3.2 RAM DA ROM
3.2.0 RAM: Yana nufin (Random Access Memory). Wannan ƙwaƙwalwa ce mai ɗaukar bayanai a lokacin da ake amfani da kwamfuta idan tana buɗe. A duk lokacin da aka rufe kwamfutar to, duk bayanan dake cikin (RAM) zasu tafi.
3.2.1 ROM: Yana nufin (Read Only Memory) shi ne mai karanta abin dake cikin ƙwaƙwalwa kawai. Shi kuma Wannan ƙwaƙwalwa ce da ke ɗaukar bayanan da ake iya karantawa, amma basu gogewa. Bayanan dake cikin ROM ba su gogewa, kuma kullum suna nan, hasali ma koda an rufe kwamfutar suna nan ba zasu fita ba. 

3.2.2 Mashigar Fai-fai (Disk Drives): Mashigar fai-fai wani abu ne dake iya karanta bayanan dake kan fai-fai. Wannan maganace da aka yi ittifaƙi a kanta, cewa dukkanin kwamfuta ta mallaki nata mashigar fai-fan; ta kuma mallaki (hard disk drive) da (floppy disk drive) da kuma (CD-ROM drive). Duk da haka, wasu a na samun su da (DVD-ROM drive). Amma shi (hard disk) a ɓoye yake can cikin kwamfuta, shi kuma mashigar (floppy) da mashigar (CD-ROM) ko (DVD-ROM) za a iya ganinsu anan gaban akwatin na’urar kwamfuta (System Unit).