BABI NA BIYAR
YANAR GIZO (INTERNET)
A takaice yanar gizo (internet), an kirkire ta ne da manufar cigaba ga kimiyyar kwamfuta ta hanyar hada dukkanin mahada ta ilimi.
Kamar yadda mukasan internet a yau, farkon kirkiro ta dai ya ta’allaka ne tun shekarar 1960’s da suka shude kuma an fara karbar sakon farko a ranar Juma’a 29/10/1969. A shekarar 1993, kimiyyar (internet) ta zama shahararriya ta kuma kara bunkasa wanda yake a halin yanzu ake ta samun karin cigaba. Sannan kuma mutane na amfani da ita a dukkan sassa na fadin duniya.

Yanar gizo ta kunshi biliyoyin shafuka wadanda mutane suka kirkira da kuma kamfanoni daga sassa na duniya, ta zama matattarar bayanai da kuma nishadantarwa da ilmantarwa ga al’uma. Haka kuma internet nada dubban hanyoyi da ke taimakawa rayuwa ta zama cikakkiya. Misali; da yawan. Alal misali, mutane da yawa na amfana da cibiyoyin bayar da kudi na taimakawa ga sha’anin (online banking) wanda zai bada damar mai amfani dashi da ya kula, ko duba asusun ajiyarshi a (online).