RIKAKAFIN KAMUWA DAGA CUTUTTUKA:- (ANTIVIRUS)

Ƙwayoyin cutar kwamfuta abu ne mai hatsarin gaske da zai iya tarwatsa da canja bayanai a kwamfuta, misalin ƙwayar cutar mutum ne, (virus) ta na tafiya ne da saurin gaske, ma’anar hakan shi ne zaku iya haduwa da mutum yana cike da lafiya amma bayan rabuwarku kaji ance yana kwance ciwo ya kada shi. Dalilin haka, dole ne a kula da kwamfuta wajen sanya mata rikakafin kamuwa daga cututtuka (anti-virus) kuma a lokaci zuwa lokaci ya na da muhimmanci a kula da yin (update) din shi, dalili kuwa shi ne a kullum a na kirkiro sababbin kwakoyin cuta da zasu iya cutar da kwamfuta amma idan a na update lokaci zuwa lokaci hakan na kara karfafa (anti-virus) din ne.