1.5 AIKACE-AIKACEN KWAMFUTA
Wannan bayani ne na irin aikace-aikacen da kwamfuta take yi, ga su kamar haka:-  
1.5.0 Kasuwanci
Ita kwamfuta dama halayyarta ce gudanar da lissafi, himma, daidaituwa da kuma tabbacin samuwar aminci daga gareta, kuma dole ya ƙasance ga kowace masana’anta ko ma’aikata su sami waɗannan abubuwa don cimma nasara a cikin tafiyar su.
Ana aiki da kwamfuta a masana’anta ko ma’aikata wajen gudanar da:-
  • Lissafi
  • Bincike kan harkar saye da sayar
  • Tsare tushen bayanan ma’aikata
  • Tsare hannun jari, da sauransu
1.5.1 Saye da Sayarwa
Aɓangaren saye da sayarwa, Kwamfuta na da matuƙar amfani kuma ana gudanar da waɗannan abubuwan kamar haka:- 

  • Talla- A kwamfuta; tallata sana’a al’ada ce da ta yi fice sosai wurin jama’a ta hanyar hoto da rubutawada kuma bugawa da watsa talla tare da burin sayar da kayayyakin da aka tallata. 
  • Sayen kaya daga ƙasashen waje zuwa cikin gida abu ne mai yiyuwa, ta hanyar yin amfani da na'ura mai ƙwaƙwalwa tare da samar da damar yin amfani da samfurin bayanai da kuma yarda kai tsaye wajen shigar da umarnida za a cika tare da abokan ciniki. Zaka a iya tallata hajarka a kwamfuta da manufar sayarwa. 
  • Yin cinikayya ko saye, abu ne mafi sauƙi da ake gudanarwa a kwamfuta.
 1.5.2 Ma’ajiya (Banki)
A wannan lokaci da ake ciki, bankuna gaba daya sun dogara ne ga kwamfuta.
Bankuna suna amfani da kwamfuta ta waɗannan hanyoyi :-
   ·       Buɗe asusun ajiya ta hanyar yanar gizo, wanɗada suka haɗa bincikar ragowar kuɗin asusu. Sanya kuɗi. Tura wa wani kuɗi. Saka hannun jari, da kuma halastaccen ɗaukar faifai ko bayanai.
   ·       Na’urar ATM ta kawo sauƙi ga abokan hulɗar kasuwanci da ke hulɗa da bankuna.

1.5.3 Ilimi
ɓangaren ilimi kuma, Kwamfuta ta taka muhimmiyar rawa kamar yadda zamu karanta abin zai biyo a ƙasa kamar haka:-
  ·       Amfani da kwamfuta yana cikin abubuwa muhimmai wajen tsarin ilimi wanda muka sani da suna CBE wato (Computer Based Education)
   ·       CBE ta ƙunshi kula, ceto da kuma kimanta harkar koyarwa.
  ·       Akwai hanyoyi da yawa na koyarwa da kwamfuta, kuma manyan makarantu suna amfani da kwamfuta don su koyar da ɗalibansu.
  ·       Ana shirya bayanai game da sakamakon jarabawar ɗalibai da sauransu.

1.5.4 Kula da Lafiya
Kwamfuta ta zama wani abu mai muhimmancin gaske a cikin dukkanin ɓangarorin tsarin magunguna.
Ana amfani da ita a asibitoci don adana bayanan mai rashin lafiya da kuma magunguna. Sannan ana amfani da kwamfuta wajen gwajin marasa lafiya, domin a gano asalin ciwon da ke damunsu, ko kuma gano takamammen rashin lafiyarsu tare da gano kala daban-daban na cutar marasa lafiya. Ana kuma ultrasounds, CT Scan, da sauransu. Waɗannan duk kansu suna faruwa ne ta hanyar kwamfuta.
Wasu daga cikin muhimman abubuwan da kwamfuta ke yi a harkar kiwon lafiya sun haɗa da:-
  ·        Tsarin gane asalin cuta:- Kwamfuta na amfani da karɓar bayanai wajen bambanta ko gane dalilin yin rauni ko ciwo.
   ·        Tsarin gane asalin bincike:- Dukkan gwajin da aka gabatar da kuma bayanan da aka samu, suna samuwa ne tahanyar kwamfuta.
   ·       Tsarin kula da Marasa Lafiya:- Wannan yana nufin bincike kan mara lafiya don gano ko ya samu sauƙi, waɗannan duk kwamfuta ta na tattare da su, da sauran su.
  ·       Tsarin bayanai kan magunguna:- Kwamfuta ita ke bincike kan matsayin magani domin gano ingancinsa, yaushe zai lalace ?, illar da yake haifarwa ajiki da sauransu.
Awannan zamani ana amfani da kwamfuta wajen gudanar da aikin fiɗa  (tiyata).

1.5.5 Aikin Injiniyanci da Zane-Zane
A cikin harkar injiniyanci da zane-zane na kimiyya, kwamfuta nada faɗi sosai wajen amfanin da take a ɓangaren.
Mafi girman sashe na farko da ya kamata mu yi magana kai shi ne (CAD) ma’ana (Computer Aided Design) shi (CAD) ya ƙunshi ƙirƙira, gyara ko kwaskwarimar hoto. Wasu daga cikin amfaninsun haɗa da:
 ·       Na'ura mai ƙwaƙwalwa na da faɗi wajen amfaniaikin injiniyadalilai faɗin haka shi ne.
Kwamfuta na ɗaya daga cikin manyan fannonin CAD. CAD na samar da sura ko halittada kuma gyara ga hotoWasu filayen su ne:-
  ·       Tsarin Injiniyanci:- Yana buƙatar faɗaɗbincike da ake buƙata domin zanen jirãge, gine-gine da sauransu.
 ·       Masana'antun Injiyanci:- Na’ura mai ƙwaƙwalwa na da alaƙwajen zanekawo cigaba da kyautatawa wajen tsarin kaya da abubuwan mutane.
  ·       Zanen Injiyanci:- Kwamfuta mataimakiya ce wajen kyautata tsarin yanayin garuruwazayyana gine-gineƙayyade wani kewayayyen gini ko gine-gine kan wani shafi2D ko zanen 3D.

1.5.6 Aikin Soja
Na'ura mai ƙwaƙwalwa na da amfani wajen ba da tsaro. A wannan zamanin makamai masu linzamida sauran makamai masu amfani waɗanda ake so su samu cikakkiyar kula da walwa da tsariWasu wuraren sojoji da ake yin amfani da kwamfuta su ne:
·       Kiyaye harsashi
·       Sadarwar Sojoji
·       Gudanar da bincike kan aikin Soja
·       Haka kuma kwamfuta makami ce mai matukar amfani da za a iya kare kai da ita.   

1.5.7 Sadarwa
Sadarwa yana nufin isar da sakowani tunanihoto ko maganar da aka samu da kuma wadda aka gan ta a fili wadda kuma take daidai da fahimtar mutum, ga wanda da shi ake nufi da ita (maganar)Wasu manyan yankuna a cikin wannan rukuni sun haɗa da:-
·       Aika sakon I-mel
·       Hira (ko wanzar da muhawara)
·       File Transfer Protocol FTP
·       Telnet
·       Bidiyo-conferencing

1.5.8 Aikace-Aikacen Kwamfuta A Harkar Gwamnati 
Kwamfuta ta taka muhimmiyar rawa a aikace-aikacen gwamnatiWasu manyan abubuwa daga cikin wannan rukunisu ne:-
·       Ƙasafin kuɗi
·       Sashen harajin tallace-tallace
·       Samun kuɗin shiga na sashen haraji
·       Walwamasu jefa ƙuri'a
·       Walwar matuƙa/tsarin lasisi
·       Ƙiyasin Yanayi
·       Ɗaukar ma’aikata
·       Sanin lokacin ritaya da sauran su.