AUREN FARIN CIKI








"Ya Ubangijinmu! Ka bani zuriyya mai kyau daga gunka. Lalle ne Kai mai jin addu’a ne ( ga abin da kuke roko)." (3/38)
















SHARAHBIL MUHAMMAD SANI 
08113777717



Auzu Billahis-Sami’ul Alim, Minash-Shaidanir Rajim. Bismillahir Rahmanir Rahim.
Godiya ta tabbata ga Allah madaukakin Sarki kuma aminci ya tabbata a bisa zababben jakada Shugaban Annabawa Muhamamd Dan Abdullahi wanda aka saukarma fiyayyen littafi (Al-Kur’ani) domin ya zama shiriya da kuma waraka ga muminai. Yarda da aminci su kara tabbata a bisa iyalan gidansa da sahabbansa da kuma muminai har ya zuwa ranar karshe.
Bayan haka: Lalle Allah madaukaki Ya kimtsa mini kuma Ya taimakeni akan na tarawa kaina da yan uwana wani abu na daga fadakarwa kan babban al’amari da kuma kalubale da ke gaban kowane Uba da Uwa  da matashi da kuma matashiya masu shirin yiwa yayansu aure da kuma masu shirin nemawa kansu mataye ko mazaje nagari domin wanzuwar zuriya mafi kyau a cikin al’uma.
Hakika na cirato wasu bayanai daga wasu kasidu da kuma fadakarwa daga wurare daban-daban tare da amfani da Ayoyi da Hadisai kadan ba dayawa ba, don ganin na cinasarar tsara wannan littafi. Ina yiwa dukkan wadanda nayi amfani da wani abu nasu ta hanyar kafa hujja godiya da kuma fatar Allah Ya biyasu Ya amfanar da su da ni da kuma Al’umma daga wannan littafi amin.
Ina mika godiyata ga Iyayena wadanda sune suka bani tarbiyya har zuwa ga wannan hali da na tsinci kaina a cikinsa. Ina rokon Allah Ya raya mu tare da su Ya kuma kyautata rayuwarsu da mu Ya yiwa rayuwar albarka amin.
Daga karshe kuma ina rokon Allah Ubanginmu Maigirma da Ya sanyawa littafina “AUREN FAFIN CIKI!!!” karbuwa da amfani da albarka ga wanda zai karbe shi ya yi aiki da shi domin amfanin kansa da kuma al’uma baki daya, kuma Ya sanyamu daga wadanda Ya yarda da su a wajen fadi da aiki, lalle Shi ne Managarcin Maijin kai.
Sharahbil Muhammad Sani
Makera
08th Shawwal, 1437AH
14th July, 2016
GABATARWA
Auzu Billahis-Sami’ul Alim, Minash-Shaidanir Rajim. Bismillahir Rahmanir Rahim.
Zanso infara gabatarda godiyar Allah daya bani damar fara wannan aiki mai kunshe da ababe muhimmai da ya kamata duk kanin iyaye da matasa su sansu domin kaucewa badakalar da muke fadawa ta fitintinun kuskurewa wajen zaben abokin zaman rayuwar aure tsakanin mace ko namiji wanda a sanadiyar faruwar hakan rayuwa zata shiga da-na-sani na har abada. Babu shakka abisa sanadiyar kuskuren yin zaben da bai dace ba imma ta wajen duba can-canta ko kuma rashin bin ka’idojin da suka dace wajen zaben abukin zaman aure. Da ikon Allah wannan littafi zai fito mana da wasu muhimman abubuwa da ke nesa kusa domin saukakawa ga masu manufa ko shirin yin aure.

Wannan littafi gata ne kuma hanya ce ta cin nasara da murewa yin AUREN FARIN CIKI, auren da babu da-na-sani acikinsa har abada tare da samun kyakkyawar zuriya daga wajen Allah (S.W.T), Allah Ya sa haka ya kasance amin.

Ina fatan Allah Ya karbi wannan aiki nawa Ya kuma gafarta mini ya kuma gafartawa Iyayena wadanda sune sanadin zuwa na wannan duniya tare da Iyayensu da kuma muminai da musulmai maza da mata masu rai da matattu da kuma wadanda zasu zo nan gaba. Ina rokon Allah Ya sanya mu daga wadanda Ya yarda da su a wajen fadi da aiki, lalle Shi ne Managarcin Maijin kai.
Sharahbil Muhammad Sani
Makera
08th Shawwal, 1437AH
14th July, 2016






ME AKE NUFI DA KALMAR AURE?  
Idan akace aure, ana nufin hada wasu abubuwa guda biyu da zasu yi alaka da juna amma kuma jinjin su ya saba. Misali; hada namiji da mace.
Aure a shari’a kuma aure sunna ce daga cikin sunnonin annabawa kuma sunnah daga cikin sunnonin da Manzon Allah (S.A.W)

ME YASA AKE AURE?
Babu shakka akwai falala mai girma a cikin ibadar aure kuma hanya ta farko da za a bi domin samun wannnan falala shi ne ayi nufin yin aure domin Allah a kuma kaucewa kwadayin duniya ko wata manufa da ake so a cimma a rayuwa. Kuma a yi auren kamar yadda annabi muhammad (S.A.W) ya tabbatar, idan akayi haka to babu shakka aure ya zama aure kuma ga shi anyi shi da a tsarkaka niyya da nufin yi don Allah idan akayi haka za a samu falala da nasararorin da ke cikin al’amarin aure da iyawar Allah (S.W.T).

Daga cikin muhimmancin yin aure ga mace ko namiji akwai hadisi daga manzon Allah (S.A.W) inda ya ke cewa "Idan bawan Allah Yayi aure, to ya cika rabin addininsa". Don haka aure wani babban al’amari ne da ya ke kunshe abubuwa masu muhimmanci a cikin rayuwar dan Adam.

ME AKE NUFI DA IYALI
Idan akace iyali ana nufin wani tubali a cikin al’umar musulmi. Za a iya cewa Iyali; wani farin ciki ne da kariya tare da kuma rufin asiri daga Allah Ya halitta a cikin ko wane jinsi na dan Adam.

Abin sha’awane ga musulmi kuma abin alfahari ne ga addinin musulunci mutum musulmi ya tara iyali ya hayayyafa, tare da samun kyakkyawar tarbiyya da za a yi alfahari da ita nan gidan duniya kuma manzon Allah (S.A.W) zai yi alfahari da ita a ranar alkiyama. 

ME YASA IYALI KE DA AMFANI A MUSULUNCI?
Kamar yadda na gabatar a ma’anar iyali. Babu shakka iyali abu ne mai matukar alfanu da mutum zai yi alfahari da su zai natsu na dasu kuma zai samu walwala. A lahira kuma Manzon Allah (S.A.W) zai yi alfahari da ita don haka ko anan kadai muka tsaya wannan bayani zai isa mu fahimci alfanun iyali.

Don haka mu sani cewa mace nada kwarjini da kima da ya kamata a kyautata mata kuma a tausaya mata saboda irin girmamawar da ta samu a cikin shari’ar musulunci.

ZABEN ABOKIN ZAMAN AURE
Yaku yan uwa na makaranta wannan littafi nawa abin sani anan shi ne zaben abukin zaman aure abu ne mai girma sosai abu ne da bai kamata a dauke shi da wasa ba. Abin sani shi ne zabe nagari zai yi jagoranci ga samun albarkar aure, idan har ba a yi zabin tumun dare ba to lallai akwai tabbacin gida zai ginu kuma za a samu zuri’ar da za a yi alfahari da ita Insha Allahu ta’ala.

Kowa ya sani cewa aure na samun tabbatuwar nasara ne idan har aka bin dokoki wajen yin shi ma’ana ba a sabawa shari’ar musulunci ba lokacin da za a zabi abukin zaman auren. Yaran da za a haifa a cikin wannan aure da aka bi dokokin musulunci zasu zama cikakkun masu biyayya kuma musulmi na gaskiya. Zasu samu wani sauti na adalci da kuma wani babban matsayi da daukaka duk sabuda irin wannan auren da akayi. Ilimin addini da kuma gudanar da shi aikace zai zama abu mai sauki garesu tun daga tashinsu (yaran).

Manzon Allah (S.A.W) Ya umurce wadanda ke da nufin yin aure da su aure masu addini a matsayin abokan zaman aure. Abokin zaman da duk ke da kyakkyawa da kuma fahimtar musulunci to, hakika shi ne mutumin da ya can-canta ya zama abokin zaman aure mai makon rike wuta da cewa nifa sai yar fara ko da mayyace ko ni sai mai duniya zan aure, ina nika yadda inyi aure cikin wahala, abin sani shi ne shi arziki wata taska ce daga wajen ubangiji kuma shi ne da iko da ita, kuma mai iya azirta wanda yaso ne don haka mu kauda kanmu daga irin wadannan shubuhohi. Ko kuma kaji ana cewa sai yar gidan wani ko sai dan gidan wani zan aura duk wadannan wasu abubuwa ne da ake iya fadawa a da-na-sani daga baya. Don haka ina babu shawara a bisa shawarar manzon Allah (S.A.W) da cewa mu kira mai addini ko da kuwa hannunsa yana ja ga kasa.

Manzon Allah (S.A.W) ya ce "Idan wanda kuka yarda da addini da dabi’unsa yazo muku to, ku aurar masa, .…". (Tirmidhi Sharief)     

A halin da muke a ciki duniya ta karkatar da al’uma ga kallon dukiya da kallon matsayi to, wannan ban ce laifi bane duban wannan sai dai kuskure ne babba da ya kamata mu lura da shi, idan har anyi dace da mai kudi mai nasaba mai kyau ga kuma addini sai a godewa Allah, an dace sai fatar samun zuri’a nagari.

Haka kuma, idan aka yi  sa’ar rashin kyakkyawan shimfidar addinin abokin zama, abubuwa sun lalace kuma sunyi muni.

Mace musulma wadda ta fahimci karantarwar addininta na musulunci makawa babu ta kai makura wajen wayewa kuma takai makura wajen cikarta mace don haka idan har za ta zabi miji to, ta yi duba da irin matsayi da kimar da Allah Ya yi mata ta zabi wanda ya cancanta. Kada ta yi duba ko ta damar da kanta da cewa tunda ta tara ilimi ta fahimci addini to kamata yayi itama ta dan shana ta mori duniya, don haka bari ta zabi kyakkyawa ko wani mai babban matsayi ko wanda ya tara abin duniya ya ke cin duniyarsa bisa tsinke ko dai wane irin abu ne da zai iya jan ra’ayin ya mace. Abin da ya dace da ita tayi duba zuwa ga matsayinsa a cikin addininsa ko a cikin al’amurran addini da halayyarsa da dabi’unsa saboda wadannan sune ginshikin samun nasara da dacewa da auren farin ciki. 

Zamu cigaba Insha Allahu