3.3 SOFTUWAYAN KWAMFUTA     
Kwamfuta ba ta aiki idan ba softuwaya cikinta. Idan aka ce Softuwaya ana nufin tarin wasu bayanai da ake sakawa a cikin kwamfuta ana sarrafa ta da dasu, ko kuma shiri ko shirye-shiryen da ke ba da umurni ga kwamfuta don sanar da ita aikin da zata yi da kuma yadda za ta yi aikin. 
Softuwayan da muke da su suma sun kasu gida biyu kamar haka:-
·         (System software)
·         (Application software)
3.3.0 (System Software): - Shi dai (system software) ana kiran shi da suna (operating system) (OS), a zahirance yana tafiya ne tare da kwamfuta. Ma’ana, duk lokacin da ka sayi sabuwar kwamfuta za a tarar da (OS(operating system) a ciki. Kuma wannan softuwaya na (OS) shi ke kula da duk wani aiki na kwamfuta da kayayyakin da kwamfuta take ɗauke da su. Mai karatu ya sani cewa, kowace kwamfuta tana aiki da (system software) sannan kuma idan har babu (OSshi kanshi (application software) ba zai yi amfani ba.
(OSɗin da ya fi sauƙin in misaltawa mai karatu da shi  shi ne (Windows Operating System) da za a iya samun shi a kowace kwamfutar tafi-da-gidanka (Personal Computer), ita kuma kwamfutar (Mac) tana amfani da (Mac Operating System).
3.3.1 (Application Software):Waɗansu tarin bayanai ne da zasu ba mai amfani da kwamfuta damar gudanar da wani takamaiman aiki da su ga kwamfuta. Akwai (application softwaremabambanta waɗanda zamu iya gudanar da takamaiman ayyukanmu da su, kamar misalin waɗannan da suke mafi shahara da za a zayyanawa mai karatu, tare da bambance-bambancen ayyukan su kamar haka: - 
  •  (Internet Application):- (Internet Explorer) ce tsarin dake ba da damar haɗuwa da yanar gizo, sannan a iya bincikar wani adireshi na yanar gizo, ko shafin yanar gizo kamar www.sharhamak.com ko www.hausacc.com 
  • (E-mail Application):- (Outlook Express) na ɗaya daga cikin tsarin dake ba mai amfani da shi damar aikawa da karɓar sakon I-mel. 
  • (Word Processing Application)(Microsoftword) shiri ne dake ba mai amfani da shi damar rubuta wasiƙar da zai iya turawa zuwa i-mel ko wani shafi na yanar gizo. Ana kuma iya ɗab’in abin da aka rubuta kai tsaye, ana kuma iya gudanar da duk wani abu da ya shafi harkar rubuce-rubuce a cikin shi idan yana cikin kwamfuta. 
  •  (Spreadsheet Application): - Za a iya cewa (Microsoft Excel), ita ce misalin wannan (application). Tsarin (Microsoft Excel) na ba mai amfani da ita dama wajen yin lissafi.

3.3.2 ABIN KIYAYEWA: Wannan na da muhimmanci ƙasan cewa idan ka sayi sabuwar kwamfuta, tana zuwa da (Operating System) da kuma wasu daga cikin (application Softwareda za a iya samu a cikinta. Dole ne ka sayi wasu ƙari n (application software) ka sanya a cikin kwamfutarka. Sanyawa ko shigarwa na nufin shigar dasu a cikin hard disk din kwamfutarka mai yuwa ne ka yi amfani da su nan zuwa gaba. Kuma duk wani kayan aikin da kwamfuta ke buƙata ya kamata a kula da su sosai.