SANADIYYAH 
“Amina ga wannan wani ne y ace na kawo maki” yaro ne da aka bawa sako ya bawa amina ke fadan hakan.
Amina ke cewa, “wa kuma ya baka sako zuwa gareni?” yaron ya ce, nima bansan shiba” amina ta tasu daga zaune zuwa mikewa a tsaye tazo dai-dai a yaron ta karbi wasikar bayan ta karba kuma take cewa, “ ka ce bakasan ko wa ya baka wannan ba? Ko wasa kake yi ne? don nasan ka da son wasa” yaron y ace, “wallahi ni ban san ko wayeba kawai ya ganni ne ya kira ni ya bani yace in kawo maki” “amina tace ba komai nagode” yaron ya juya ya fita, amina kuma ta koma ta zauna akan wata zankaleliyar kujera wacce ta ke acikin falon gidan, ta kuma dura dayan kafar kan daya, sannan ta bude takardar da yaron ya kawo ma ta, tana mai fara karatun takardar kamar haka:
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah subhanahu wa ta’ala tsira da aminci su tabbata ga annabi muhamad (S.A.W) wanda shine fiyayyen halitta. Aminci a gareki ba shakka nasan zakiyi mamakin wannan sako nawa abisa ganinsa ba tsammani da kuma rashin sanin ko waya aiko da sakon, to amma wannan bai zamu abu mai mamakiba idan har kika kasance mai hakuri bashakka hausa wa hance komai nisan jifa kasa ne makomarsa ba shakka wannan wasikar tawa ba wani abu mai bammamaki a ciki saidai kawai abin da ke iya kasancewa ne a rayuwa.
          Bashakka kece abarkauna a gareni kuma kece wannan na fada a cikin gurbin soyayyar ta badare da na daba sanin matsayintaba, abu ne mai matikar Al’ajabi. Sonki shine ya zamu jagoran zuciyata, dare da rana kece abin tinanina Amina ina mai sanr da ce wa sonki bazai taba fita a zuciya ba, fatana ki amintada soyayyata, ki kuma kasance wacce zata sharan kukana, shakkababu kaunarki ta zamu abun ban al’ajabi da kuma bammamaki ina fatan ki kasance da ni a kowane lokaci. Amina ina mai yi maki fatan alkhairi ki huta lafiya.
Daga mai kaunarki
Lallai wannan wasikar ta matikar kwance mata kai dumin rasa sanin mai wannan sakon/wasikar, duk da yake wannan sam bai tsorata taba kuma kadan da ga cikin razanar da taji a jikin ta. Bayan kwana biyu amina ta shiga Makaranta, da ya ke amina ‘yace mai kamun kai kuma mai tinani da sanin ya kamata, amina sam ba ruwanta da idan ta shiga makaranta ba ta kula da wadansu mashiriritan dalibamba, hakan ma yasa amina ko abokai bada kulawa ma’ana wadansu mashiriritan abukai sam bata kula su, abunda ya kaita shine ta ke yi.
Amina ‘yace wacce ta samu tarbiya tun agurin iyayen ta, amina ‘yar alhaji idris wanda ya shahara a bangaren kasuwanci bashakka alhaji Idris mutun ne mai tausayi da kuma taimakawa talakawa...