An kirkira kamfanin Microsoft a ranar 4th ga watan 4 a shekara alif 1975, kamfanin da Bill Gates da Paul Allen suka kafa. A halin yanzu kamfanin Microsoft yana daya daga cikin mafi shahara da kuma kamfanonin da suka yi nasara a fadin duniya. Haka kuma Kamfanin Microsoft shine wanda ya kirkiro Microsoft Windows, Microsoft Office, DirectX, XBOX da kuma wasu shirye-shirye na wassanni (games)