Wadannan wasu shafuka ne guda takwas 8 sanannu da ke wallafa littafan hausa wadanda muka zakulu muku domin cigaba da kayatar da ku, ku kasance da shafin mu na www.hausacity.com domin ilmantar da ku da kuma kayatar da ku. 

1. Aisha Ummi:Yarinya ce wacce ke sha'awar karatu da rubuce-rubuce kuma ta yi wasu daga cikin rubuce-rubuce da take sha'awar bada gudummawar ta a cikin harshen hausa inda ta rubuta littafin MIJINA SIRRI NA a cikin shafin ta mai suna http://aishaummi.blogspot.com/  

2. Zahra Muhammad Mahmoud: Ita ce marubuciyar CIN AMANA KO FANSA, Zahra yar Kaduna south , Kaduna state , da ke tarayyar Nigeria ita ma dai ta yi kokarin bada gudummawarta ga cigaban harshen hausa inda ta wallafa shafin ta na blog domin kawai ta nishadantar da masoyanta. 


3. Jedda Aliyu: Yarinya ce wacce ke sha'awar rubuce-rubucen hausa tare da karance-karence haka kuma ta rubuta wani littafi na SOYAYYA mai suna SONKI NE SANADI a shafin ta na blog mai suna http://jeeddahaleeyu.blogspot.com/


4. Gidan Novels: Shafin gidan Novels shafi ne da Abba Muhammad Gana ya samar domin masoya littafan hausa a kyauta wanda yake samo littafan hausa daga marubuta daban-daban a cikin shafin nasa. Za ku iya samun littafan da yake sakawa a shafinsa ta wannan adireshi kamar haka: https://gidannovels.guidetricks.com/

5. Bilkisu Dan Jumma: Wacce akafi sani da Billy Tabaco yarinya ce da ke sha'awar karatu da kuma rubuce-rubucen littafan hausa, haka kuma ta bada gudummawarta ga cigaban harshen hausa inda ta yi rubuce-rubuce a shafinta na blog mai suna http://billytabaco.blogspot.com/ 


6. Mrs Umar: Mawallafiyar shafin https://mrsumaru.blogspot.com/ inda take baje hajarta a shafin na rubuce-rubucen da take kuma itace ta wallafa littafin MAZA DA MULKI, MATA DA TAKAMA. 


7. Hausa City: Shafi ne da ke rubuce-rubucensa a cikin harshen hausa wanda mawallafin shafi marubuci ne wanda ya wallafa littafai da dama ya kuma saka a shafukansa na yanar gizo kamar su www.hausacci.ga, gidanmarubuta.blogspot.com da kuma www.craspost.xyz  haka kuma a cikin shafin ya wallafa littafin MABUDIN WAHALA, HUBBUL YAKIN na Asiya Sadiq Maccido da sauran littafai daban-daban.


8. Lafazin So: Shafi ne da ya shahara wajen wallafaka rubutattun wakokin soyayya tare da littafan hausa wanda yana da littafai da dama da aka wallafa a cikinsa da masu karatu zasu mora a ciki. Zaku iya ziyartar shafin ta wannan adireshi mai zuwa