7.2 TAYAYA ZA A GANE KWAMFUTA TA KAMU DA ƘWAYAR CUTA
Za a ga wani akwati ya fitoidan da F-Secure ake amfani akwatin na cewa an samu ƙwayar cuta. Haka kuma halayen PC za su nuna idan kwamfuta ta kamu da ƙwayar cuta.
 A dubi waɗannan alamu kamar haka:
ü Linzamin kwamfuta zai din ga motsi da kanshi ba tare da an taba shi ba.
ü Kwamfuta za ta dinga buɗewa ta na rufewa da kanta.
ü (Applications) za su gaza ko suƙi buɗewa ko su dinga budewa da kansu ba tare da an buɗesu ba.
ü Idan da F-Secure a ke amfani F-Secure icon zai ɓata daga abin dannawa na dama ga abin kallo. (DisplayScreen)
ü Ƙunshin yanar gizo (internet browser) za ta dinga buɗewa da kanta ba tare da an buɗe ta ba.
ü Kwamfuta za ta dinga nuna cewa ba ta da isasshen filin (low disk space) ko (low virtual memory).

ü Outlook zai dai na budewa