5.1YADDA ZA AYI WANI BINCIKE A INJIN NEMA
Idan za a buɗe Google a matsayin abinda za a yi misali dashi, za azo kusa ga inda akarubuta Address sai rubuta www.google.com sai adanna (Go) ko a danna (Enter), bayan an danna shafin zai bude.
Sai arubuta abin da ake so yi bincike kansa a cikin wani  dogon layin da aka gani,duk abin da ake neman a kusanto da shi a nan ne za a rubuta. Bayan an rubuta abin daake nema sai adanna (Enter). Alal misali ana neman wani littafi mai magana kan shaye-shaye a yanar gizo, bayan an buɗeGoogle sai azo dogon layin nan a danna abin nan da ke yawo a cikin layin (click) sai rubuta sunan littafin da ake tunanin za a iya samunshi a yanar gizo kamar haka; “Kashedinku Mashaya” bayan an rubuta sai a dannan nema  akan (Google search), ko kumaa danna(Enter).Bayan an yi hakan sai aɗan jira binciko mana amsar abinda ake nema, idan ya nemu, za aga shafuka daban-daban, to, anan ne za ariƙa karanta kanun bayanan, idan an ga irin bayanin daake nema, sai a danna akan tushen labarin.