DU’AUL MUSTAJABA - FALALAR AMBATON ALLAH MADAUKAKI DARASI NA 1
Allah tsarkakakken sarki kuma MadaukakiYa ce: “Ku tuna da Ni, Ni kuma zan tuna da ku, kuma ku yi godiya zuwa gare Ni, kuma kada ku butulce min”.
Don haka wannan ya nuna cewa duk wanda ya kasance yana tuna Allah a koda yaushe Allah zai tuna dashi zai taimaka masa, zai kuma kasance gatansa a duk inda ya sami kansa.
Kuma Allah Madaukaki Y ace: “Ya ku wadanda suka yi imani! ku ambaci Allah, amboto mai yawa. Kuma ku tsarkake Shi, a safiya da marece. Shi ne wanda ke tsarkake ku, da Mala’ikunsa kuma suna yi muku addua, domin Ya fitar da ku daga duhu zuwa haske. Kuma Ya kasance Mai jin kai ga muminai. Gaisuwarsu a ranar da suke haduwa da Shi ita ce “Aminci”, kuma Ya yi musu tattalin wani sakamako na karimci”.
Babu shakka Allah Ya yi kira ga wadanda suka yi imani da su tsarkake Allah ta hanyar ambatonsa cikin safiya da marece, tare da tabbacin zuwa garesu da cewar idan suka yi hakan shima Allah zai tsarkake su tare da mala’ikunsa da basa saba masa, zai kuma yi masu jagora ta hanyar dorasu a bisa hanya ma daidaiciya ya kuma kawar masu da duhun kafirci da zalunci. Kuma ya kasance mai tausayawa zuwa ga muminai. Bayan haduwar su a cikin rahamarSa zasu kasance suna yiwa juna barka da cewa “Salam/Aminci, Aminci” zasu kuma dauwama a cikin karimcin ubangijinsu.
Kuma Allah Madaukaki Ya ce: “Ka hakurtar da ranka tare da wadanda ke kiran ubangijinsu, safe da maraice, suna nufin yardarSa. Kuma kada idanunka su juya daga barinsu, kana nufin kawar rayuwar duniya. Kuma kada ka bi wanda Muka shagaltar da zuciyarsa daga ambatonMu, kuma ya bi son zuciyarsa, alhali kuwa al’amarinsa ya kasance yin barna”.
Allah ta’ala ya na bawa manzonsa hakuri tare da wadanda sukayi imani masu yawan ambaton Allah a cikin safiya da yamma, masu nufi da neman yardar Allah. Tare da fadakar musu cewa kada su juya zuwa ga barin nagartattun bayi idanuwansu su koma ga kawar duniya ko kwadayin duniyar wasu wadanda suka kasance masu yin barna.
Kuma Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma wanda ya bijire daga ambotoNa, to, hakika Rayuwa mai kunci ta tabbata a gareshi, kuma muna tayar das hi a ranar kiyama yan makaho”.
Allah Madaukakin Sarki Ya ce: “Kuma wanda ya makanta daga barin amboton Ubangiji mai rahama, to, za mu sabauta shaidan a gareshi, watau shi ne abokin sa.
Wadanda basa ambaton Allah zasu kasance cikin kunci da tashin hankali a ranar kiyama haka kuma anan cikin duniya shaidan ne zai zama aboki garesu.


Haka kuma Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Hakika Allah madaukaki yana cewa: “Ni ina tare da bawana matukar ya ambace Ni, kuma labbansa sun motsa saboda Ni”. Ahmad da Ibnu Majah da Hakim suka ruwaito shi (Hadisin Abu Hurairah R.A)
Kuma Manzon Allah ya ce: “Allah madaukaki yan cewa: “Ni ina inda bawana ya zace ni. Kuma ina tare dashi idan ya ambace Ni, idan ya ambace Ni a cikin ransa sai in ambace shi a zatina. kuma idan ya ambace  Ni a cikin taro, to, zan ambace shi a cikin taro mafi alhairi daga nasa. kuma idan ya kusanto gare ni da taki day azan kusanto gashi da zira’I guda; kuma idan ya kusanto zuwa gare ni da zira’I guda zan kusanto zuwa gare shi da gaba gudu; kuma idan ya zo mini yan mai tafiya, to, zan zo masa ina mai gaggawa”. Ahmad, Bukhari, Muslim, Tirmizi, Nisa’I da Ibnu Majah suka ruwaito shi (Hadisin Abu Huraira R.A).
Kuma Annabi  ya ce: “Mutane ba zasu zauna suna ambaton Allah madaukaki ba face mala’iku sun kewaye su, kuma rahama ta lullube su, kuma natsuwa ta sauka a garesu, kuma Allah madaukaki ya ambace su a wajen wadanda suke wajensa”. Ahmad, da Muslim suka ruwaito (Hadisin Abu Huraira R.A)
Kuman Manzon Allah Yace : “Lalle, Allah zai tashi wasu mutane ranar alkiyama alhali a cikin fuskarsu akwai haske, suna zauna a kan mimbarai na lu’ulu’u, mutane suna kwadayin halin da suke ciki, gasu kuwa ba annabawa ba ne ko shahidai”. Sai wani balarebe ya durkusa a kan gwiwoyinsa sai ya ce : Ya manzon Allah! siffanta mana su, don mu sansu”. Sai ya ce : “Su ne masu soyayya don Allah daga kabilu daban-daban da garuruwa daban-daban da suke taruwa a bisa ambatun Allah. Dabarani ne ya ruwaito kuma hadisi ne mai kyau daga (Abud-Darda’I R.A)

Kuma Annabi Ya ce: “Mafificin zikiri shine ‘La’ilaha Illallah’, kuma mafificiyar addu’a it ace Alhamdulillah”. Tirmizi, Nisa’I, Ibnu Maja, Ibnu Hibban da Hakim suka ruwaito shi (Hadisin Jabir R.A)

Annabi (S.A.W) ya ce: “Mutum da dai bai fadi ‘La’ilaha illallah ba yana mai tsarkake niyyarsa face an bude masa kokofin sama har sai an sadar da ita zuwa al’arshin Allah, muddin ya nisanci manyan zunubai”. Tirmizi ya ruwaito shi (Hadisin Abu Huraira R.A)
Kuma Annabi (S.A.W) ya ce: “Kewa yayin mutuwa a cikin kabari ko a lokacin tashi daga kabari ba za ta kasance bag a ma’abuta ‘Laila ha’illah’. Kamar cewa ni ina duba zuwa gare su yayin tsawar tashin kiyama suna karkade kawunansu, suna cewa :Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya tafiyar mana dab akin ciki’ Dabarani ya ruwaito (Hadisin Dan Umar R.A)
Annabi (S.A.W) ya ce :Yan aljanna ba za su ga hasara a kan wani abu ba, face a kan wani lokaci da ya wuce su lokacin da suke a duniya ba tare da sun ambaci Allah mabuwayi mai girma a cikinsa ba.” Dabarani dai Baihaki suka ruwaito (Hadisin Mu’azu R.A)
Annabin Allah (S.A.W) ya ce :Babu wani mutum da zai fadi La’ilaha illallah sau dari (100 times) face Allah madaukaki ya tashi shi ranar kiyama fuskarsa tana haske kamar wata daren sha biyar. kuma a wannan ranar ba za a daukaka aikin wani ba mafi falala daga aikinsa face wanda ya fadi misalign fadinsa ko ya kara akai”. Dabarani ya ruwaito shi (Hadisin Abud Darda’I R.A)
Kuma Annabi (S.A.W) yana cewa “La’ilaha illallah Wahdahu Lasharikalah Lahul Mulku walahul hamdu Wa huwa ala kulli shai’in kadari” 10x Ma’ana (Babu abin bautawa da gaskiya fa ce Allah, madaukaki, baida abokin tarayya a tare dashi, Mulki na sa ne, kuma godiya ta tabbata a gareshi kuma shi mai iko ne abisa kowane abu. Sau Goma. Ya kasance yana da kwatankwacin ladar yanta bayi hudu daga yayan Annabi Isma’il (A.S)”. Buhari da Muslim da Tirmizi da Nisa’I suka ruwaito shi (Hadisin Abu Ayyub (R.A)

ALSO REAL ADDU’A DAGA LITTAFIN DU’AUL MUSTAJABA - GABATARWA