5.8 SAKO TA HANYAR SADARWA (I-MEL)
Abin da yake nufi shi ne saƙo ta hanyar sadarwar yanar gizo (Electronic Mail) (E-mail).
I-mel wata hanya ce da ake iya bi domin musayar wasiƙu tsakanin kwamfutoci guda biyu ko fiye da haka. Waɗannan saƙwannin da mutum zai iya aikawa sun haɗa da rubutu, hotunasauti, da kuma hoto mai motsi (video) a lokaci guda.
I-mel yana da matuƙar amfani ga ayyuka na yau da kullum domin buƙatuwarsa a wannan lokaci ya kai buƙatar da ake da ita ta wayar tafi-da-gidanka. Kasancewa a dukkanin harkoki da hulɗar da ake yi da mutane za a iya musayar rubutu ko magana ko hotuna.
Ɗalibai suna amfani da akwatin i-mel dinsu domin ajiyar takardunsu, da kuma bincike da suka yi domin sake amfani da shi, kuma aikawa malamansu. Masu neman aiki suna amfani da akwatin i-mel wurin ajiyar takardunsu da na shaidar kammala karatunsu domin aikawa zuwa ga kamfanoni masu neman ma’aikata.
Kwamfutocin da ake amfani da su domin zama uwar-garken saƙwannin su ne (maiframes computers) da (mini computers). Irin waɗannan kwamfutoci guda biyu suna da tsarin da yake ba su damar karɓa da kuma iya aikawa da saƙon da mutane ke aikawa zuwa ga abokanan huldarsu.
Bayan mutum ya gama rubuta wasikar da zai aika yana buƙatar adireshin wanda zai aikawa, ta wannan hanya ce kaɗai wanda ake son ya sami wannan sako zai iya samu. Aikawa mutum guda sako ko kuma aika ma mutane da yawa shi ake kira da “Broadcasting” a tsarin ilimi na i-mel. Sannan saƙwanni da zasu iya zuwa ta hanyar imel suna da alama ta ‘@‘.
Cikakken yadda kowane tsarin sunan akwatin mutum na i-mel yake shi ne kamar haka: sunanka@misali.com wanda sunanka shi ne sunan da ka zaba ya wakilce ka a duk lokacin da za a aiko maka da saƙo.
Alamar @ wacce itace ke biye da sunanka ita wannan alamar na nuna cewar wannan zai tafi ɗakin ajiya da kuma kai saƙo ne, duk saƙon da ake son a aika matuƙar ba a saka wannan alama ba to ba zai taɓa tafiya ba.
Misali.com shi kuma yana fadar uwar-garken da zai aika da saƙon, saboda haka duk saƙon da ba a saka uwar-garken da za shi ba to ba zai tafi ba. Saboda haka kana buƙatar waɗannan abubuwa guda uku kafin saƙonka ya zo gare ka ko kuma ya tafi wurin wasu mutane. Sannan kuma babu sarari (space) tsakaninsu.
Ba zaka iya aikawa da wani saƙon i-mel ba sai idan ya kasane kana da akwatin da zaka iya amfani da shi wajen aikawa da kuma karbar saƙo na email. Wannan akwati shi ne ake kira da “email account. Misalin akwatin sakon shi ne www.yahoo.com ko www.naij.com ko www.hotmail.com ko kuma www.gmail.com da sauransu.