MAKAMAR IBADA 
NA BILYAMINU YAHAYA AMBURSA


 
TSALKI
Minene tsalki?
Tsalki shine tsafta tareda tsalkakuwa daga najasa.
Da farko dai tsalki wajibine yazo a al’Qur’ani da  kuma sunnar manzon Allah (S A W) Allah madaukakin sarki yace “idan kuka kasance da janaba to kuyi tsalki  kuma Allah madaukakin sarki  yace kuma tufafinku ku tsalkakesu kuma Allah madaukakin sarki yace lallai Allah yana son masu tuba kuma yana son masu tsalki.
Ba shakka wadannan ayoyi sun nuna mana wajabcin yin tsalki .
Haka ma hadisai suma sun nuna mana wajabcin yin tsalki manzon Allah  tsirra da amincin Allah su tabbata agareshi yace “mabudin sallah shine tsalki ‘’
A wani hadisi manzon Allah tsira da amincin Allah sutabbata agareshi yana cewa “ba’a karbar sallah batare da tsalki ba ‘’
Kuma manzon Allah yana cewa na wani hadisi tsalki yankine daga cikin imani ko kuma tsalki rabin imani ne’’ haka ma wadannan hadisai sun nuna mana wajabcin yin tsalki .


KASHE- KASHEN TSALKI

Tsalki ya kasu kashi  biyu
1.    Tsalki na badini 
2.    Tsalki na zahiri
Tsalki na badini :- shine tsalkin da a boye , wato tsalkake rai  daga zunubi da kuma sabo tare da tuba ta gaskiya daga dukkan zunubai da sabo da kuama tsalkake zuciya daga shirka da hasada da girman kai da riya da dai rausansu.
Tsalki na zahiri :- shine tsalkin da a bayyane , wato wato tsalkin hadasi da kuma tsalkin habasi.
      1. tsalkin hadasi :- shine alwala da wanka da taimama
    2. tsalkin habasi :- shine gusarda najasa da ruwa masu tsalki na daga kufar mai sallah na daga jikin sa ko gurin sallarsa.

RUWA NA KASANCEWA DAGA ABU BIYU

1.    Ruwa sakakku :- sune ruwan da basu garwaya da komai ba wadanda ake rarrabawa ga rinjaya. Shin ruwan masu janasa ne ko masu tsalkine .rijiyane ko ruwan marmaro ko kuma ruwa masu gishiri.
Saboda zancen Allah madaukakin sarki “ kuma mun saukarda ruwa daga sama masu tsalki .
Haka ma hadisan manzon Allah ya nuna haka a inda manzon Allah tsira da aminci amincin Alllah su tabbata a gareshi yace ruwa masu tsalki ne sai idan kanshinsu ya canza ko kuma dandanon su
2.    Wuri mai tsalki:- shine ban kasa mai tsalki na turda ko yashi ko dutsi ko bakar kasa  manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yace  abin sani an sanya mini kasa ta kasance masallaci’’
Kuma wuri yana kasan cewa mai tsalki saboda rashin ruwa ko kuma kasa. Allah madaukakin sarki yana cewa “ idan baku  samu ruwa ba, ku ,mufi tuskar kasa mai kyau”

NAJASA
Minene Najasa?
NAJASA:- shine abinda yake fita daga farjin dan adam na daga kashi, ko hitsani ko maziyi ka wadiyi ko maniyi hakanan kashin dukkanin dabbar da baa halatta cin naman taba, ko kuma amai wanda ya canza hakanan nau’u kan matattu amma banda fata wadda aka jeme, saboda fatan da aka jeme mai tsalki ce. Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yace “ duk fatar da aka jeme hakika ta tsalkaka”
LADUBBAN BIYAN BUKATA
 Yana daga laduban biya bukata
1.    Ya samu wuri taka mame daga mutane amma wanda ya nisanta daga ganin mutane.
2.    Kada ya shiga abinda keda ambaton Allah
3.    Gabatar da fatar hagu gunshiga makewayi
4.    Kada ya dauke wandan shi har sai yayi kusa da kasa
5.    Kada ya fuskanci  alkibla
6.    Kada ya juya wa alkibla baya.
7.    Kada ya biya bukatarsa a aikin inuwa.
8.    Kada ya biya bukatarsa a samun hanya
9.    Kada yayi tsalki da kasha a wani hadisi manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yace, “kada kuyi tsalki da kasha domin guzurin yan uwan kunw daga aljannu”
10. Kada ya shafa zakarinsa da hannunsa na dama alhahi yana fitsari

ALWALA
Alwala a al’Qura’ani da kuma hadisin manzon Allah. Allah madaukakin sarki yace” yaku wandanda suka bada gaskiya ida zakuyi sallah ku wanke fuskokin da hannuwanku zuwa ga mirafikai ku shata kanaku da kafafunka zuwa ga idon sahu”
          A wani hadisi manzon Allah yana cewa “babu sallah ga wanda bayyi alwalaba.”

                                      FALALAR ALWALA
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yace “ dan bawa muslumi ko mumini yayi alwala ya wanke fuskarsa za’a kan kare mashi abinda ya kalla na daga zunubi. Idan kuma ya wanke hannunsa za’a kankare mashi abin daya taba na daga zunubi.

                                               
                                                FARILLAN ALWALA
Farillan alwala guda bakwai ne gasu kamar haka.
1.    Niyya
2.    Wankin fuska
3.   Wanki zira’i
4.    Shafan kai
5.    Wankin kafafu zuwa ga idan saha
6.    Cudanayawa
7.    Gaggautawa

SUNNONIN ALWALA
1.    Yin bismalla
Manzon Allah yana cewa “babu alwala ga wanda bai ambaci sunan Alwala ba”
2.    Wanke takunan hannu sau uku
3.    Yin aswaki
Manzon Allah yana cewa “badon kada intsanan tawa al’umma ta ba da na umurcesu dayin aswaki ga koi wace alwala.
4.    Kurkurar baki:- shine motsarda ruwa a cikin baki.
5.    Shaka ruwa da shacewa.
Shaka ruwa :- Shien jan ruwa da ga hanci
Shacewa:- Shine fitarda ruwa daga hanci
6.    Tsatsatsafe gemanya
7.    Ukkunta wanki
8.    Tsatssafe yatsun hannu da kafuwa
9.    Damantawa
10.                       Shafanka

ABUBUWAN DA AK KARHANTA
1.    Makaruhine alwala a wurin najasa
2.    Kari akan wanki uku
3.    Barnar ruwa
4.    Bari sunna daga sunnonin alwala
5.    Alwala da kingin mace

YADDA AKE ALWALAA AIKACE

          Da farko dai zai aje abin alwalan shi a geton damansa. Kuma alwalan shi a geton damansa kuma yace “Bismillahi” ya zubo ruwa akan tafinsa yana mai niyar yin alwala ya wankesu sai uku (3) ya kurkure baki sau uku(3) shaka ruwa da sha cewa sau uku(3) wankin fuska tundaga matsirar gashi tun daga gashi na atada zuwa karshen geman yada kuma kunne zuwa kunne sau uku(3) a wanke hannun dama dana hagu sau uku(3)  zuwa mirafikai sannan shafar kunne cikinsa da wajensa sai wankin kafata dama da ta hagu sau uku(30) zuwa ga idon sahu. sai kayi addu’a wadda ta dace da sunnar manzon Allah (S.A.W) gata kamar haka;Ashhadu allailahaillallahu wa ashhadu anna muhammadarrasulullah Allahumma ijalni minattawwabina wa ijalni minal –mutadahhirina.

                             ABUBUWAN DAKE WALWALE ALWALA
1.    Ridda
2.    Cin nama rakumi
3.    Kwana mai nuyi
4.    Shafa zakari da cikin takun hannuwa
5.    Shafa macce da sha’awa.dadaisauransu

WANKA
Minene Wanka?
Anka shine game jiki da ruwa.
Ba shakka wanka yazo acikin al’Qurani da kuma sunnar mazon Allah tsira da amincin Allah sutabbata a gareshi. Allah madaukakin sarki yace “kuma haka idan kuma masu janaba, face mai ketare hanya har kuyi wanka mazon Allah tsira da amincin  Allah su tabbata a gareshiyace “idan kaciya biyu suka hadu hakikata wanka ya wajaba”.

                             WAJIBBAN WANKA
1.    Janaba
2.    Katsewar jinin haila ko na biki saboda fadar Allah madaukaki sarki “saboda haka ku nisanci mata a cikin wurin haila, kuma kada ku kasan ce dasu sai sun yi tsarki to idan sunyi wanka sai kuje musu daga inda Allah ya Umurce ku
3.    Shiga musulunci
4.    Mutuwa
Bayan haka kuma anso kayi wanka kamar haka:-
1.    Jumma’a:manzon Allah yce:idan jumua tazowa dayanku yayi wanka.
2.    Ihrami
3.    Na shiga makka da tsayuwar arfa dadai sauransu.

FARILLAN WANKA
1.    Niyya
2.    Game saurin jiki da ruwa
3.    Tsatsafe yatsu da gashi


`                           SUNNONIN WANKA
1.    Yin bismillah
2.    Wanke takunnan hannaye kafin a shigar dasu a cikin ruwa
3.    Farawa da gusarda kazanta
4.    Gabatar da gabban alwala
5.    Kuskurar baki da shaka ruwa

ABUBUWAN DA AKA KI

1.    Fara wanke wurin da keda kazanta
2.    Barnar ruwa
3.    Wanka batareda shamakiba
4.     
TAIMAMA

Minene taimama?
Taimama shine tsalkin turda wanda ya shafi shafar fuska da hannaye.
  Bashakka taimama tazo a Alkurani mai girma Allah madaukakin sarki yace “kuma iankuka kasance majinyata,kokuwa akan tafiya ko kuwa wani daga cikinku idan yazo da ga qayadi, ko kuwa kun shafi mata baku sam ruwaba to, ku nufi fuakar kasa mai kyau, ku yi shafa ga fuskokinku da hannuwanku” wato kuyi taimama saboda rashin ruwa.
                  

                             FARILLAN TAIMAMA
1.    Niyya
2.    Wuri mai tsalki
3.    Bugu na farko
4.    Shafar fuska da takunan hannu

SUNNONIN TAIMAMA
1.    Yin bismillah
2.    Bugun kasa na biyu
3.    Shafar zira’i

ABINDA KE WALWALE TAIMAMA
Dukkan abinda ke walwale alwala shike walalwale taimama.
                            
                             YADDA AKE YIN TAIMAMA ATAKAICE
Da farko zakace “Bismillahi” kana mai niyya, sa’nnan ka buga takunan hannayanka akan kasa ko yashi ko dutsi ko bakar Kasa damaka mantansu. Balaifi ka kakkabe kurar dake takunan hannunka kakkaba sassauka, sa’an nankashafa fuskarka shafa daya sai ka sake buga kasa ga takunanka ka shafa hannunka.

                             HAILA DA JININ BIKI
Mata masu haila sunkasu kash uku gasu kamar haka;-
1.    Wadda ta fara
2.    Waddata saba
3.    Mai ciki
Ø Mafi yawan haila ga wadda ta fara shine kwana goma shabiyar(15)
Ø Wadda ta saba kuwa idan jinin ya cigaba dazowa zata kara kwana ukku(3) matukar bata ketare kwana goma sha biyarba (15)
Ø Ita kuwa mai ciki bayan wata uku sai tayi kwana biyu ko makamanci haka bayan wata shidda kuwa zata yi kwana ashirin ko makamancin haka.
Shi kuwa jinin biki kamar hailace acikin hanuwarsa. Mafi yawa kwana sittin, idan ya katse ko da ranar da aka haihu tayi wanka tayi sallah.
                  
                             ABINDA AKA HANA GA HAILADA JININ BIKI
1.    Taki/saduwa
fadan Allah maudakakin sarkin “kuma kada kukusancesu harsai sunyi tsalki”.
2.    Sallah da azumi.
sai dai shi azumi ana ranka shine bayan anyi tsalki.
3.    Shiga masallaci
4.    Karatun al’Qurani
5.    Saki

ABINDA AKA HALATTA GA MAI HAILA KO JININ BIKI
1.    Ambaton Allah
2.    Harama da tsayuwar arfa da sauran ayukka banda dawafi.
3.    Zozayya ga abinda bai kai farjiba
Manzon Allah yace “ku aikata ko mai amma ban da saduwa”.

                   SALLAH
Allah madaudakakin sarki yace” ku tsayarda sallah.Lallai  sallah ta kasance ga muminna farilla abin kayyadama lokaci”
Kuma manzon Allah yasan yata ta biyu acikin shika shikan musulunci guda biyar.






                   HIKIMAR YIN SALLAH
Hikimar yin sallah kuwa fadar Allah madaukakin sarki “ku tsayar da sallah.Lallai sallah tana hani daga al fasha da abin ki.

                   FALALAR YIN SALLAH
Ba shakka sallah tanada falala daga ciki:

1.    An tambayi manzon Allah, wane aiki yafi? Sai yace sallah acikin lokacinta
2.    Manzon Allah yace “tsakanin mutum da tsakanin ka firci shine barin sallah
3.    Manzon Allah yace “kan alamari  shine musulunci ginshikinsa shine sallah

SALLALOLIN DA AKA FARLANTA
Sallolin da aka farlanta guda biyar ne kamar haka:-
1.    Azzuhur
2.    La’asar
3.    Magariba
4.    Ishai
5.    Asuba

SALLOLIN DA AKA SUNNANTA
1.    Sallar idi biyu da ta alfijir
2.    Sallar shafewar rana kowata
3.    Sallar rokon ruwa
4.    Da wuturi
Wadannan sune sunnoni masu karfi.

                   SHARUDDAN WAJABCIN SLLAH
1.    Muslumi
2.    Mai hankali
3.    Baligi
4.    Shigar lokaci
5.    Yankewai jinin haila ko na biki
SHARUDDAN WAJABCIN SALLAH
1-musulmi
2-mai hankali
3-baligi
4-shigar lokaci
5-yankewar jinin haila

SHARUDDAN INGANCIN SALLAH
1.    Tsalki
2.    Suturtarda alaura.
3.    Fuskantar al kibla.



FARILLAN SALLAH

1.    Tsayuwa a salla ta farillah
2.    Niyya
3.    Kabbarar harama
4.    Karatun fatiha
5.    Rukui
6.    Dauka kowa da rukui
7.    Sujuda
8.    Daukakowa da sujuda
9.    Natsuwa acikin rukui da sujuda
10.                       Sallama
11.                       Zama domin sallama
12.                       Jerantawa tsakanin rukunnai

SUNNONIN SALLAH
1.    Kararun sura
2.    Cewa “sami Allahu liman hamidah”
3.    Cewa “subhana rabbiyal azim”
4.    Kabbara, ciratowa daga tsayuwa zuwa sujuda.
5.    Tahiya tafarko da ta biyu
6.    tahiya
7.    Bayyanawa a wurin da ake bayyanawa
8.    Asirtawa a wurin da ake asiritawa
9.    Salatin Annabi Muhammad [SAW].
Daga karshe ina mai kira garemu da mu kasance masu tsayar da salla. Manzon Allah yana cewa” farkon abinda za’a yiwa bawa hisabi a ranar kiyama shine sallah idan tayi kyau hakika sauran ayuka za suyi kyau.


KAMMALAW












GODIYA
dukkan godiya da yabo sun tabbata ga Allah madaukakin sarkin , mai kowa mai komai , mahaliccin abinda ke sama da kasa, abin da yaso shiyake kasancewa , abinda bai soba bazai taba kasan cewa ba .
Tsira da aminci su tabbata ga shugaban halitta Annabi Muhammad (S A W) da alayansa, da sahabbansa, da dukkan masu koyi da  dabi har zuwa ranar karshe.