5.9 MA’ANAR INJIN NEMA?

Injin nema wani kunshi ne (software programme ko script) wanda ake iya samu a yanar gizo, ana neman daftari aiki (documents) ko fiyil (files) ta hanyar madannar kalmomi na Allon Rubutu a kwamfuta sannan amayar maka da amsar ko wane irin fayil wanda ya yi kamanni da wadannan madannai da ka rubuta. A yau akwai dubunnan injin nema da ake da su a kan yanar gizo, ko wane daga cikinsu ya kunshi iya karfi da kalolin abinda ake iya samu daga gareshi.
Injin nema na farko da aka fara kirkirowa shi ne Archie, wanda muke amfani da shi don nemo fayil na FTP da kuma injin nema na farko da aka fara neman rubutaccen rubutu da shi shi ne injin nema na Veronica, wanda ya fi zama shahararre a yau shi ne injin nema na Google. Ba su kadai muke dasu ba muna da AltaVista, Excite, HotBot, Infoseek (go.com), Lycos, da kuma yahoo.