BABI NA BIYU
2.0 MUHIMMAN ABUBUWAN MASU ALAKA DA KWAMFUTA 
Kwamfuta tana iya amsa umurni ta cikakkiyar hanya, kuma ta aiwatar da umurnin da aka ba ta. Sannan kuma tana iya aiwatar da ayyuka bisa tsare-tsaren da aka shimfiɗa mata bai ɗaya.

2.1KWAMFUTOCIN ZAMANI
Kwamfutar zamani na amafani da wutar lantarki ko kuma wani batiri na musamman da kuma wani yare da ake amfani da shi wajan ba su umarni wato (software)Ɓangaren injin kwamfutar da ake kira (hardware) ya ƙunshi wayoyin lantarki, taransisto (transistors), ƙwaƙwalwa (processor) da sauran kayyayakin da za a iya maƙalawa a jikinta domin ta yi aiki.
ɓangaren tsari da kuma yaren da ake ba ta umarni ta wajen sarrafa kwamfuta shi ake kira da suna (software).
Dukkan kwamfuta tana ƙunshe ne da ɓangarorin (hardware) kamar haka: -
1.     
Ƙwaƙwalwa (Memory) ko (RAM) wurin tara bayanai.
A nan ne kwamfuta ke tara bayanai na wucin-gadi, umarni da ayyukan da aka ba ta ko kuma zata yi.
2.     
(Mass Storage) wurin ajiye bayanai na dindindin.
Shi ne wurin da ake ajiyar bayanai na dindindin har sai an nemi ta goge su.
3.     
(Input Devices) Na’urorin shigar da bayanai ko karɓar umarni
Ta waɗannan kafafe ne ake iya ba ta umurni ko a shigar da bayanai na abin da ake so. A takaice dai  allon rubutu (keyboard) da kuma linzamin kwamfuta wato (mouse) ko a ce kusu (Ɓera).
4.     
(Output Devices) Na’urorin da ake fitar da bayanai ko kuma umurnin da aka ba kwamfuta.
Ta waɗannan kafafe ne take fitar da bayanai ga mai sarrafata. A takaice dai shi ne abin kallo ko kuma a ce allon majigi (Monitor) ko kuma (Display Screen) da kuma lasifika wato (Speaker) ko injin daɓ’i (Printer) da sauransu.
5.     
(Central Processing Unit)
Wannan shi ne zuciyar kwamfuta wanda yake aiwatar da dukkanin ayyuka.
Wani ƙarin bayani game da waɗannan ɓangarori da muka lissafa shi ne; dukkaninsu suna haɗe ne da juna ta hanyar wayoyin da ake kira (BUS). Ta wannan hanyoyi ne bayanai suke tafiya daga wannan ɓangare zuwa wancan, har a cim ma aiwatar da abinda ake so a aiwatar na umarni.