BABI NA UKU
3.0 ABIN DA ZA A IYA GANI KUMA A TAƁA A KWAMFUTA (HARDWARE)
Kwamfuta na da abubuwan dake amfani da lantarki da kayayyakin inji da ake ce ma (hardware)
Hardware: shi ne abin da za a iya ganin sa kuma a taɓa shi a kwamfuta, ya kuma ƙunshi kayayyakin shigarwa da na fitarwa da tsarin na’urar kwamfuta (system unit) ya ƙunshi ma’adana da kuma kayayyakin sadarwa.
Idan har babu waɗannan ababen, to, ba yadda za a yi a yi amfani da kwamfuta:
3.0.1 Na’urorin Shigarwa (Input Devices): Abin da ake nufi da wannan shi ne dukkanin wani abu da za a iya amfani da shi da zai ba da damar shigar da bayanai a cikin kwamfuta.
Akwai na’urorin shigarwa (input devices) da yawa, amma shida daga cikinsu su ne ma fi shahara, ga su kamar haka:

 Jerin gwanon na’urorin da ake iya gani masu shigar da bayanai, kuma a taba su kai tsaye

LAMBA:
SUNA
HOTO
1.     


Allon Rubutu (Keyboard): Ana amfani da madannin allon rubutu (keyboard) domin rubuta wasiƙa, lambobi da kuma yin wata alama (symbols) a cikin kwamfuta.
          




2.     
Linzamin Kwamfuta(Mouse): Linzamin kwamfuta wani abu ne da ake yawo da shi, kuma yana da maɓallai waɗanda za a iya canjawa a ko wace irin siffa, akan lallatsasu lokacin da ake aiki da kwamfuta.
A na danna linzamin ta hanyar dannawa da sake madannin. Wannan tsarin na bada damar shigar da bayanai lokacin da ake aiki da linzamin.


 
3.     
Abin Kwaikwayon Siffa (Scanner): Tana ɗaya daga cikin abubuwan shigarwa wacce take kwaikwayon siffa (kwafi) daga takarda zuwa cikin kwamfuta
4.     
Makirufo (Macrophone)Makirufon ana amfani da shi wajen shigar da murya cikin kwamfuta.
5.     
Kamarar ɗaukan Hoto (Digital Camera): Kamarar ɗaukar hoto na ba da damar ɗaukar hotuna waɗanda za a iya sanya su a cikin kwamfuta. 
6.     






Kamarar Bidiyo (Video Camera)Kamarar hoton bidiyo ta kwamfuta na ba da damar ɗaukar hoton bidiyo, kai harma da hotunan da ba na bidiyo ba, kuma a sanya su a cikin kwamfuta.













3.0.2 Na’urorin fitarwa (Output Device):  Su ne duk wani abin da za a iya amfani da shi wanda zai ba da damar fitar da bayanai a cikin kwamfuta. Kuma akwai sanannu guda uku, gasu kamar haka:-

Jerin gwanon na’urorin da ake iya gani masu fitar da bayanai kuma a taɓasu kai tsaye
LAMBA
SUNA
HOTO
1.     
Abin Kallo ko Allon Majigi (Monitor): Wannan shi ne allo mai fitar da saƙo lokacin da ake gudanar da wani abu ko ake danna wasu madannai ga Allon Rubutu (keyboard).
2.     
Injin ɗab’i (Printer)Wannan ita ce firinta dake fitar da bayanai ta hanyar fitar da su bisa takarda. Su kuma waɗannan takardu da ta fitar, su ake kira had kwafi (hard copy).
3.     
Abin Magana (Speaker):Murya tana ɗaya daga cikin saƙo ko kuma a ce bayanan da za a iya karɓa daga abin magana.