2.2 BAMBANCE-BAMBANCEN KWAMFUTA TA GIRMA DA ƘARFI KO SAURIN AIWATAR DA UMURNI
Akasarin kwamfutoci ana bambanta su ne ta ɓangaren girmansu ko ƙarfi ko kuma saurin aiwatar da umarni.
LAMBA
|
KWAMFUTA
|
BAMBANCI
|
1.
|
Akasarin irin waɗannan kwamfutocin ƙanana ne wadda mutum zai iya mallaka kuma ya yi amfani da ita a ko wane wuri. Tana da ƙarfi daidai gwargwadon yin lissafelissafe da wasu ayyukan da za a ba ta umurni da su. Tana zuwa ne da allon rubutu (keyboard), majigi ko a ce abin kallo wato (Monitor) ko (Display Unit) na nuna bayanai, da kuma ƙwaƙwalwa wato (Memory) na tara bayanai.
| |
2.
|
Ita ce kwamfuta ma fi ƙarfi ta aiwatar da ayyuka wacce mutum ɗaya zai iya amfani da ita. Tana yanayi ko kama da kwamfutar tafi-da-gidanka. Amma abubuwan da ta ƙunsa kamar ƙwaƙwalwa sun bambanta. Tana da ƙarfin gaske da sauri wajen aiwatar da ayyuka. Kuma majiginta ya fi na kwamfutar tafi-da-gidanka fitar da hotuna.
| |
3.
|
Kwamfuta ce da mutane a ƙalla goma (10) zuwa wasu ɗaruruwa zasu iya amfani da ita a lokaci guda.
| |
4.
|
Ita ce kwamfuta ma fi ƙarfi wadda mutane fiye da dubbai zasu iya amfani da ita a lokaci guda.
| |
5.
|
Ita wanna kwamfuta bayan fin kowacce kwamfuta ƙarfi, tana kuma iya sarrafa kanta.
|
0 Comments
Post a Comment