AMFANIN YANAR GIZO/KAFAFEN SADARWA (INTERNET) 

Bazan iya lissafo amfanin ta ba gaba ɗaya, saboda amfaninta yana da matuƙar yawan da ba za a iya lissafashi ba, amma ga kaɗan daga ciki:- 

Fasahar Intanet wata duniya ce mai cin gashin kanta, fasahar a yau ta zama gagarau, domin bayan hanyoyin sadarwa, duk abin da kake da bukata a internet zaka samu ta hanyoyi daban-daban; ko dai ta hanyar Injimin nema misalin manema ta google, ko Yahoo ko kuma AltaVista, zaka iya samun bayanai ta tsararrun hanyoyin neman bayanai misali; (Directories). Baya haka kuma, akwai wasu nau’ukan bayanai da suka shafi sauti ko na hoto mai motsi (video) duk zaa iya samu a wannan hanyar ta yanar gizo.


1. A ɓangaren ilimi kuwa; a yanar gizo za a iya karatu har a kai ga matsayin digiri ko digirgir har a digirgire ma’anar wannan shi neza a iya samun shedar takardar yin (degree), (Masters) da kuma (PhD). Zaka iya shiga makaranta ka ɗauki darasi, ka nemi bayanai wurin malaminka, kayi jarabawa har ka samu sakamakon jarabawar babbar jami’ar da ke cin karenta babu babbaka a duniyar yanar gizo. Misalin waɗannanjami’o’in sun haɗa da National Open University of Nigeria (NOUN), World Education University (WEU, da kuma Online Islamic University (OIU) da sauransu.

2. Idan kuma muradinka haduwa da mutane, shima wannan abu ne mai sauƙin gaske, tun daga wadanda ka sani da kuma wadanda baka sansu ba. Akwai hanyoyi da yawa da zasu baka samu wannan damar, misali; Facebook, Twitter, MSN Messenger, Yahoo Messenger, ICQ Chat Messenger, Sharhamak Forum da sauransu. Babu shakka idan har wanda kake son hira dashi yana da irin waɗannan hanyoyi kuma ya bude su, yanzu zaku yi rubutacciyar hira da nau’ukan hirarrakin da zasu iya samuwa ta waɗannan kafafe. Idan kuma hirar video kake so, ma’ana; kana ganin wanda kake hirar da shi, shima yana ganin ka kai tsaye; wannan ma abu ne mai sauƙi domin akwai kafafen da wannan ne kawai amfaninsu a kafafen yanar gizo. Misali; ooVoo da skype da sauransu.

3. Shafukan sada zumunta na yanar gizo ba karamin taimakawa mutane ya yi ba, musamman idan kana neman wani abokinka na shekara da shekaru ka ƙasa samun sa, to idan ka laluba za ka same shi a daya daga cikin waɗannan shafuka wato facebook ko twitter ko instagram ko WeChat, da sauransu. Haka kuma idan ma labari kake nema da dumi-duminsa to ka leka daya daga cikin waɗannan shafuka to tabbas zaka samu labarin da kake nema. Kai a takaice dai duk abinda kake nema kama daga mutane, kayan sayarwa, labarai da dumi-duminsa labarai na nishaɗantarwa dana ban al’ajabi da sauransu idan ka tambaya to tabbas za ka sami mai baka ansa.

4. Intanet har wa yau wata duniya ce ta ma’adanar bayanai. Mutum ya zauna da jahilcin wani abu, bayan ya iya rubutu da karatu alhali ga (Intanet) – ina tunanin wannan shi ya so ta ƙasance masa. Duk bayanin da kake bukata, zaka sameshi (muddin wani yayi rubutu a kansa). Idan takamarka karatun jarida ne, an gama! Dukkan wata jarida da ka san ta shahara a duniya zaka samesu a yanar gizo (Intanet).  Sai ka karanta su ma kafin a fara sayar da su a biranen da ake bugawa ko yada su. Idan kana son karanta irin binciken da wasu masana suka yikan wasu al’amura, duk zaka iya samu a yanar gizo (Intanet). Dukkan wata ƙasa da ka sani zaka iya samun bayaninta a kafafen ko shafukan (Intanet), ka karanta ko ka ma yi dukkan abinda ka ga damar yi dashi, ya rage naka.

5. Dandalin sada zumunta a shafukan yanar gizo sun taimakawa mata sosai, musamman matan da suke gida basa aiki ko zuwa makaranta, sai dai zaman gida. Irin waɗannan matan da suke zaune a gida yawanci idan sun gama aikace-aikacen gida su kan leka irin waɗannan zauren sada zumunta su zama membobi na guruf-guruf din da ke ciki domin samun karuwa. Wasu daga cikin guruf din facebook sun haɗa dana girke-girke, saye da sayarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa da dai sauransu. Sau da dama za ka ga wasu matan auren sun shiga irin waɗannan guruf din ne da zuciya daya, domin su samu su karu akan wani abu da ba su sani ba ko kuma su yi tambaya idan wani abu ya shige musu duhu.

6. A ɓangaren siyaya kuma, munga irin rawar da amfani da internet ya yi mana a wannan karon, wajen yada manufufin mu na siyasa da tallata yan takararmu tundaga shugaban ƙasa, yan majalisa, sanatoci, gwamnoni da sauransu. Don haka; internet abune mai matukar muhimmanci a wannan rayuwar tamu ta yau da kullum, akan haka ne yasa idan za ace da mutum ya fadi amfanin internet babu shakka sai dai kayi iya ƙoƙarinka don kowa da irin amfanin da sai iya morema a yanar gizo.