda ya ke da matuƙar sauƙi wajen ɗauka aje duk inda ake da buƙata da shi, sannan ya fi sauƙin riƙewa bisa ga (floppy disk). A yadda muke gani a cikin hoto yana da ƙanƙanta sosai idan mun kwatanta shi da sauran da suka gabata.