ADDUO’I DAGA LITTAFIN DU’AUL MUSTAJABA
DAGA ALKUR’ANI DA HADISI
WALLAFAR AHMAD ABDULJAWAD
ACIKIN HARSHEN HAUSA

Wannan wani darasi ne da zamu rinka kawo ma masu bibiyar shafinmu na www.hausacity.com wanda ya shafi addu’o’i daga cikin littafai daban daban na mawallafa daban daban a cikin harshen hausa domin amfanin hausawa da kuma masu jin yaren hausa.

Da yardar Allah wannan shafi zai dukufa wajen kawo muku abubuwa masu amfani ga Rayuwa tare da kokarin karantarwa a fannin Rayuwa da kuma addinin musulunci, haka kuma wannan shafi duk abinda zai wallafa zai kasance a cikin harshen hausa ne insha Allahu.

Muna fatar zaku nuna mana soyayya ta hanyar cigaba da yada shafin mu zuwa ga abokai da yan uwa domin suma su amfana.


GABATARWAR MAWALLAFIN LITTAFIN
Godiya ta tabbata ga Allah, kuma aminci ya tabbata a bisa bayinSa wadanda ya zaba. kuma aminci ya tabbata a bisa fiyayyen Annabi da Allah Ya zaba, shugabanmu Muhammad (S.A.W) wanda daga ubangijinSa aka saukar masa da aya cewa, “Kuma idan bayiNa suka tambiyeka game da Ni, to, Lalle Ni makusanci ne. Ina amsa kiran mai kira idan ya kira Ni. Saboda haka su nemi karbawata. kuma suyi imani da Ni, tsammaninsu, su shiryu.” Sai Annabi (S.A.W) ya yiwa al’umarsa bushara da baiwar ubangijinsa Ya ce, “Ku kira Ni in karba muku”. kuma ya tsoratar da al’umarsa daga bijirewa ga barin yin addua. Ka ce, “Ubangijina ba ya kulaa kuu inba domin adu’arku ba.”
Bayan haka, lalle Allah Madaukaki Ya kimsa mini kuma Ya taimake ni akan na tarawa kaina da yan uwana wani abu na addu’oin da Allah Ya saukar a cikin littafinsa mabuwayi, da kuma addu’oin Manzonsa mai girma (S.A.W), da kuma sauran addu’oin da aka ruwaito a cikin littafin da na sa masa suna: “ADDU’A ABIN NEMAN AMSAWA – DAGA ALKUR’ANI DA HADISI”.
Hakika na jera addu’oin a bisa adadin kwanakin sati domin mutum ya tabbata yaa mai bayyana bukatarsa zuwa ga UbangijinSa. Sai ya roke Shi yana mai Kankan da kai da nuna tsoro bad a bayyanawa sosai ba: “Ko wane ne yake karbawa mai bukata idan ya roke shi?” Hakika, Allah ne!.

Also Read Falalar Ambaton Allah 

Kuma, kafin addu’ar, na gabatar da falalar ambaton Allah Madaukaki, da falalar wasu surorin Al’kur’ani, sannan falalar Salati ga Annabi (S.A.W); domin tsarkake zuciya da warkar da mutum daga cutarsa. kuma domin mai addu’a ya samu karfin karbar hasken da zai shiga zuciyarsa, kuma ya haskaka kirjinsa a dai dai wannan lokacin ne mai addu’a zai yi ji da saukar rahama a gare shi kamar farkon ruwan sama, ko kuma ya sunsuna mafi dadin turare da zai tashi a cikin bakinsa a lokacin addu’ar ko kuma ya rika rokon Allah a zuciyarsa lokacin adduar lokacin da harshensa ya sarke. farin ciki ya tabbata ga mutumin da Allah Ya yi masa umurni day a roke Shi, kuma Ya amsa masa.
Hakika na cirato hadisan daga littafi mai suna JAMI’US-SAGIR da kuma karinsa na Imam Suyudi; wanda ya isa matuka wajen fitar da hadisan ciki kuma ya kiyaye ta daga abin da wani mai kago hadisi ko makaryaci ya kadaita da shi (kamar yadda ya zo a cikin gabatarwar littafin Jami’us din).
Amma abin da na cirato daga littafin JAMI’UL KABIR na Imamu Suyudi da kuma wanda ake kira da KANZUL UMMALI, to, hakika na yi nuni a karshen hadisin domin bambance na farko da na biyu. Sa’an nan kuma na yi kokarin inganta littafin da kuma tantance shi tare da shugabanni: MAFUZ IBRAHIM FARAJ, DA ABDURRAHEEM JUM’AH SHAREEF, MUHAMMAD MAHDI MAHMUD ALI, DA SHA’ABAN ALI KHALIL ABDURRAHMAN; su kuma suna daga Malaman Jami’ar Azahar.
Kuma muna rokon Allah ubangijinmu Maigirma da Ya sanya wa littafina “DU’AUL MUSTAJABA”, karbuwa da amfani da albarka ga wanda zai karbe shi ya yi addu’a da shi. Kuma Ya sanya mu daga wadanda Ya yarda dasu a wajen fadi da aiki. Lallai shi ne managarci Mai jin Kai.
Mai kaunar Rahamar Ubangijinsa, Mai yawan kyauta.
Ahmad AbdulJawad  

Also Read Falalar Ambaton Allah