1.4 ILLOLIN KWAMFUTA
Waɗannan bayanai da zan zana a ƙasa su ne illoli ko rashin amfanin na’urar kwamfuta a wannan rayuwa tamu ta yau:-
   ·       Kwamfuta na’ura ce wadda ba ta da tunani, hankali da kuma basira. A ƙashin kanta ba ta iya gudanar da komai.
   ·       Kowane irin aiki zata yi dole ne sai an sanar da ita shi kafin ta aikata shi.
   ·       Kwamfuta ba ta iya ɗaukar kowane irin mataki da kanta. 
   ·       Duk abin da zata yi tana ƙarɓa ne daga mai amfani da ita, don haka ya zama wajibi duk abin da zata gudanar yafito daga mutum ne.
1.4.0 Muhalli
   ·       Tabbas muhallin da zaka adana kwamfuta ya zama mai tsafta kuma ya ƙasance wuri ne da ba ƙura.
1.4.1 Rashin Ji
  ·       Kwamfuta ba aba ba ce da ke ji ko gani ko kuma ta iya gudanar da wani tunani da kanta.
  ·       Ba ta iya yanke hukunci.  
  ·       Bata iya ji ko ɗanɗano ko yin wani abin gwaninta ko kuma aiwatar da wani abu na ilimi saɓanin mutum.