WASALI DAYA



SIN ONE (1)
Da karfe tara na safe Alhaji  Yusha’u baban salima yafito da ga kuryar dakinsa izuwa falo da jakarsa tazuwa office arataye alamar ya kammala shirye-shirye zaije wurin aiki, turo kofar falon da yayi ke da wuya sai yaci karoda hajiya a’isha matarsa zaune a falo tana jiran fitowarsa tayi masa rakiya ko adawo lafiya. Wato mamar salima a’a hajiya yau zaman rangadi kawai akeyine? Hmm baban salima kenan ai wayon da kake yimin ne nagaji dashi na lura kwana ukun nan koda nake Ankara ka fice abinka ba tare da nayi tozalin safeba ko kuma insamu ladar adawo lafiya ko ta rakiya mamar salima ta fada acikin yanayi na shagwaba ga mai gidan nata Alh. Yusha’u acikin yanayi na murmushi da kuma kada kai baban salima yace da ita Aisha bakya barin zolaya wallahi .wai ina salima ne yau bata fito bane har yanzu? Wallahi makare ta tashi yanzu take sallah, inji Aisha haba wannan wane irin shashancine haka sallar safe karfe tara Aisha? Ya fada acin yanayi na damuwa bayan da yayi shiru na Kamar kika daya ya sake nisawa yace amma dai kin gaya mata sakonako? Eh. Nagayamata yan zuma jiran nake ta fito inkara nanata mata don ba gajiya akeba Aisha ta acikin ladabi ga mijinta wato yusha’u. to shikenan ni zan fita to adawo lfy mai gidana Aisha ta fada acikin farin ciki.

SIN TWO (2)
Aisha:-Salima:-Salima!! Hajiya Aisha ce mamar salima zaune a falo rikeda rimot yayin da take kokarin raba hankalinta biyu daya awuri kunna talabijin bango (plasma) daya kuwa awurin kiran yar tata salima na am momy  wannan itace amsar da tayiwa mahaifiyar tata amatsayin amsar kiran da tayi mata, batare da saba lokaciba kuwa tafito jikinta asauyaye bisaga sanin cewa gatanar gizo bata wuce ta kokiba maganarce dai daya da aka saba ko yanzu itace za’ayi zamanta keda wuya akan dayar kujerar dake fuskantar ta mahaifiyarta acikin katafaren falon gidan ne hajiya Aisha ta soma gayamata salima: wai ina zancenmu ya kwanane kingafa ko yau da abbanki zai fita sai da yayi wannan maganar tukuna yafita.
Salima:- Wallahi Umma nidai abba yasani a gaba wai meye haka shin mutum kulum baza’abbarshi ya hutaba ta fada acikin shagwaba
Aisha:- Iyeh! Lallai salima wuyanki yai kauri harma wani antakura maki kike gani ko? Laifi nane nida nake kakkareki awurinsa amma dagayau zan dinga barinki dashi ki ji irin tsuwar da nake ji akunnuwana wata kila kyasan dawa ki ke yi.
Salima:-kai! Umma don Allah kirufa min asiri salima ta fada acin fargaba taredadora hannuwanta acikin labban bakinta yayinda bakin yake hangame alamar mamaki.
Aisha:- eh mana don naga hakan kikeso ayi ko?
Salima:- a’a Umma kinga wasa nakeyi don Allah kiyi hakuri karki gaya masa tafada acin yanayi na karaya da damuwa.
Aisha:- To inkuwa ba hakaba kiyi kokari fito da mijin aure a kwanan nan a tsayar da Magana guda daya. Kinji na gaya miki.
SIN THREE (3)
Na’imaacikin dakinta na kwana a gidansu yayinda take kan gado ta tashi banta da filon dake kan gadon wato ta kishingida akan filon data jingina akan jikin gadon idanun ta kuwa a kafe a sama alamar tana cikin halin nazarine kamar daga sama taji wayarta tayi ringing wanda shine ya katse mata nazarin da takeyi takuma mika hannunta asauyaye ta dauko wayar tata taga ashe kawarta salimace ke kiranta adaidai lokacinda ya dace ace tana can sharer bacci harda mishari azawar datayi a kunnenta taji muryar salima nan take kuwa tace da ita ke kuwa me ya hanaki baccine
Salima:- Abinda ya hanaki domin na tabbatarba haka kawai kika kai karfe goma sha daya bakiyi bacciba.
Na’ima:- wallahi salima Ummace ta sakani a gaba wai dole saina fito da mijin aure a kwanan nan.
Salima:- wallahi na’ima duk matsalar dayace nima abba ya takurani saina fito mijin aure
Na’ima:- Aikuwa da kinyi jinkiri kadan da nice zanfara kiranki domin kuwa wallahi na rasa abinda yake yimin dadi arayuwata ammafa kinsan wannan baisani na janye kudurina da nake akai.
Salima:- kawata ai biyan bukata yafi dogon guri inji kuda wallahi nima bazan karayaba  saidai kome za’ayi ayi amma salima sai salim aduk inda yake aduniya
Na’im:- Allah ya barmin ke kawata haka na’ima  sai na’im saida safe kawata
Salima:- Allah ya nuna mana.
SIN FOUR(4)
Na’im da salim ne azune awani lambu na farfajiyar gidan nasu suna cin abinci  akan wani dan wani dan teburinda aka shiryashi domin cin abinci ayayin irin wannan zaman.
Bayan da na’im ya soma kai abinci abaki yace yaya na’im har yanzufa kaki motsawa balantana kabana guri inkasa hajata.
Salim: nakamar meyefa Salim ?
Na’im: haba yaya zancen Aure mana
Salim: murmushi tare da gyadakai acikin sautin hmm Na’im waikai meyasa kake son tayarda zaune tsayene Aurefa da kake gani horewace ta Allah kuma da shi da mutuwa duk ba a tsallake lokacinsu idan yazo kawai mudai kara jiran lokaci
Na’im: haba waikai wane irin lokacine kake jira haka wanda bairiga yazoba yaya ?katunafa mun kammala karatu kuma gwargwado munada ayukanmu ahannu to meye kuma yarage ?
Salim: salim da Na’im su mallaki salima da Na’ima
Na’im: Hmm yaya kenan waikai har yanzu kanan da wannan tsohon ra ayin azuciyarka karka mantafa yau shekaru uku kenan dakare karatunmu dasu kuma bawata yarjejeniya ce tsakaninmu dasuba ta aure hasalima kolam bobbin wayoyinsu bamuda suma haka kuma bamu san indasukeba basusan inda mukeba kuma ma matsalar anan itace ba mamaki yanzu sunriga sunyi aurensu agaskiya kawai yaya kadai sake tunani kainefa babba agareni tokuma yaushe zaka tsaya jiran gawon shanu
Salim: murmushi wai Na’im kodai kaine kake yimin zagon kasa awurin Abba yake neman dasa keyata agaba dangane da wannan zance ?
Na’im: haba yaya ni ai bana wan nan kuma kasani kawaidai tunaninmu dashine yazo daya ya fada acikin yanayin annashuwa
FADE
SIN FIVE (5)
Na’ima: wallahi salima ba karamin sakaci mukayiba nazama da mutanen nan amakaranta daya har shekaru uku amma mukakasa kulla hudadar komai dasu koda ta musanyar lambar waya kosanin adireshin juna.
Salima: kedai bari kawai kawata hakika munyi sakaci bakadanba musammanma da aka gama (Exams) ne yadace ko lambar wayarsu ko adireshi mumallaki daya amma kunya ta hana sai yanzu ga abin yana cimana tuwo akwarya munkuwa rasa ina zamu saka kawunammu musami saukin lamari.
Na’ima: amma ba komai indai da rai da rabo insha Allahu zamu hadu da su komai daren dadewa.
Salima: to amma bakya tunanin cewa watakil sun dade da mantawa damu kasancewar ba wata kullalliyar maganace atsakanimmu da suba balantana muce zaman jiranmu sukeyi harya zuwa wannan lokaci.
Na’ima: eh don wannan kam gaskiyane amma airabon kwado baya hawasama kuma shi mai arziki ko akuwara ya saida ruwako ?tafada acikin yanayi na wasar abokantaka da nishadi harma suka tafa hannu da juna. FADE

SIN (6)
Auwalu ya hadu da salima akanhanya ya kuma yimata al adarda ya saba ta takokarin  tsaida ita ko ainane domin jadada mata kalamansa nakauna Salima : salima: wannan itace kalmar da Auwalu ya rinka kyarawa Salima yayinda saida tayi kamar bazata juyobane dayake ta dansoma bashi baya dakyar da alamar rashin jindadi ta matse ta waigo da tsaki tace wai Auwalu mekake nufi danine wannan naci haka nagaya maka bana iyawa wai anaso dolene?
Auwalu: Salima aikuwa naci yanzu kika somaganinsa domin na tabbata shine kadai makullina na bude kofarki ta karfe da kika kargame afusace
Salima nifa inakara nanata makicewa itafa soyaya ba kiyaya bace kuma son maso wani koshin wahalane saboda haka kidaina kallon soyayata afuskar naci kamar yadda naji abakinki isowarsa awannan gabar kedawuya kuwa sai Salima ta tarbi numfashinsa dacewa dakatta Auwalu ba wani dogon turanci na tambaye kaba salatin ya isa haka kafadi abinda zakafada so nake intafi sauri nakeyi karka batamin lokaci kaji furucine kuwa da tayi acikin yanayin fushi da damuwa fadin hakan tayine kuwa ya bashi damar.


SIN SEVEN (7)
MAFALKIN NA’IMA
Na’ima: Na’im Na’im haba nawa dan dakata kaji mana kasaurareni kaji me zangayama mana katausaya mini bisaga irin halin da nashiga wallahi yanzu haka agida iyayena sun takurani sosai akan cewa saina fito da mijin aure nikuwa naki inbiye ra ayinsu domin zuciyata tanada nata gurin nadabam hakika Na’im tuni na shar antawa zuciyata kyamar kowane irin sunan saurayi indai ba mai suna irinnakaba kasancewar sunammu yazo iridaya wasali dayane ban banci ina fatar zaka karbi hanzarina.
Wannan shine majigin Na’ima na Birnin mafarki yayinda taga wani kyakkyawan saurayi mai irin sunanta atsaye kusaga motarsa maikirar……..yayinda yake kokarin bude gambun motar tasa domin tafiya wurin nasa sha ani bayan waiwayowar da yayi acike da mamakine ya furta kalma kamar haka
Na’im: aikuwa kinyi kuskure domin namiji ko mace duk wanda yake gaugawar yanke irin wannan sharadin sodadama yake kirkirowa kansa babban aiki
Na’ima: Na’im dole kafadi haka kasancewar bakasan irin tasirin da nahanga atattare da hakanba Na’im ka ayyana azuciyarka yaya shawa dakuma dadin sunayen biyu zasu kasance idan akace sunzamo ango da amarya ? tambayarda kafin ya amsa ta cigaba da cewa aikaga sunayen sun hadu wasali dayane bambamciko? To yakuma zukatan zasu kasance idan suka aminta da juna jinsi kawai banbanci ? nantake kuwa Na’im yayi wani dan saurayin murmushi tare da cewa gaskiyarki Na’ima abin zaiyi shawa sosai kuwa dahaka sukayi tsaye suka kurawa juna idanuwa kamar bazasu kyaftaba.
SIN EIGHT (8)
FALKOWAR NA’IMA DAGA MAFALKI
Na’imace kwance akan gado tana yan mirgine mirgine hade dajujjuyakai alamar wadda bacci ya gundura tana neman malkowa bayan dakika daya sai tasoma bude idanuwanta kadan yayinda tagane cewa bacci tayi nan take kuwa tazabura firgigi ta tashi zaune tareda yan sallallami harma datafa hannaye dagakan da tayi zuwa duba agogon bangone yanuna mata safiya tana daf da wayewa yayinda taga karfe biyar saura kwata. FADE
SIN NINE (9)
SALIMA TAZO SUPER MARKET
Yayinda Salima ke kokarin isowa daf da babbar kofa ta shiga super market wato (gate) anan ta taki daura wato rashin sa argamuwa da Salimdomin shikuwa Salim ya riga ya shige motarsa yana kokarin rufe kofar motar tasa yariga yagama shoping) kenan zai koma gida itakuma alokacinne ta iso batako shigaba tukuna Salima takuwa gane kowanene shi domin sa ardayi bairiga yarufe kofar motarba harma said a tanisa zata tinkareshine ya jawo kofar yarufe dai dai lokacinda ta kwala masa kira saubiyu amma bris baikosan tanayiba saboda dama gilashin motar atashe yake badabata lokaciba kuwa yaja motar yatafi abinsa ba tareda ya fahimci abinda ke faruwaba Salima kuwa tayi tsaye acikin yanayi na damuwa kimanin minti daya sai safa da marwa takeyi ranta abace hankalinta atashe.
SIN TEN (10)
SALIMA DA NA’IMA SUNA BAIWA JUNA LABARI
Na’ima: wallahi Salima yadda kikaji nagaya mikin nan haka abin yafaru abin takaici wai saida na falko nagane cewa mafalki nayi ingayamiki takaici ya wani rufeni narasa abinda yake yimin dadi wallahi adai dai wannan gabarne kuwa Salima ta tarbi numfa shin Na’ima dacewa hmm aike gwandama naki mafalkine nijiya azahiri ga Salim inakallonsa amma ahaka ya kubuce mini ba karfi ba dabara kallonsa nake har bace mani Kalmar kuwa da ta sanya Na’ima saida tazabura kadan acikin yanayi na nuna damuwa harda kai hannu akirji tace wai don Allah Salima da gaske kike wannan zancen naki kuwa bayan dan shirun da Salima tayine kafin ta sake cewa wani abu Na’ima ta sake nisawa tace to garin yaya haka tafaru ?
Salim: Wallahi in gaya miki dai dai lokacin da nake isa a gun yake kokarin dagawa harma na soma jarraba laransa amma ina baijiba haka ya tafi a binsa.
Na’ima: To, amma me yasa kika kasa tare dan acaba kiyi ta binsa a baya har sai kin ga inane unguwarsu koma kiyi sa’a ya zo ya tsaya a wani gun kizo ki taddashi.
Salima: Haba kawata kwantar da hankalinki ai indai ana zuwa ruwa bari ake in dai ana zuwa ruwa bari ake in dai da irin wannan kuren wata rana za a dace.
SIN 11
DA BUDEWAR CAMERA
Mahaifiyar Na’ima a falon gidan bayan dan nisha din da su kayi ya yin da suka kamala dare wane Na’ima tace amma Umma agaskiya idan aka yimin haka ba ayimin adalci ba.
Mahaifiyarta: ai kuwa adalcin ken an a haka ba ita ce yayar ki ba? Kamin Na’ima tace wani abu sai babar tata tasake cewa yauwa Na’ima wai wanene Na’im? Kalmar da ta sanya gaban Na’ima ya fada rasi nan take fuskarta ta canza izuwa yanayin damuwa ba tare da bata lokaci ba ta ce “Umma ta ya kika san wannan suna kuma?
Hajiya Luba: hmm! Murmushi da kuma gyada kai a hankali, ta yarda kika yi ta famar sheka mafalki shekaran jiya da dare a cikin bacci ni kuma ina tsaye kusa da ke komai kika fada a cikin kunne na ya yin da naje tayar da ked a kika ce kina son za ki yi azumi da naga aki falka shi ne na juyo a bina batare da kin ganni ba
Na’ima: so ke kai a cikin yanayi na kunya tare dad an murmushin rashin gaskiya
SIN 12
Na’ima da Salima suna fitowa daga Supermarket ya yin shigarsu Na’im amma ba wanda yaga wani. Dalili kuwa shi ne, Salima da Na’ima sunga garo matakakan supermarket dinne a cikin yanayin raha da Nishadi da juna alamar wani abu suka tattauna wanda ya burgesu har yasa suka tafa hannuwansu a cikin yanayin nasu natafiya wannan kuwa yana faruwa wane dai-dai lokacin da suka Na’im da Salim ke kokarin Parking din motarsu daga gefe dayan wajenda ake (Parking) na motoci wanda sanadiyar hakan yasa babu wanda ya lura da wani a cikinsu bayan karya kwanar da su Salima sukayi ne kadan saii gasu Salim sun shiga hidimar bude gambun motar su batare da ba’ata lokaci ba kuwa Na’im day a ke bas hi yake jan motar bay a zagayo ya tarar da yayansa Salim suma haka su ka shiga yanayin kamar irin nasu Salima da Na’ima wasa da yanayina koma da ana zolayar juna, wada kane ne amma kaunar junata sa sun zame kamar abokan juna, ina mada ace abinda suke fada ga fito zahiri da amshi dariya haka dai suka rike hannun juna suna tafiya har suka shige a cikin Supermarket din
(FADE)
SIN 13
Salima da Na’ima suna cikin mota suna hira akan hanyarsu takomawa gida ne kwatsam Salima ta bude Jakarta don nunawa Na’ima wani abin al’ajabi da ta cikaro da shi a yanar gizo ta safiyar ranar. Wanda a mai makon dauko wayarce Na’ima taji Salima ta buga Salati tare da tafa hannayenta harma dacewa na shiga uku Na’ima na baro waya ta a Supermarket. Direba kaji mu koma don Allah wannan shi ne abinda Salima ta rinka fada a cikin yanayin damuwa. Ya yin da kawarta Na’ima a cikin yanayin mamaki t ace da ita tabbi Salima wayace fa! To, inama da labarin salwancewar rayuwa kikaji ai sai kwakwalwarki ta somar damu. Kuma ai wayar nan ba bata zatayi ba domin a kudin cikakkun yakinin a Supermarket kika barta kuma kin tabbatar.
Supermarket mutanene masu amana komame ka bari indai ananne zaka tadda shi ba tare da matsalar komai bah aka Na’ima ta ce da ita.
Salima: hmm! Ke dai bari kawata abin mutum garai shika abki koma da kece fiye da hakama sai kiyi inji Salima
Duk kuwa wannan abin da sukeyi diraba baice dasu uffanba, amma yariga ya dauki matakinsa na komawa supermarket din domin dauko abinda aka manto wato (waya).
SIN 14
DAWOWAR MAHAIFIN SALIMA ALHAJI YUSHA’U DA AIKI
Alhaji: Salamu alaikum tare da izo gambun shigowa a cikin falon da hajiya Aisha take yan shirye – shiryen kayayyakin abin cinsa naci dana shaye-shaye akan wani dan kyakkyawan teburi yaci karo da ita kuwa tsaf irin yadda yake son ganin motarsa a koyaushe kamin yasake cewa komai sai ta buge da wani dan saurayin murmushi tare da cewa alaikassalam da kuma sannu da zuwa acikin yanayi na fara’a  
Alhaji: Yauwa a cikin yanayin annashuwa kuma aje jakarsa a gefe dayan kujera da ke gefen teburin bada bata lokaci kuwa ya kai zaune alamar wanda ya dawo gajiye. Uwargida rangida hidimomi kawai aketa famayi haka ya fada tare da kura mata ido kurum babu kyabtawa tsalguwar da tayi saurin yin kallon ne ya sa a cikin yanayi na shagwaba tace das hi wai meye haka sai kace ni bakuwar kace kamin ya kankanta murmushinda yayine ta sake cewa dashi gaskiya ni bana so sai barma kayanka ka hada da kanka in haka ne ta fada ashegwabance Kalmar kuwa da tasa ya fada a hanzarce ah a’a’a ci gaba da sha’aninki ai ko ba yanzu akwai anjima inji Alhaji Yusha’u.
Aisha: Labace baki tare da yin ko oho da batunsa ta cigaba da lamarin gabanta. Bayan da yadan natsa kanna yace yauwa Aisha wai ina yarinyarnan ne?
Aisha Sunje supermarket da ita da kawarta Na’ima zasu sayo mayuka dako menene ma suka ce? Shiriritarsu dai yayin da tayi wata alama da hannu mai nuna sudai suka san kayansu.
Alhaji: Wai anya kuwa Aisha bake kike daurewa yarinyar nan gindi akan sagarci ba kuwa irin wannan yawace yawacenfa bashi da amfani
Aisha: Wallahi maigida bah aka bane idan yaune dai kawai in ka haifeshi baka haifi halinsa ba, duk abinda kace ingaya mata na gayamata ni kaina ina yin nawa dabarun amma duk a banza.
Alhaji: kinga idan ta dawo kice tasameni aciki ankai karshe dole sai ta gayamin inda ta dosa damu wannan sakarcin ya isa haka ya fada a cikin yanayi na soma nuna damuwa
(FADE)

SIN 15
ISOWARSU SALIMA A SUPERMARKET KARO NA BIYU
Salim da Na’im ke tattakalo mata takala masu hawa kosauka don fitowa daga cikin supermarket din suka kuwa sun nufi matarsu haikan don su riga sun kamala siyayyarsu zasu koma gida. Bayan da suka isa awurin motar tasu har sun bude sun saka kayan da ke rike a hannayensu ne sukatuna da cewa zasu biya har recharging din Go Tv ya yin da suka yanke shawarar canza hanyar da suka biyo domin saukin isa a gunda zasu je. Wajen da hakanne kuwa yasa suka sake yin ban hannun makfi das u Salima ya in da soma (rivers) din nasu ked a wuya sai gasu Salima sun iso amma dayake ga san motocin duka biyu masu duhune kuma bawanda yasan motar wani dalilin da yasa barin tasiri kenan. Gama parking din su Salima ked a wuya Salima c eta daya gafara fitowa a cikin motar a cikin hanzari takuma nufi cikin supermarket din yayin da Na’ima ta fito a cikin natsuwa ta kuma jingina a jikin motar da tafito a cikinta amaimakon tabi yar  uwartata izuwa cikin super market din bayan kamar mintuna basufi biyuba sai ga Salima ta dawo acikin anna shuwa wanda tundaga nesa Na’ima ta yanke hukuncin cewa Salima taga wayarta domin shine sakon da fuskar Salima ke aikowa Na’ima daga nesa da isowarta kuwa ba tare da bata lokaciba suka fada mota cike da nishadi da zolayar juna

SIN (16)
Salim ne a cikin falon gidansu bayan dawowarsu kadan ya ke dudduba jakar hannun da ya shigo da ita, domin dauko wani (emvlop) mai dauke da hotunan su shi da Na’im, bayan Na’im din ya shige acikin kuryar gidan. Amma hotuna su kace dauke mu inda ka ajiyemu, abin kuwa da ya soma sashi damuwa har sai da ya mike a tsaye saboda rashin sanin meye mafita, kai dan kankanin lokaci ma sai da ya dan soma Safa da Marwa a hankali a falon tare da damuwa  da kuma tunanin yaya za a yi. Haka dai ya rinka yan sake sake azuci yarsa, amma ya kasa matsaya daya.
SIN (17)
SALIM NE A WURIN MOTA, NA’IM KUMA YA TARAR DA SHI
Bayan da Na’im ya bullo waje ne a sakamakon rashin ganin Salim a cikin da ya barshi a zaune ya kuma hangeshi ya bude gambun motar da suka dawo da ita. Kuma a cikin yanayin demuwa yana da dudduba cikin tad a alama yana neman wani abune bayan da yayanke shawarar isowa gun yayan nasa ne ya soma tatta kowa izuwa wurinsa, isowarsa keda wuya ya ce.
Na’im: Yaya, meke faruwane? Me kake nema?
Salim: Hotunan da muka karba ne bangansuba, shi ne nake zaton ko a mota muka barsu, ko kuma suna a gun kane?.
Na’im: Haba dai, ka manta hanani ganinsu kayi, kace kai ne zaka fara morewa tukuna. Ko dai a supermarket din ka barsu ne?
Salim: Ina zaton haka, idan kuwa haka ne ai dole ne sai mun koma.
Na’im: A’a ba dai yanzu ba, kaga abinci zamuci tukuna, saboda har ma na fito dashi naga bakanan, nace bara na duba ka a waje. Kuma mantuwa indai a ____________ supermarket ne ai ba zata salwanta ba, domin su mutane ne masu amana.
Salim: to, shi ke nan imma dai sun bata da kai ta rutsa, dama ni nasan banyi kyau ba, kai ne nake tsammanin zakafi haduwa a hoton.
Na’im: kagafa yaya, duk ba wannan ake ba nifa shegiyarce ta dameni, muje mu gyara kai tukuna, yazo daga baya muzo a cigaba da wannan zancen.
CUT TO SUPERMARKET
SENCE 18
Salima da Na’ima camera zata bude a kansu, yayin da suke a cikin matsanancin al’ajabi.
Ya isheka ganin yanda suka kurawa wasu fotuna da ke ajiye a gabansu a kan teburi idanuwa. Bayan dan kankanin lokaci kuma, sai ga na’ima tayi wani dan matashin murmushi tare da kallon kawar tata Salima ta ce, “to, kuma meye wani abin damuwa a cikin wannan lamari? Ai zai naga nesa ce tazo kusa mai zuwa sama ya taka leda. Mutanen nan fa nemansu mukeyi ido rufe, sai ga alama ta nuna mun kusa mu samesu.
Salima: Haba Na’ima wannan wane irin raggon tunani ne haka? Meye mafita a garemu idan ya kasance shedanun iskokine suka shigammana al’amari, ko kuwa yau watan kunyanmu ne zaikai safe, idan ya zamu sirrin da mu kayi shekaru muna boyewa iyayenmu ne suka gano.
Na’ima: hmm! To, wai idan ma sun gane sai me? Ai kawai murnace tamu ganin hakarmu ta cimma ruwa, ko kina da wani burine da ya wuce ki mallaki Salim a duniyar nan.
Salima: haba na’ima! wannan wace irin maganace? Ai ko na amsa maganarki da eh! Ki dauka kawai ba a hayyaci na nake ba, domin sanin kanki ne Salim bashi da tamka a wurina.
Na’ima: to, idan kuwa haka ne wannan wata damace a garemu a duk sanda iyayenmu suka sake tunkaromu da maganar aure kawai sai mu nuna musu hotunan samarinmu, kinga wannan ya isa ya kwantar da hankalinsu kamin mu nemo su a duk inda suke a duniyar nan. Zance ne kuwa da ya sa Salima a cikin matukar farin ciki, bata san lokacin da ta tafa hannu da Na’ima ba tare da cewa kawata kinyi gaskiya.
FADE

SIN 19
SALIMA A BAKIN GARKA TSAYE DA AUWALLU SAI FAMAR ZUBA TA KE YI, MAHAIFIN TA YA TARAR DA SU
Salima: bayan da ta daga kofar gidan ne ba tare da wata-wata ba ta kyalla idanuwanta zuwa ga mutumin da ya sallama mata, zaton ta kuwa ya zama gaskiya domin tun kafin ta fito take nasawa a zuciyar ta wata kilama marar zuciyar nan ne Auwallu. Cin karo da shi keda wuya sai ta game fuska ta bata rai a lokaci daya ta ce “Innalillahi Wa’inna Ilaihi Raji’un, Auwallu kai ne kadai matsalar rayuwa ta duniya, da zaka mutu da na huta”. Kalmar da ta sa sai da Auwallu ya dafe kai, saboda mamakin irin yadda Kalmar ta fito daga bakin Salima. Kafin ya ce kala, ta sake ci gaba da cewa, “Wai kai wane irin marar zuciya ne? na gaya maka bana sonka, bana sonka, ka fita a haraka ta. In kuwa ba hakaba “in ba hakaba sai me ? nace imba hakaba saime ? Alhaji Yusha’u ne mahaifin Salima ke fada yana nanatawa domin itace kalmar ta dai-dai gabar maganar ta da ya sharba, ya yin girsuwar da ya yi mata a bakin garka da Auwallu tana ci masa mutunci ya kuma ci gaba da cewa, To, ki sani wannan Shashancin an kai karshensa, ya fada tare da nuna ta da yatsa kin gama naki wargin ni kuma zan soma nawa daga yau. Ya sake juyawa a wurin Auwallu ya ce, Kai yaro idan da gaske ka keyi aurenta zaka yi ka toru magabatanka nan da sati daya muyi magana da su. Zancen kuwa da yasa Salima ta fashe da kuka ta juya a guje ta koma cikin gida.
SIN 20
FLASHBACK
SALIM A SUPERMARKET YANA BINCIKEN HOTONAN DA YA MANTA
Budewar camera keda wuya sai ga Salim tsaye tare da mai Supermarket ya yin da mai supermarket ya jinjina kai tare da cewa gaskiya ne, amma abin da ya faru shi ne. sai ya daga kansa sama ya yi shuru dan wani lokaci, alamar zai tuno abin da ya wuce.
Nan take kuwa sai ga Salima ta shigo a cikin supermarket din a cikin yanayi na hanzari, ba tare da bata lokaci ba ta ajiye jakar hannunta a kan teburin da ke gaban wannan mutumin mai mu’amalar cinikayya da jama’a. Ta kuma wuce a cikin sauri da nufi kuryar supermarket din, da yake ita Salima sanannar customer ce kallo daya ya yi mata ya cigaba da sha’anin gabansa. Bayan da ya soma mayar da hankalinsa izuwa jakarda ta ajiye ne sai ya ci karo da wani ambuluf zai fadi kasa a gefen dayan jakar ne kadai ya dafeshi da tuni ya fado kasa. Ganin jakar a saman ambuluf din sai ya tsammani ambuluf din na mai jakar ne, nan take kuwa ya dauko ambuluf din ya saka a cikin jakar gudun kar ya fadi a manta da shi anan. Bayan da ya gama hakaicen labarin ne ya ce da Salim.
Mai Supermarket: To, kaji yadda abin ya faro
Salim: To, shi kenan don Allah a kara kulamin sosai ko Allah zai sa su dawo da yake bada nisa nake ba nan nake a layin nan da ke bayan ku gidan Alhaji Dauda Dan Kasuwa.
SIN 21
HAJIYA LUBA MAHAIFIYAR SU NA’IMA CE A ZAUNE CIKIN FALON GIDAN TA, YAR TA SALMA WATAU YAR NA’IMA TA SHIGO
Hajiya Luba: A’a!, me nake shirin gani haka? Shin ko dai mafarki nakeyi ne? Salma ke ce ayanzun nan da rana tsaka? Wannan shi ne abin da Hajiya Luba ta fada. Ya yin da yarta Salma ta izo kofa tare da Sallama da yake kuma sun dade basu gana ba, wannan shi ne zowarta gida tunda akayi aurenta.
Salma: Ummah na! Ummah na!! haka ta rika fada tare da shekuwa ta rungume mahaifiyar tata cike da farin ciki da annashuwa.
Luba: aw to ina surukin nawa kokuwa ke kadai kika zone ?
Salma: aa Umma atare mukazo ya tafi ya isarda sakon wani abokinsa ne kawai ya dawo kugaisa ya ya koma domin ni sati daya zanyi anan “sati daya iye wai abu nayi to isa ki ajiye jakar kihuta tukuna, “antyna antyna sannu anty Salma yaya hanya  shine abinda Na’ima ta rika fada yayinda ta kwaso gudu ta zo tayi tsalle ta rungumo yayar tata Salma ba tare da tsai tsayawaba kuwa ta shiga yimata tambayoyi kamar haka
Na’ima: aw anty salma ina Salmanunki ? ta fada acikin shagwaba da annashuwa
Salma: salmanuna yananan kalau atare mukazo dashi yananan shigowa bada jima waba, nadai fahimci suna yennan dadi suke yimaki ko Na’ima?
Na’ima: to ai sunayen ne sun hadu Antyna kijifa Salma Salman tafada tareda kwatanta yatsunta na hannaye don kamanta sunayen biyu
Salma: hmm, lallai, Umma kina jintafa ta fada acikin yanayi na mamaki tareda dora hannayenta akan lebban bakinta
Hajiya Luba : tabbi, aike komaima baki ganiba domin kuwa wasali dayannan ba karamin tasiri yake dashi awurin Na’ima da kawarta Salimaba ayanzu haka ban san inda taje ta hadu da wani Na’im ba sai famar zabga mafalkin sa takeyi amma koda rana daya bai taba tako gidan nan da sunantaba.
Salma: Allah sarki to ai Umma in sha Allahu mai wuya ta kare tunda Allah ya kawoni yanzu, naki kawai idone don kallo kunnuwa don sauraro damacan mu abokan shawarar juna ne zo mutafi kanwata Salma ta fada tare da jan hannun kanwar tata Na’ima suka nufi kuryar daki acikin nishadi mahaifiyar tasu kuwa sai kallonsu takeyi cike da mamaki yayinda daga karshe tayi wani abu da hannu alamar kudai kuka sani.
SIN (22)
SALIMA AZAUNE CIKIN FALON GIDANSU TANA KUKAN BAKINCIKI GANIN CEWA GOBENE AUWALU ZAI TURO IYAYENSA MAHAIFIYARTA TA TARARDA ITA AWANNAN  HALI.
Hajiya Aisha: salima da kuka da rashinsa duka dayane awurinki domin gobece ranar da gurin mahaifinki zaicika akanki na tarbon iyayen Auwalu da kuma badake agaresu don haka tarakai kidauki kaddara shine kadai mafita agareki komai ya faru kece kika jawowa kanki kama da dukan guduma Salima kejin wayannan kalaman da ke fitowa abakin mahaifiyar tata Aisha yayinda ta game kai da gwiwa zaune kasa jingine ajikin kujera amarmakon ta haukan kujerar falon anman ko dago kai batayi ta kalletaba balle harta nuna taji metake fada ahakan dai mahaifiyar tayi tsaki tashige kawai abinta ta barta anan tanata famar cika aikin da tasa kanta(kuka )
SIN (23)
SALIM NE ZAUNE AKAN KUJERA YAYINDA AKE GOGE MASA MOTAR DA YAKE SON YAFITA DA ITA ANA CIKIN HAKAN NE SAI IBRAHIM MAI SUPER MARKET YA TAHO YA TARADDASHI
A a Ibrahim kaine tafe adai dai wannan lokacin haka? Kalmar data futo dag bakin salim kenan bayan ya karbawa ibrahim sallamarsa har suna kokarin hada hannu da junansu
Ibrahim eh wallahi nine salim wannan adreshshi ne  mutanenka sukace inbaka idan kazo amaimakon subai hotunan inbaka to najira kwana biyu naga baka bulloba sai na yanke shawarar na sameka gidda
Salim kai mutumin yau akwai matsala amarmakon subaka hotunana kawai kabana shi ne zasu baka adreshinsu kabani menene adreshinsu zai anfanamun?
Karka damu aiwanan ba komai bane yannada
 kyau kaje kaji menene zasu fada ya yiwuma wannan yazamo sanadi wani alhairin
Salim: toshikenan babu komai godiya nake malam Ibrahim sai mun hadu ko
Ibrahim: ok to shikenan nima godiya nake
SIN (24)
Bayan salima ta dade acikin yanayi nabakin cikiki ne ta yanke sha warar tinkarar Auwalu domin yimasa magiya ko Allah zaisa tadace , da misalin karfe tara na safene Auwalu yana zaune a wata farfajiya mai ban shawa akn wata yar karamar kujera rikeda wani dan karamin littafi ahannunsa yana dubawa kwatsam sai yaji sallama kamar daga sama ba tare da bata lokaciba kuwa Auwalu ya dago kai don tan tance gaskiyar abinda zuciyarsa take raya masa nacewa Salima ce tazo wurinsa, Allah sarki kyallara idanu wansa kuwa keda wuya sai yaci karo da Salima  cikin wani yanayi mai ban al ajabi wanda ko   kusa baya tsammanin ganinta acikin irin sa domin kuwa wani murmushi takeyi irin na kunya tare da tako dai­-dai irin na yanayin zaaaaaa babu shakka karim ta yarda karasowa agunda yake sai da yakasa hakurin ta sameshi a zaune ya mike tsaye ya tinkare ta shima cike da annashuwa domin ganin yake hakar sa ta cimma ruwa.haduwar su ked a wuya, acikin alamar za a saita jan rusuna kadan tareda yimasa kyakkyawar gaisuwa kamar haka:-
Salima:- yaya auwalu barka day au antashi lafiya?
Auwalu:- yauwa kanwa ta antashi lafiya ya gidan?
Auwalu ya amsa mata cike dad a farin ciki-
Salima:- yauwa yaya auwalu don allah idan baza ka damu ba wata alfarma nazo nema gare ka.
Auwalu:- haba kanwata ki daina bata lokacin ki ki fada kawai anga ma meye bazan iya yima kiba?
Salima:- auwalu gobe ne iyayen ka zasu zo gidan mu ko?
Auwalu:- eh! Gaskiya ne wanna karfe biyar na yamma tana bugawa kuwa, ya fada acikin yanayin nishadi
Salima:- yaya auwalu kana sona kuwa da gaske?
Auwalu:- haba kwarai ma kuwa tawa.
Salima:- to don Allah ina neman kayimin afuwa yaya auwalu kajan ye zowar nan domin zai iya zama mafarin rasa rayuwa ta.
Auwalu:- haba meye haka? Me kile fadi ne haka?
Auwalu ya fada acikin yanayin tashin hankali da matukar damuwa.
Salima:- auwalu bana sonka! Bana sonka! Bana sonka! Kuma wannan shine gargadin ka na karshe inkaki kaji to kome ya faru ka zargi kanka kuma wallahi in Abba kasha ni zaiyi kasani idan iyayen naka suka zo gidan mu a gaban kowa zan cinna wuta in kona kaina  in kona iyaye naka yaso komai zai faru ya faru adai dai nan ne kuwa ta juya fusace bako sallama ta nufi inda ta fito a ciki da bakin rai  shi kuma auwalu sai dafe kai yayi hannu biyu acikin takaici da mamaki sai famar kallon ta yake har ta bace.
SIN (25)
Salma da kawarta na’ima a falon gidan, budewar camera keda wuya salma ce ta kada kai a cikin mamaki tace haba na’ima wannan ai akwai waba buna dake da kawar taki kuna cikin rudani babba. Domin kuwa jiran gawan shanu ku keyi samarin nan fa basu kosan kana yiba hasalima kudasu ba wanda yasan ina wani yake a yanzu maganar nan da akeyi;
Na’ima :- haba aunty salma nafa baki wannan labarin  ne domin ki tayani neman mafita, imfa ba keba duk gidan nan ba wanda yasan wanna sirrin.
Salma:- bayan dan suru da salma tayi ne can sai ta numfasa tace tau shikenan bakomai insha Allahu abu zaizo da sauki tunda har Allah ya sa kun sami hotunan su ta yiyu idan muka bita hanyarda hotuna suka zo ma iya samun mafita
Na’ima:- acikin yanayi na tausayi da sagwaba tace don Allah aunty ki taimaka mana kinji.
(FADE)
SIN (26)
Alhaji yusha”u ne a falon gidan sa ya kasa zaune yakasa tsaye domin yau itace ranar da yakamata iyayen auwalu su zo, amma gashi har lokaci ya soma kulewa basu zoba wannan dalilin ne kuwa yayasan yashi safa da marwa ransa abace sai kulla wa yakeyi yana kwancewa arayuwar sa kamar haka:-
Shin mutanen na lafiya kuwa kodai dama yaron nan bada gaske yakeyi bane ko kuwa dai matsala suka samu a hanyar su ta zawa ne?


SIN (27)
Budewar camera keda wuya sai ga Alhaji dauda ne a falon gidansa zaune a kan wata katafariyar kujerar da ke cikin kataparen falon. Kai daga nin Alhaji Dauda ba sai ance maka mai arziki ba ne domin kuwa irin shigarsa kadai ta isa ta bayyanar da hakan. A gefen fuskantar mahaifin nasa a cikin ladabi da kunya.
Bayan daukan lokaci kalilan sai ya rufe jarida da ke hannunsa asa adda karkatar wuyansa ke kokarin komawa gad an nasa Salim ne a cikin manyanci da cikar girma ya yauwa.
Dauda: Salim na tabbatar kafin nace komai ka san dalilin da yasa nakiraka to, sai dai bansan ko Allah Ya sa kadauki matakin kare kanka dag a sharadin da nagindaya maka kafin inyi tafiya ba, saboda nagaya maka bana tsayi jiran gawon shanu, a dai-dai wannan gabarne Salim ya shiga shafan kai da Magana a cikin kunya alamar rashin tafada kamar hakan.
Salim: Eh! Eh! Am’am Abba Na Na---
Ganin hakan ne kuwa yasa mahaifin nasa ya katse masa hanzari da cewa
Dauda: Dakata Salim na fahimce ka bawani katabus da kayi a cikin duk tsibin damar da nabaka, da yake nag ode Allah da dan cikina na ke Magana wanda yake ya sanni ciki da bai, baya bukatar tawili ko sharhin maganata in eh. Eh in kuma a’a. a’a kai ne kafi kowa sanin haka sai dai ka bawa wani labara, to, ka sani kayi wasa da damarka ta farko da kuma ta biyu, lokaci kuma ya kare ba abin da ya rage maka. Salim ta yaro kyau ta keyi amma kuma ba fa karko ta keyi ba. Kafin sauko gida nayi magana da wani amini na akan nema maka yar wurinsa da aure kuma ya bani damar hakan, sati mai zuwa rana ita yau, zamu tafi tare da kai a can kuga juna a yi maganar ta zama daya. Tashi ka bani wuri wannan itace kalmar day a rufewa Salim kofa da ita.
Ba tare da bata lokaci ba kuwa Salima a cikin sanyin jiki da rashin tayi ya tashi ya nufi kofa cike da damuwa.
SIN 28
LUBA CE DA SALMA DA NA’IMA A ZAUNE
Mamar Na’ima za ta ce: Tabdi wai jiran jira, Kare jiran tsakin mai toke, saboda Allah Salma yanzu ina zance hankali a nan?. Wata kilama samarin nan tuni sunyi aurensu sun manta da ku. Domin bawata yarjejeniyace a tsakaninku da su ba. Kawai daurare ku keyi na banza to ni bazan zan yarda da hakan ba Salma. A cikin damuwa. Bayan ta gama sauraren abin da yarta Salma ta gaya mata.
Salma: A’a Umma kar kiyi haka, ki bari mubi lamarin a hankali da ya ke sai ranar lahadi ne zan koma Abuja zanyi amfani da ranar Assabar a matsayin damar da naked a ita mutafi tare da ita gidansu. Salima itama inaso inji ta bakinta yaso daga nan zamu iya daurare ta hanyar da hotunan nan suka zo insha Allahu koma meye gaskiyar lamarin zata bayyana.
Hajiya Luba: Salma, karki daurewa yarinyar nan gindi a cikin sha’anin karya ta fada tare da nuna Na’ima da ke zaune agefe dayan kujerar, wanda ya ke ita dai ba ta ce uffan ba a duk cece kucen da mahaifiyar tad a yayar tata sukeyi.
Salma: haba Umma ai bah aka bane kinsan da rashin kira Karen bebe ya bata.
Hajiya: Bayan duk Shirun da ta yi ne tanisa tace tau ku kuka sani.
FADE
SIN 29
CAMERA NA BUDEWA
Hajiya Aisha da yarta Salima ce yayin da Aisha ta ke zaune a kan kujera yarta Salima ta dora kanta akan kafadar mahaifiyar tata sai hawayen bakin ciki ke famar kwaranya a idanuwanta. Ya yin da mahaifin ta Alhaji Yusha’u yake a tsaye yana ta famar safa da marwa agaban kujerar da suke zaune akan ta sai musiba yak eta famaryi. Adalilin zuwan da Salima ta yi wurin Auwal domin yima sa kashedi ko (Barazana).
Alhaji Yusha’u: Yanzu nasan wana Haifa kuma da wana ke zaune a gida daya, tabbas Salima tabbas kin nunamin cewa ke ci kakkiyar yar ta’addace kuma maras mutunci. To, amma kafin kije kiyi masa barazanar kona shi dashi da mahaifan nasa meya hana ki farad a mu din nan tukuna?. Ya zamana duniya ta baki lambar yabo (award) kafin ki kona iyayen wasu naki kika fara konawa.
To, bara in gaya miki in duk garin nan zai kama da wuta baza abi ra’ayin naki ba, kuma tabbas kinyi nasara a wannan karon domin iyayensa sun nuna cewa in ke kadaice Ya mace a duniya bazai aureki ba. Domin ba irinki suke nufi ba, uwa marar tarbiyya, amma kuma ki sani har wayau ina yi miki albishir da rashin sa’a domin har yanzu dai jiya iyan kinada sabon alkawarin wani akanki wanda bakisan waye shi ba, balanta na inda zaki taraddashi kiyi masa rashin mutunci kuma tabbas ranar tana cika za suzo kuma inda suka zo nan za a shafa fatihar aurenku sai naga ta tsiyar lukin iya kamin indawo ki tabbatar kin babbaka gidan nan. Kalmar da ya fada tare da buga hannun rigarsa ya sa kai ya tafi abinsa. Ita ce kuwa kalmar da tasake sanya Salima tafashe da kuka mai kara har sai da ta runtumo jikinta gaba daya akan cinyoyin mahaifiyarta ta bata ce dasu uffan ba a duk jidalin nan da ake ta zubawa.


SIN 30
Salim ne a zaune cikin wata gadinar fulawa mai ban sha’awa ya yin da Salima ta bullo masa ta baya ba tare da ya sani ba tana tatta kowa a hankali a hankali har sai da ta zo gab da shi ta bayansa sai ta karkada masa ganyen da ke rike a hannunta a gefen kunnensa na hagu, ya sa hannu ya kakkabe batare da ya waigaba kafin kace kabo tasake karkada masa abangaren dama, ya sake taba wurin kafin ajima yaji abin abayan wuyansa. Da yaji tsalguwar ta soma yawa sai ya waiga don tantance meyake faruwa namfa yaci karo da Salima ce ke da wta irin kwalliya abin sai wanda ya gani tana ga nin ya waigo kuwa saita bushed a dariya ta juya aguje tanufi inda tafito shikuwa Salim yace dawa aka hadani ba da ita ba, ya bi ta da gudu danufin ya cimmata ya kamata haka dai sukayi ta bode – bode a cikin fulawowin amma bai smau kamata ba.
SAI WAKAR DA SUKAYI TA WASALI DAYA
SALIM
SALIMA
SIN 31
Salim ne a kwance dakinsa yana yan mirgine mirgine da yan juye – juyen kai alamar zai fako daga baccin da ya keyi wanda a cikine ya yi mafarkin haduwarsa da Salima bayan day a falko ne ya zabura ya tashi zaune a hargitse yana yan salatoci. A cikin yanayin damuwa wanda said a takai ya yi tagumi idanuwansa suna kallon sama yana nazari irin halin da ya sami kansa a ciki.
FADE
SIN 32
Na’im: Hakika wannan shine abinda ya faru bayan rabuwarmu da ku amakaranta.
Salima: kamar yadda kikaji Yaya Salim ya fada yanzun nan
Salima: Ai Na’im da kai har yayanka naku wasa ne domin kuwa byaan mun rabu daku a makaranta da shekarar daya ne a kayi auren anty Salma yayar Na’ima da Salmanu abin yayi matukar burgemu kasancewar sunayensu sunzo iri daya wasali dayane ban-banci, muma muka fitinu da matsa nancin gurin samarinmu suzamo haka. Wanda nan take faruwar hakan tajefamana kakkarfan tarnaki a zukatanmu wanda ayau tsawon shekaru biyu kenan muna fama da wannan kurji a zukatammu ta yaya zamu samu irin nasarar da Auty Salma ta samu? Sai yau gashi kamar da ga sama mun hade wuri daya da ku yayin da ukubar iyaye ta addabemu akan maganar aure.
Salim: Eh, haka ne amma wani hanzari ba gudu ba Salima; Na’ima mun biyo adirehin da kuka bamu ne kawai don karbar mantuwar mu dake hannun ku amma badon kulla wata alakar soyayya ko aure ba. Domin kuwa mahaifina yayanke shawarar aurar min yar amininsa, kuma na tabbatar ta haka zai yankewa dan uwana irin mummunan hukuncin day a yanke min.
Wannan itace kalmar da take fitowa daga bakin Salim yayin da yake mikewa a cikin sanyin jiki. Daga zaunen da yake akan gaban motarda suka zo da ita. Na’im kuw na jingina a jikin motar ne kusa da shi Salima tana gefen hagunsa Na’ima kuma tana gefen damar Na’im. Itama jingine a jikin motar yayin da Salima ta kura masa ido tayi tana kallonsa da irin furucin da ya ke fitowa bakinsa.
Na’ima: tabbi jam, a she kuwa bacin yaba kafar baya kai kuwafa? Ina muka kwana? Ko kaima duk maganar dayace? Na’ima ta kalli saurayinta Na’im a cikin damuwa jejjefa masa tambayoyi amma sai kallonta kawai ya yi sanyaye a cikin mamaki batare day ace da ita uffanba.
SIN 33
Sallamar Na’im da izo kofa kusan duka daya ne, yayin da shigowarsa falon yayan mahaifin nasa Dauda ked a wuya yaci karo dashi yana yiwa yayansa Salim gargadi shigowar tasa ce kuwa tasa yayanke maganar da yake akanta yace yauwa! Na’im zonan yanzu nake ce masa idan ya fita yakira min kai. Na’im kuwa a cikin girmamawa yazo a gaban yayan mahaifin nasa ya rusuna zai zauna a kasa sai mahaifin yace dashi.
Alhaji Dauda: A’a zauna kusa dad an uwan naka wato (Salim) da ke kan kujerar daya ta gefen kafadar hagu da Alhaji Dauda bayan Na’im y agama gyara zamanne Alhaji Dauda ya ci gaba da zance kamar haka:
Dauda: Na’im da kai da Salim duk yaya nane ku, domin kuwa tun ranar da kanena wato mahaifinku ya kwanta dama  a dai – dai shekararka ta uku a duniya na karbi tarbiyarka a hannuna ganin cea mahaifiyarka bayan kasan nan bace. Bana so a ce kata shi ba a kusa da mu ba, yasa muka hanata tafiya da kai. A kasarta ta haihuwa wato (maleshiya).
Daga wannan lokacin zuwa yau ina zaton na sauke wasu daga cikin farillanku na wajabci a kaina kamar ci da sha, sutura, ilmantarwa, lafiyarku da kuma tarbiyya. A yanzu mataki na gaba shi ne maganar raya sunnar ma’aiki wato aure, daya ke Salim ya gayamin cea akwai wadda kukayi alkawari aure da ita na keso inji abakinka ko gaskiya domin inason a hada bikin naku lokaci daya ne.
Na’im: a cikin yanayin jin nauyi ya rutsa yace gaskiya ne abba. Aishima yaya Salim yana da wadda sukayi alkawali daya ke tayi.
Dauda: Dakata Na’im baruwana dawannan zancen nariga nayi alkawari bazancen kwancewa Salim yar aminina zan aura masa. Kalmar kuwa da tasa Salim da Na’im suka kalli juna a lokaci daya a cikin yanayin damuwa.
SIN 34
Salima da Na’ima ce a zaune a cikin dakin Na’ima na bacci a gidansu yayinda Na’ima take zaune a bakin gado, ita kuma Salma ta na a tsaye ne daf da kafadarta tana bata magana dangane da Halin tunanin da taga kanwar tata Na’ima tashiga.
Salma: Na’ima aurefa nufin Allah ne kuma da ce da miji kowane irin daga gareshi ne, don hakabana son ganinki a cikin irin wannan halin yakamata kalma da furucinta yazo dai-dai da ringin din da wayar Na’ima tayi wannan ya zama sanadin dakatar da zancenda Salma takoroyiwa Na’ima domin tuni hankalin Na’imar ya juya izuwa ganin wane irin sako ne tasamu a wayarta ta, nan take kuwa Amadadin yanayin fushin da take ciki sig a wani dan saurayin murmushi yak e to fuskarta ta ganin cea sakon daga Na’im ne bada bata lokaci ba kuwa ta soma karanta sakon kamar haka: Assalamu alaikum, Masoyiyar rayuwa tan a tabba ta tsawon kwanaki hudu da muka rabu da juna kina a cikin irin halin da nasami kaina a ciki na damuwa, amma yau ina mai yi miki albishir da cewa Abba ya bani damar zabin mata dakaina wanda tuni kin sani na sani kece zabi na. amma sai dai kash Yaya Salim ya kasa samun irin wannan damar, domin kuwa Abba ya nace akan bakarsa tacewa sai yar amininsa da sukayi alkawari dashi.
Daya ke karatu ne da takeyi a bayyane Salma ta riga taji komai Na’ima na kai suratun wasika ne tace da ita To, kinga ga maganar wan an tafara fitowa dadin hakurin kenan. Yanzu sai dai mutaru mutaya Salima ad addua’ar dacewa itama. Alokacin nan kuwa da Salma ke wannan zancen fuskar Na’ima cike take da annuri ganin cewa burinta zai cika bayan da hartana ganin kamar ya kubuce mata.
SIN 35
Salima da Na’ima da Na’im da Salim ne suka jero akan hanya suna tafiya suna hira harma da dare-dare. Kwatsam, sai su kaji kamar daga sama anhada birki a gabansu, yayinda suka ankara wata motace ta alfarma ta bayyana agabansu, amma tuni Salima da Na’ima sun gane ko wane ne sai dai Salim da Na’im sai mamaki kawai su ke yi tare da daukar abin amatsayin rainin wayo na musamman. Kai abinfa kamar wasa karamar magana ta zama babba domin tsaya war motar ke da wuya sai Alh. Yusha’u Baban Salima da ya ke shi ne jaye da motar yayi wuf ya bude ganbun motan ya futo da hanzari yana cewa ke
Alhaji Yusha’u: Salima ba na hanaki sauraron ko wane saurayi ba in dai ba wanda na tsayar maki ba?. Salima da Na’ima tuni sun sha jinin jikinsu tun kafin faruwar hakan sai faman kyarma su ke yi da kuma alamar I’inniyar magana, amma basa iya furta komai saboda rashin hujja. Nan take shima Alhaji Dauda ya bude gambun motarsa ya fito cike da mamaki
Alhai Dauda: Salim, Na’im! me zan gani haka? Su waye wadan nan? Hauka ku ke yi ne?.
Alhaji Yusha’u: Amm! Alhaji Dauda dama ka kansu ne?
Alhaji Dauda: “Ai yaya na ne, wannan shi ne salim din da nake nemawa yar wurinka.
Alhaji Yusha’u: Ikon Allah ai wannan itace Salima ‘Ya ta da na yiwa Danka alkawarinta.
Alhaji Dauda: Allah Sarki!, tuwo na maina kenan. To, dama kunsan juna ne? ya kalle ya tambaya
Na’im ne ka dai ya samu damar magana.
Na’im: Abba dama ai wannan itace Salima wacce Yaya Salim ya ke so tun da dewa amma gudun ya keta umurnin ka ne ya sa ya ki ya gayamaka.
Duk zancen nan da ake kuwa, Salim da su Na’ima kawunan su a sunkuye ne alamar jin kunya.
Alhaji Yusha’u: To, kai kuwa fa, Na’ima ko? Shawaraki. Ya fada a cikin yanayin dariya cike da farin ciki.
Na’im shi ma ya soke kansa a kasa, ya shiga layin yan uwansa
SIN 36
Salma ce da Salima da Na’ima da Mahaifiyarsu Na’ima Hajiya Luba a cikin gidansu suna al’jabin wannan babban al’amarin da ya faru
Salma: To, kunga abin da nake gaya muku yau ga magana ta ta fito dama ance mai hakuri ya kan dafa dutse harma ya sha romunsa.
Hajiya Luba: To, Fadi dai ke, wayan nan yaran, wayan nan yaran, nacin su ba kadan bane. Da wannan gurin nasu bai cika ba da ba’asan ya za a kwashe da su ba. Ta fada tare da nuna yar da Na’ima da yatsa.
Na’ima: Wallahi Umma ji muke kamar an saka mu----
Salima: A aljanna ko kawata?
Salima ta idar mata da zancen da ta fara har ma suka tafa hannaye da juna a cikin yanayin farin ciki.
Hajiya Luba: Kaicu!, kinga marasa kunya ko?
Salima: Ayyah! Umma ai ba rashin kunya bane farin ciki ne suke bayyanawa, irin na masoyan zamani.