*****       *****       *****
GABATARWA
Kwamfuta ta taka muhimmiyar rawa cikin rayuwarmu ta yau da kullum. Bugu da ƙari  kwamfuta ta taka rawar gani a harkar sadarwa na yaɗa labarai kamar talabijin, rediyo da kuma jaridu. A halin yanzu mun sami mafi sauƙin hanyar sadarwa. Muna amfani da kwamfuta don mu tura saƙon imel, hira da ƴan uwa da abokan arziki, muna kuma gudanar da bincike a yanar gizo muna amfani da ita wajen tattauna abin da ya shafi harkar ilimi. Amfanin kwamfuta ba a nan kaɗai ya tsaya ba, muna amfani da ita makarantun zamani wajen koyar da ɗalibai, haɓaka tattalin arziki da kuma gudanar da kasuwanci da aikin gwamnati, sayen tikitin jiragen sama, da sauransu.
Abubuwan da suka fi burgeni a wannan harkar ta na’ura mai ƙwaƙwalwa sun haɗa da; a duk lokacin da muke mu’amalantar waɗansu kafafen yaɗa labarai, kamarsu gidajen talabijin, rediyo, jaridu da sauransu, kai tsaye sai mu sami bayanai masu gamsarwa a lokacin da muka ziyarci shafukansu dake kan yanar gizo da kwamfuta.
Wannan littafi mai suna “Kimiyar Na’ura mai ƙwaƙwalwa (Kwamfuta)” shi ne matattakala ga kimiyar Na’ura mai ƙwaƙwalwa a wannan zamani. Dukkan ɓangarorin ilimi suna da alaƙa da harkar kwamfuta.
Wannan kundin, ya ɗauki kaso mafi tsoka wajen ganar da mafi sauƙin hanyar koyar da ɗalibai na kowane ɓangare na ilimi da ka sani.
Na’ura mai ƙwaƙwalwa muhimmiyar abokiyar tafiya ce kuma babbar hanyar gabatarwa ce don cim ma nasara ga ilimin kimiya.
SHARAHBIL MUH’D SANI
25th Sha’aban, 1436AH
10th June, 2015CE

*****       *****       *****
*****       *****       *****
GAME DA LITTAFI
Wannan littafi an shirya shi ne domin kawo cigaban masu koyo, masu burin lakantar ilimin kwamfuta a kimiyance da sanin halayenta da kuma aiki da ita.
Wannan littafi malami ne mai matukar amfani ga daliban Babbar Makarantar Sakandare da Jami’a; masu karatun ilimin kimiyyar kamfuta; injiniyanci, kasuwanci da dai sauransu. Wanda yake a hakikanin gaskiya gabatarwar kwamfuta yana cikin manhajar (tsarin) koyarwar wannan kasa tamu (Nijeriya).
Bayan kammala wannan littafi dalibai zasu sami kansu a matsakaicin matsayi na gwaninta a cikin ilimin kimiyya na kwamfuta, wanda yake daga nan zasu iya dorawa zuwa wani matsayi na ilimin, don morewa da cin gajiyar ilimin ba tare da wani kalubale ba.

*****       *****       *****