Buri!
Hmmm kalmace mai matukar girma…
Sau da dama Rayuwa take lalacewa abisa dalilin kokarin ganin buri ya cika.
Sau da yawa za kaji kasala a tunaninka bazaka iya ba.
Sau da dama bazaka samu kwanciyar hankali ba adalilin rashin cikar buri.
Sai kaji kamar sallamawa ce kawai mafita agareka.

Duk lokacin da kaji kamar gazawa to, wannan lokacin ne lokacin da ya dace ka turza wajen ganin cewa ka cika burinka.

WANNAN LOKACIN NE ZAKA JAJIRCE DON GANIN KA CIKA BURINKA
Mutane da suna samun dama a Rayuwa sai dai basa amfani da damar.

Shin kana so ka cigaba da zama kullun a baya ne?
Ko kuma ka yanke shawarar ka jajirce don ganin ka cika burinka?

To, dole ne ka samu yakinin cewa zaka iya
Dole ne ka sakawa zuciyarka gishiri

Ka sani cewa
Zuciyarmu kamar zaki ce

Sai dai wasu mutane sun yanke cewar bazasu bawa zakin damar fitowa ba
Mutane da yawa sun saka zakin a cikin akurki

Shin ka matsu ne baka cimma burinka ba?
Shin ko ka shirya ka yi fada don cika burinka?

To ka bar wannan zaki ya fito
Je ka yi farautar burinka

Ka sanicewa maganarka a kan burinka bazai taba sanyaka kayi gaba ba.
Gudanar da burinka a cikin fargaba yakan ragwantaka.
Makiyanka zasu baka shawarar cewa ka barshi
Ka sani cewa kai kadaine zaka iya zuwa inda yake ka sameshi.

Shi burinka
Babu wani
Wanda zai taimaka maka akanshi

Babu wani
Wanda zai farauto maka shi

Babu wani
Wanda zai goyi bayanka
SAI DAI KAI KADAI
Masu hikima na cewa: “Kowa naso ya ci, sai dai kuma wasu burinsu suje su farauto burinsu”

Kowa na so yayi nasara a rayuwarsa
Sai dai daga ciki kadan ke kokarin ganin hakan ta kasance.

Ka daina iyakance kanka akan burinka

Ka sani cewa zaka iya tabbatar da manufarka ta zama gaskiya.

MUTUM DAYA NE KAZAI IYA
WANNAN MUTUMIN
KAI NE
Akwai Jama’a da dama kamin kai, wadanda suka yi nasana akan ababe manya a rayuwarsu.
Kuma ababen da suka tsara ne a cikin manufofinsu
Sun kammala tsaf.

Wannan ya nuna cewa kaima zaka iya
Hakan ya nuna cewa zaka iya tabbatar da burinka zuwa ga tabbata idan har ka so yin hakan.

Kaine wanda yafi kowa zama hatsari akan cikar burinka, saboda kai ne kadai zaka iya yanke hukunci da cewa NA FASA, na ja dabaya saboda bana iya cimma burina

KAI KADAI NE
WANDA ZAI HANA DAKILE KANSA DAGA CIMMA BURINSA.

Kana da JARUNTAR da kai kanka taba saninta ba
ZAKA IYA CANZA DUNIYA DA MANUFOFINKA.
Sai dai kana bukatar dagewa da jajircewa akan haka
Kana bukatar kafewa akan hakan
Kana bukatar tabbatar da hakan
KO MAI WAHALA

Idan har kana da ragwanci, idan kana jin tsoron fadawa hargitsi da hasara, tabbas bazaka taba zuwa gababa a rayuwarka

Kazayi ta cibaya ne
Bazaka taba cimma burinka na Rayuwa ba, saboda ba’a a gina buri da fargaba ko rauni.

Rayuwa ba a iya sanin makamarta
Tana dauke da abubuwan ban mamaki acikinta

Zai yiyu ka kusa cimma burinka ne
Kana kusa dashi fiye da yadda kake tunani
Manufarka zata iya zama gaskiya idan har baka ja da baya ba.

KA ZAMA KAMAR ZAKI
KADA KA TABA JA DA BAYA
Daga kalu-balen da kake fuskanta na Rayuwa

Zaki baya taba barin abinda ya sa a gaba har sai ya sameshi
KADA KA BAR BURINKA HAR SAI KA TABBATAR DA SHI

YI BURI MAI GIRMA
Haka kuma kada ka bar dan karamin abu ya hanaka cimma burinka na Rayuwa
KA YARDA DA KANKA idan har kana hanyar buri.

NA BAKA SHAWARA DA KA MOTSA
KA DAUKI MATAKI
KUMA KAYI BURI BABBA ZAKA IYA TABBATAR DASHI

Join Sahihiya Network