1. Dubi status na anti – virus software kuma a tabbatar wannan anti virus an yi (up-to-date) din shi kuma ya na tafiya daidai.
2. Ka da a kyale idan an ga jan kunne na shigowar kwayar cuta (virus)
Idan an kyale jan kunne (warning) na shigowar virus ba a cikin hatsari kaɗai kwamfuta za ta tsaya ba, sai dai matsalar za ta shafi dukkanin kwamfutucin da ke wurin. Don haka a ɗauki mataki cikin lokaci.
3. Ka da a buɗe kowane irin sako na i-mel da a ka yi (attachments) idan har ba a san me ya ƙunsa ba ko ba a san asalin inda ya fito ba.
4. Ka da a sanya wani ƙunshi (software) wanda ba a da tabbacin inda ya fito ko ba a san daga wane shafi ya fito ba.
7.4 SHAWARA GA MASU AMFANI DA KWAMFUTA
A kalla a sadar da ita ga kafar sadarwa ta yanar gizo (network) sau ɗaya a wata, imma a gida ko a makaranta don a sabunta rigakafin kwayoyin cuta (anti-virus) a cigaba da zama cikin tsaro.
0 Comments
Post a Comment