1.3 AMFANIN KWAMFUTA
Abin da zai biyo baya shi ne, kaɗan daga cikin amfanin kwamfuta a wannan rayuwa tamu ta yau da kullum:-

1.3.0 Sauri Mai Yawa
Kwamfuta ita ce mafi saurin na’ura 
   ·       Kwamfuta na dauƙar bayanai masu girma/yawa
  ·       Kwamfuta na raba saurinta cikin  abin da bai cim ma daƙiƙɗaya ba. Tana gudanar da miliyoyin lissafi cikin abin da ya ƙasa ga daƙiƙa, wanda yake idan aka misalta shi da mutum da zai ɓata watanni yana gudanar da aiki ɗaya. 

1.3.1 Dai-daito
Bugu da ƙari kuma bayan sauri da himma da kwamfuta take da shi haka kuma tana da cikakkiyar daidaito ko ace daidaituwa kwarai da gaske.
  ·       Kuma kwamfuta na iya gudanar da lissafi 100% ba tare da samun kuskure ba.
  ·       Kwamfuta na iya gudanar da kowane irin aiki 100% tare da cikakkiyar daidaito.
1.3.2 Damar Ajiya
Ƙwaƙwalwa na da muhimmanci ƙwarai da gaske ga kwamfuta, ƙwaƙwalwa wata dabi’a ce mai taka rawar gani sosai ga kwamfuta. 
  ·       Kwamfuta nada isasshiyar ma’adana fiye da ɗan adam.
  ·       Tana iya adana bayanai masu ɗinbin yawa.
  ·       Tana adana abubuwa iri daban-daban misali; hotuna, bidiyo, rubutu, sauti, da sauransu.
1.3.3 Himma ko Ƙwazo
Saɓanin mutane, ita kwamfuta ba ta gajiya, ba ta kuma buƙatar mataimaka wajen gudanar da aikinta.
  ·       Kwamfuta na aikin ta ba tare da tsayawa ba, kuma ba tare da kawo kowane irin matsala ko rashin jin shauƙi ga aikin da take gudanarwa ba.
  ·       Ta na kuma iya maimata aiki ɗaya ba tare da naƙasa ko gajiyawa ba.
1.3.4 Rashin Ƙasawa
Kwamfuta na’urace wacce bata ƙasawa
  ·       Kwamfuta na’ura ce wacce ba ta ƙasawa a wurin gudanar da ayyuka ko kuma wajen tafiya daidai.
  ·        Na’urar tana iya wanye ko daidaita matsalolin da suka shafi fannoni iri daban-daban.
  ·       A lokaci guda, zata iya kuranye  ko kawar da matsala maigirma da ta shafi harkar kimiyya, kuma a wannan halin kana iya yin wasa (game) da ita.


1.3.5 Aminci
Kwamfuta na’ura ce amintacciya ko abin amincewa.
  ·       Kwamfutocin zamani yardaddu ne wajen rashin yawan kawo matsala, suna ɗaukar lokaci mai tsawo ba tare da sun kawo wata matsala ba.
  ·       Na’urar kwamfuta an yi ta ne don abubuwa su sauƙaƙa.
1.3.6 Aiki da kai
Kwamfuta na’ura ce dake iya gudanar da aiki ita kaɗai ko kuma in ce aiki da kanta.  
  ·       Aiki da kai yana nufin tana da damar gudanar da aiki ita kaɗai ba tare da mataimaka ba idan har an shirya mata aikin kuma an ba ta umurnin yin haka, ma’ana idan ta adana bayanin da aka ba ta a cikin ƙwaƙwalwarta shi zai ba ta damar aiwatar da aikin ba tare da mutum ya taimaka mata ba.
1.3.7 Raguwar aiki da takarda
Aiki da kwamfuta don adana muhimman abubuwa a ma’aikatu na zama sanadiyyar rage wanzuwar aiki da takardu da kuma saurin gudanar da aiki a cikin ƙanƙanin lokaci.
  ·       Idan an adana bayanai a cikin na’ura mai aiki da wutar lantarki zasu zauna ne har sai lokacin da aka neme su don a yi amfani da su. Kun ga kenan kamata ya yi makarantu su nemawa kansu da kansu sauƙi ta wajen aiki da kwamfuta idan zasu ɗauki sabbin ɗalibai. Don haka matsalar tara tari-tarin fiyil zai ragu.

1.3.8 Sauƙi Wajen Kashe Kuɗi
  ·       Ko da yake a farkon jari a harkar kasuwanci, sanya kwamfuta abu ne mai wahala amma yana kuma kawo sauƙi wajen zirga-zirga da kuma kawo cigaba wajen harkar tattalin arziki.

1.4 RAUNIN KWAMFUTA
Waɗannan bayanai da zan zana a ƙasa su ne illoli ko rashin amfanin na’urar kwamfuta a wannan rayuwa tamu ta yau:-
  ·       Kwamfuta na’ura ce wadda ba ta da tunani, hankali da kuma basira. A ƙashin kanta ba ta iya gudanar da komai.
  ·       Kowane irin aiki zata yi dole ne sai an sanar da ita shi kafin ta aikata shi.
  ·       Kwamfuta ba ta iya ɗaukar kowane irin mataki da kanta. 
  ·       Duk abin da zata yi tana ƙarɓa ne daga mai amfani da ita, don haka ya zama wajibi duk abin da zata gudanar yafito daga mutum ne.
1.4.0 Muhalli
  ·       Tabbas muhallin da zaka adana kwamfuta ya zama mai tsafta kuma ya ƙasance wuri ne da ba ƙura.
1.4.1 Rashin Ji
  ·       Kwamfuta ba aba ba ce da ke ji ko gani ko kuma ta iya gudanar da wani tunani da kanta.
   ·       Ba ta iya yanke hukunci.  
  ·       Bata iya ji ko ɗanɗano ko yin wani abin gwaninta ko kuma aiwatar da wani abu na ilimi saɓanin mutum.