5.4 ABUBUWAN DA AKE YI A YANAR GIZO (INTERNET)
   1.   Bincike:- Kamar yadda muka san amfanin yanar gizo haka kuma ya kamata mu san abubuwan da ake yi da ita don haka zamu fara ne da abin da ya shafi bincike. Da yanar gizo ana bincike mai zurfin gaske wanda ya shafi ko wane irin bincike misali; binciken tarihin magabata, ana kuma binciken abin da ya shafi kiwon lafiya, da sauransu.
  2.   Koyon karatu:- Akwai shafuka na musamman da aka ginasu don masu sha’awar su koyi karatu, za a iya zuwa kai tsaye domin ayi koyon wani darasi mai amfani.  
  3.   Neman Aiki:- Akwai shafuka da dama da za a shiga ta yanar gizo domin neman aiki, misali aikin gwamnati, aikin zane-zane (graphics), gina shafukan yanar gizo (website design) ma’ana, (applications design), (typing) da sauransu, kuma za a iya ribatuwa da waɗannan shafuka don gudanar da aiki ba tare da an fita an je wurin aiki ba, ma’ana za  a yi aiki a na zaune a gida bayan ka kammala kai tsaye sai su biya ka kudin aikin ka.
  4.   Saye da Sayarwa:- A mahaɗar sadarwa ta yanar gizo akwai shafukan da suka shahara wajen gudanar da kasuwanci a kafafen yanar gizo wanda za a iya saye ko sayarwa a shafin, misali kana da littafai da kake so ka shigar da su kasuwar duniya akwai shafin da zaka iya yin rajista da shi sai ka saka littafan ka a ciki mutane su saya kana karuwa da kuɗaɗen da suke sayar hajarka.
  5.   Aikawa da saƙonni da karɗan saƙonni:- Ta mahaɗar sadarwa za a iya aikawa da saƙo zuwa wurare mabambanta, za a iya aikawa da sako daga shafin da ke a yanar gizo zuwa wayar hannu.