MUHIMMANCIN SANA’AR HANNU

Bashakka ita sana’ar hannu ba karamar muhimmiyar sana’a ba ce musamman ga al’umma, domin kuwa tana iya zamowa:
   1.    Sanadiyyar wadata
   2.    Samun yanci ga kai da kuma kasa baki daya
   3.    Walwala
   4.    Hana ta’addanci irinsu sata da yaudara
   5.    Hana zaman banza
   6.    Bunkasa tattalin arzikin kasa da sauran su.
Babban misali idan munyi la’akari ko nazari akan wannan baton zamu ga dukkan manyan kasashen duniya irinsu Ingila da amurika, uwa uba Chana da Jamus da Rasha kai har ma da Indiya, yau an wayi gari kayansu a kasuwar duniya su ne abin tu’ammali. A kan haka, sai ya zamo abin kuri da alfahari zuwa ga kasashen da ke tasowa musamman kasashen Afirika. Don haka a ganina ba wata kasa wacce za’a ce ta ci gaba face sai tana dogaro ga kanta.
Dogaro ga kai kuwa ya samu asali ne gun fasaha, fasaha kuma ta samo asali ne ga tunane tare da aiki da hannu ga albarkatun da Allah Ya shimfida a doron Kasa. Wannan shi ne ya samu tushe masana ke ce masa sana’ar hannu.
Ita sana’a abace wacce ke iya zama kariyar mutunci musamman a gare mu matasa.
Idan muka yi la’akari da sana’a a bangaren mata zamu ga a wani bangaren takan iya kara ma mata girma da daraja a wajen mazajensu, domin idan mace na da sana’ar yi, wani abin ba sai ta jira an yi mata ba, kuma tun daga nata bangaren izuwa ‘ya’yanta, takan dan rage wasu lalurori, kenan ko a nan sana’ar ta yi amfani, wannan matar da ke da aure kenan.
Sana’ar ba ga matan aure kawai take da amfani ba, tana da amfani  ainun ga yan mata musamman na yanzu.
A nan ya kamata yan mata su tsaya su kama sana’a. wannan shine dogaro ga kai, saboda matsalolin day an matanmu ke fuskanta a wannan lokaci, wanda idan ga sana’a, insha Allahu zata zama wata kariya a rayuwarmu.
A nawa tunani, yana da kyau iyaye su rika sanya yayansu a bisa hanyoyin koyon sana’a yafi a wayi gari a iske yara matasa kullum sai gara-ramba basa wannan inuwa basa waccan idan mace ce kuma bata wancan gidan, bata wannan gidan sai yawace yawace zuwa gidajen makwafta.
Sana’a zan iya cewa ya danganci yadda  
Idan muka dawo a dukkan bangarorin biyu na matasa maza da mata a halin yanzu sana’a ta zama wajibi ga dukkan matashi ko matashiya, ni a nawa tunani Sana’a kamar karatu ce idan matashi