Dan wasan kwallon kafa Olivier Giroud ya sa hannu ga sabon kwantaragi na shekara daya da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea. Dan wasan ya bayyana hakan ne a shafin sadarwar kungiyar inda ya ce "Ina matukar farin cikin sanya hannu a wannan sabon kwantaragin nawa." Ina matukar sha'awar na sake ko da shekara daya ne a nan, ina son kungiyar tun a da can baya, ina kuma fatan zamu kara lashe wasu kofuna a nan gaba." Daraktan Chelsea Marina Granovskaia ya kara da cewa "Mun ji dadin gani cewa Olivier dan wasan Chelsea ne a wasa mai zuwa. Tun da ya zo kungiyar wasan kwallon kafa ta Chelsea wata 18 da suka wuce, wani lokacin yana yin hakuri ya jira a bashi dama amma ya taimaka wa kungiyar sosai. Muna fatar shi lashe kofin sa na biyu a Chelsea a wasan sa Europa da zamu buga a Baku domin ya kara a kan kofin FA din da ya ci a shekarar da ta gabata".

ALSO READ: Shin ko kun san yadda bacci ke daukar mutum?