6.1 BABAN KWAMFUTAR TAFI-DA-GIDANKA

 Henry Edward Roberts (coined the term) kwamfutar tafi-da-gidanka) shi ma an dube shi a matsayin baban kwamfutar zamani ta tafi-da-gidanka, bayan ya fitar da Altair 8800 a watan Disamba 19, 1974. Sai dai bai gabatar da ita ba saia shekarar 1975. Kwamfuta ta samu da kimanin $439 ko a tsare a kimanin $621 ta kuma kunshi abubuwa masu yawa da aka ƙara na (add-ons) kamarsu (memory board da interface boards). A watan Augusta shakarar 1975, an sayarda Altair 8800 sama da 5,000 na kwamfutar tafi-da-gidanka; daga nan sai zamanin kwamfutar tafi-da-gidanka ya cigaba.

Muna da wasu sama da mutum sha biyu a matsayin babanni waɗanda suka taimaka kuma suka bada gudummawarsu a wasu sassa daban-daban na kwamfuta.