BABI NA ƊAYA
1.0 MANUFA
Kimiyar Na’ura mai ƙwaƙwalwa (Kwamfuta) ya ƙunshi tubalin ganarwa ga mai karatu tare da taƙaitattun bayanai akan abin da ya shafi harkar kwamfuta, ya kuma zaƙulo wani sashe a harkar yanar gizo da yadda za a samu amfani a harkar kimiya ta kwamfuta. A cikin littafin an bada wasu shawarwari masu amfani da mai amfani da kwamfuta zai kula dasu da sauran su.
Littafin zai ba ɗalibai damar sanin matakin aiki da samun ilimi ga abinda ya shafi harkar kwamfuta da kuma yadda take aikiBayan duba wannan littafi ɗalibai zasu iya kirkiro tambayoyi game da kwamfuta da za su samar da ma'ana tawajen tattaunawa a cikin aji.
1.1 MA’ANAR KWAMFUTA
Kwamfuta na’ura ce mai amfani da wutar lantarki da ke karɓar (ɗaukar) bayanai kuma ta sarrafa bayanan ta hanyar ba da umarni. Sannan ta bayar da amsar umurnin da aka ba ta.
1.2 HALAYYAR KWAMFUTA
Dukkanin (dijital) kwamfuta ta ƙunshi sharuɗɗa guda biyar waɗanda take amfani da su.
   ·       Ɗaukar bayanai domin shigarwa
  ·       Adana bayanai a cikin ma’adanar ƙwaƙwalwarta (memory) sannan tana iya amfani da bayanin da ta adana a lokacin da aka buƙace shi
  ·       Tsara bayanai da kuma sarrafa su ko juya su zuwa ga bayani mafi kyau
  ·       Bayar da sakamako
  ·       Kula da dukkan waɗannan matakan guda huɗu
Waɗan nan su ne abubuwan da (dijital) kwamfuta ta ƙunsa.