,
Zidane kd.
TASKAR AJALI!!!
littafi na daya 1 part B.. end
,
dole nayi post kadan, coz banida lpy ne.
,
cigaba.......
mallaketa.Bisa wannan dalili ne
boka Salmara yasa
aljanu suka kwashe gaba dayan
dukiyarsa suka kaita
can wani kogon dutse wanda ake
yiwa lakabi da
TASKAR AJALI,Masana tarihin
wannan kogon dutse
sun tabbatar da cewa fiye da
shekaru dubu uku baya
babu wanda yasan hanyar da
za'abi a je inda
wannan kogo yake kuma kogo ne
wanda babu komai
a cikinsa face tarin dukiya ta
zinare,lu'u
lu'u,jauhari,murjani da sauran
duwatsu masu
daraja,wadanda aljanu ke satowa
daga sassan
bangaroro na duniya suna kaiwa
can su boye tun
daga farkon wanzuwar duniya
kawo iyanzu.Su kansu
aljanun da suke kai wannan dukiya
izuwa kogon
Taskar Ajali a makance suke shiga
dajin kuma su
fito a makance domin duk wanda
ya shigeshi
idanunsa a bude toya daina gani
kenan har
abada.Tsananin mugunta ce tasa
aljanun suka rinka
kai duniyar izuwa taskar ajali
saboda kawai basa son
waninsu ya mallaki dukiyar
kwatankwacin irin tasu
ko ta iyayen gidansu,inda za'a ce
su koma izuwa
taskar ajali idanunsu a bude ba
zasu iya gane
hanyar ba dama da karfin sihirin
tsafi kadai ake
zuwa wajen.Boka Salmara ya gano
cewa shi ko wani
jininsa zai iya zuwa taskar ajali
idanunsa a bude
kuma harma ya sami nasarar zana
taswirar zuwa
can din amma dayaga cutar ajali
ta kamashi sai ya
yanke shawarar yakai tasa dukiyar
izuwa can yadda
babu mai iya mallakarta har
abada,sannan kuma sai
ya raba taswirar izuwa kaso uku
kaso na farko na
taswirar sai ya barshi a jikin
jemammiyar fatar
dabba,kaso na biyu sai ya zanashi a
gadon bayan
wata yarinya yar shekara tara a
duniya wacce ta
kasance hadimarsa ce,ita dai
wannan yarinyra ana
kiranta da Suna Sarila.Asalin Sarila
tsintarta Boka
Salmara yayi tun tana jaririya a
wani daji inda aka
tare wadansu fatake aka kashesu
aka kwashe
dukiyarsu.Boka Salmara yazo
giftawa ne ya hango
Sarila tana ta tsala kuka irin na
jarirai har ya gifta ta
sai tausayi ya fado masa a rai ya
dawo ya
dauketa.Daga wannan rana yaci
gaba da renonta
amma sai ya baiwa wata farkarsa
tana shayar da
ita,ita kuwa wannan farka tasa ana
kiranta da suna
Basma.Saida Basma ta shafe
shekara uku tana renon
Sarila ya zamana cewa ta shaku da
ita tamkar itace
ta haifeta amma dare daya boka
Salmara yazo ya
rabata da ita.A wannan rana
Basma tayi kuka kamar
ranta zai fita kuma babu irin rokon
da bata yiwa
boka Salmara ba akan ya bar mata
Salira amma yaki
kawai sai ya tafi da Salira izuwa
gidansa yaci gaba
da renonta kuma ta zama kamar
tafinta a tsakaninsa
da aljanun da sukeyi masa hidima
ya zamana cewa
tana taimaka masa matuka a
harkokinsa na tsafi
amma har tsawon shekara shida
bata taba fita ba
daga cikin gidansa tun daga ranar
daya kawota.Sau
daya a cikin wata guda Boka
Salmara ya amincewa
Basma tazo gidansa taga Sarila
kuma bai taba yarda
ta kusanceta ba saidai suga juna a
daga nesa.A
watan karshe da Basma ta kawo
Ziyare ne izuwa
Gidan Boka Salmara bayan taga
Sarila zuciyarta tayi
fari sai ta juya da nufin ta fice
daga cikin gidan kawai
saitaji boka Salmara ya kira
sunanta.Cikin mamaki ta
tsaya kuma ta juya ta fuskanceshi
saboda rabon
daya kira sunanta ma tsawon
shekara shida kenan
tun daga ranar daya rabata da
Sarila bare wani abu
ya shiga tsakaninsu.Kawai sai taji
Boka Salmara ya
kama hannunta ya jata izuwa can
dakinsa na
tsafi.Ashe kamuwa yayi da
tsananin bukatarta don
haka a wannan lokaci hankalinsa
ya dan gushe bai
san sa'adda ya kaita cikin dakin
tsafinsa ba ya
kawar da bukatar tasa.Faruwar
hakan keda wuya sai
yaji rabin jikinsa ya shanye ashe ya
karya tasirin
tsafin nasa ne bai sani ba.Koda ya
gane hakan sai
ya kurma uban ihu kuma ya fashe
da kukan bakin
ciki a yayin da nadama tazo
masa.Al'amarin daya
razana Basma da Sarila
kenan.Sarila ta fashe da
kuka tana mai tambayarsa tace
yakai Abbana ina
dalilin wannan kuka naka?Waishin
ma menene dalilin
da yasa ka nisantani da wannan
mahaifiyar tawa?
Koda jin wannan tambaya sai boka
Salmara ya dubi
Sarila cikin alamun tsananin
tausayi tace yake 'yata
ki gafarceni bisa abinda zan gaya
miki yanzu domin
wani babban sirri ne wanda ban
taba gaya miki
ba,kafin haka inason ki sani cewa
daga yau duk
sirrikan tsafina sun mutu bazan iya
yin komai ba da
karfin sihirin tsafi face abu
guda,wannan abu kuwa
shine zan iya kwashe duk dukiyata
dana mallaka na
kaita can kogon Taskar
Ajali.Wannan dukiya tawa
zan kaita canne saboda babu
wanda zai iya
amfanarta face ni kadai ko kuma
jinina ke ba jinina
bace,tsintarki nayi a daji an kashe
iyayenki da
dukkan jama'arsu kece kadai kika
tsira da rayuwarki
kuma a wannan lokaci kina
jaririya.Koda jin wannan
batu sai idanun Sarila suka zazzaro
ta cika da
tsananin mamaki gami da dimbin
bakin ciki kuma
taji ta tsanin komai da kowa kawai
sai ta fashe da
kuka.Boka Salmara yace waccan da
kike kallo a
matsayin mahaifiyarki kuwa ba ita
ce ta haifeki ba
amma ta shayar dake kuma ta
reneki har tsawon
shekaru uku daga nan na karbeki
daga hannunta
naci gaba da renonki kawo izuwa
yanzu da kika cika
shekara tara a duniya.Yake Sarila ki
sani cewa
rayuwata ta zo karshe nan da cikar
kwanaki kadan
zan mutu na barki amma ki sani
cewa ba zaki taba
wulakanta ba a duniya domin zaki
sami daukaka da
arziki mai yawa amma zaki nisanta
da kowa da
dukkan mutane kuma zaki yi
rayiwa ne a wurin da
dan adam bai isa yaje ba koma
hatsabibancinsa
kuma aljanu ne zasu rinka yimiki
hidima sai kuma
tsurarun bayi na bil'adama da zaki
iskesu acan
wadanda dama can nine na
tanadesu domin ki.Koda
Boka Salmara yazo nan a
jawabinsa sai Salira ta
rungumeshi ta sake fashewa da
matsanancin kuka
da kyar ya rarrasheta tayi shiru
sannan ya janyeta
daga cikin jikinsa ya dubi Basma
yace...
Zidane kd.
TASKAR AJALI!!!
Littafi Na Daya (1)
Part C
Ya dubi Basma yace ke kuma daga
yau dinnan kin
sami gaba dayan sirrikan tsafina
kuma babu wanda
zai iya gadarsu daga gareki face ki
sami juna biyu
dani wanda sai tsananin sa'a da
rabo sannan hakan
zata iya kasancewa.Ke kanki baki
isa ki iya zuwa
kogon taskar ajali ba ki dauko
wadannan dukiya
tawa amma inda zaki sami juna
biyu sakamakon
sadauwar da mukayi to duk abinda
kika haifa walau
mace ko namiji zai iya zuwa Taskar
Ajali ya dauko
wannan dukiya tawa amma fa sai
ya gwammace
baije ba saboda tsananin wahalar
da zai sha a cikin
tafiyarsa izuwa Taskar Ajaki don
saiya gwammace
MUTUWA akan RAYUWA.Ke ma zaki
sami
daukaka,mulki da dukiya kuma har
ki bar duniya ba
zakiyi aure ba kuma babu wani da
namiji daya isa
ya sake tarawa dake.Da wannan
furuci nakeyi muku
bankwana na karshe don haka na
sallameku saiku
kama gabanku amma ku sani cewa
zamanku a tare
ba zai haifar muku da komai ba
face masifu,tashin
hankali da annoba iri iri don haka
dolene ku rabu ko
wannan ku yabi hanyarsa
daban,amma idan kuna
shakka ne akan hakan to ku jarraba
zama a waje
guda zaku sha mamaki.Koda gama
fadin hakan sai
Boka Salmara yayi tari sau uku
saiga gudan jini ya
furzo daga cikin bakinsa.Take
idanunsa suka juye
sukayi jawur ya kife kasa yana
numfashi sama sama
al'amarin da yasa Sarila da Basma
suka kamu da
tsananin tausayinsa kenan kuma
suka fashe da
kuka.Cikin matukar karfin hali boka
Salmara ya mike
tsaye ya nufi inda kofar dakinsa na
tsafi yake har ya
sanya kafarsa guda izuwa cikin
dakin saiya tsaya
cak ya juyo ya yafito Basma da
hannu ta taho
gareshi,kawai sai ya zura hannunsa
cikin aljihun
rigarsa ya fiddo da taswirar zuwa
kogon taskar Ajali
dake jikin jemammiyar fata ya
mika mata ta karba
yace wannan taswira ce izuwa
kogon taskar ajali
amma kaso daya cikin ukunta ki
duba gadon bayan
Sarila kaso na biyu na zane
akai,kaso na uku kuwa
yana can inda zaki zauna ki karasa
sauran rayuwarki
ta duniya rubuve akan wani allo na
katako.Dole sai
an hada wadannan taswira guda
uku sannan za'a iya
samun cikakken zance na hanyar
da za'abi aje
kogon taskar ajali.Kinga kenan idan
kin sami damar
samun juna biyu na kin haifeshi to
zaki iya baki
taswirar guda biyu,ta cikon ukun
kuwa dolene ya tafi
neman Sarila.Ki sani cewa Sarila na
fita daga nan
yanzu Aljanu ne zasu dauketa su
kaita can tsakiyar
birnin Jannatul Duniya.Wannan
tsibiri shine wurin da
yafi ko ina tsaro da ni'ima a cikin
kaf din wannan
duniya,kuma yana tsakanin
karshen birnin sin da
Mastur Kusa da dan karshen
bangon duniya.Ba'a
tsufa a wannan tsuburi ba'a rashin
lafiya koda kuwa
mutum ko aljan zai shekara dubu a
wajen,amma ana
mutuwa.Koda Boka Salmara yazo
nan a jawabinsa
sai ya yiwa Basma kallon karshe.A
lokacin da
hawaye ya zubo masa sannan ya
juya da nufin ya
shige cikin dakinsa na tsafi amma
sai Basma ta
dakatar dashi tace,yakai Salmara
yanzu ta yaya zan
kai kaina inda zan karasa sauran
tawa rayuwar kuma
inane wannan wuri?Koda jin
wannan tambaya sai
Boka Salmara ya numfasa yace
kamar yadda aljanu
zasu kai Sarila Tsuburin Jannatul
Duniya kema
akwai wanda zai yi miki jagora
izuwa masauki
wanda shine Darul Azmin,shi kuwa
wannan wuri a
karshen bangon duniya yake daf da
birnin
Hindu,zamanki acan shine kadai
kubutar dukkanin
matsafan duniya,in ba haka ba
kuwa sai ki zame
musu annoba mai shayar dasu
mugunyar mutuwa
domin sai an wayi gari babu sauran
boka guda daya
a raye a doron kasa face ke.Idan
kuma kinason ki
zama sanadin mutuwar miliyoyin
wadannan rayuka
to ki cigaba da zama a cikin
mutane kada ki tafi
izuwa wannan masauki naki.Koda
gama fadin hakan
sai Boka Salmara ya shige izuwa
cikin dakin halwar
tsafin nasa bai yarda ya sake
waigowa ba ya dubi
Basma da Sarila.Ai kuwa yana
shigewa sai kofar
dakin ta kullo kanta,wannan shine
ganin karshe
wanda Basma da Sarila suka yiwa
Boka Salmara.Ba
tare da bata lokaci ba kuwa Basma
da Sarila suka
fice daga cikin gidan Boka Salmara
suna fita sai
gidan ya bace bat tamkar bai taba
wanzuwa ba a
wajen.Faruwar hakan keda wuya
kafin Basma ta dubi
Sarila tace wani sai sukaji wata iska
mai karfi a
samansu.Kafin su daga kawunansu
suma suga
abinda yayi musu inuwa tuni an
suri Sarila anyi
sama da ita,ita da abinda ya
dauketan kafin dakika
guda sun kule a cikin gajimare.Ita
kuwa Basma sai
ta hango wani mutum akan wani
farin doki sanye da
bakaken tufafi ya durfafo inda take
a sukwane,abinda
ya razana ta dangane da mutumin
shine ya lullube
kansa da bakin mayafi amma kuma
bashi da
fuska,ma'ana babu fata,tsoka ko
kashi akan fuskarsa
bare a sami hanci,baki ko ido kawai
sai wani irin
haske mai dallare idanu tamkar an
ajiye madubi a
rana.Babu shiri Basma ta sunkui da
kanta kas ta
daina kallon fuskar mutumin da
isowar wannan
mutumin daf da Basma sai ya
sureta da hannu daya
ya azata a bayansa bisa wannan
farin doki ya
zabureshi cikin azababben gudu na
gaba
misali.Tunda Basma tazo duniya
bata taba ganin
doki mai gudun wannan doki ba
domin ko walkiya
bata fishi saurin baiyana da bacewa
ba,ai kuwa ko
rabin sa'a basuyi ba da fara
wannan tafiya ba sai
barci mai nauyi ya dauke
Basma.Lokacin da Basma
ta farka daga barci sai ta tsinci
kanta a cikin wani
kasaitaccen daki wanda komai
dake cikinsa anyi
shine da gilashin lu'u lu'i mai launi
fari hatta
luntsumemen gadon da take kao
kuwa.Tana bude
idanunta taji kanta yayi mata nauyi
tamkar an dora
mata katon dutse haka kuma taji
ciwon kai ya
kamata,tsaitsaye a gefe daya a
bayanta gadon da
take kwance a gabansa kuyangi ne
na bil'adama su
arba'in da daya,koda kuyangin suka
ga Basma ta
farka daga barci sai biyu
™Abubakar Haleefah Physicist™
daga cikinsu sukayi sauri suka
matso gareta.Daya
na ruke da tambulan cike da
sabuwar madarar
shanu mai gardi da dumi dayar
kuma na rike da
dogon kofi na gilashi take suka
zuba mata madarar
a cikin kofin suka cika shi taf
sannan suka bata ta
kama sha.Bata san sa'adda ta
shanye shi tas
saboda dadin dandanon tana gama
shanye nonon taji
ta daina ciwon kan take ta dawo
cikin haiyacinta tare
da lura da cewa ashe an canja mata
ma suturar
jikinta an sanya mata wata.Farar
doguwar riga cikin
dimauta da firgici Basma ta dubi
kuyangar data bata
madarar da tasha tace yaushe ne
nazo nan kuma
ina abokin tafiya wanda ya kawo ni
nan akan farin
dokinsa?Koda jin wannan tambaya
sai kuyangar tayi
murmushi tace ya shugabata ai
abokin tafiyarki
manzo ne kawai ba kowa ba,ya
gama aikinsa ya tafi
izuwa can kasarsu ta birnin matsafa
a wata nahiya
dake cikin kasashen aljanu.Ki sani
cewa yau
kwanaki arba'in da daya kina barci
tun akan
hanyarku daga can birninku zuwa
nan dajin Iblas
dake daf da birnin Hindu,ki kwantar
da hankalinki ya
shugaba kiyi sani cewa indai kina
nan baki da wata
fargaba ko bakin ciki ko kewa
kuma duk abinda
kikeso indai akwai shi anan cikin
duniya zaki
sameshi face abu guda wato
abokin rayuwa.Kowacce
'ya mace tana bukatar namiji
abokin rayuwarta
amma ke ba zaki taba samun saba
har ki kammala
rayuwar kwanakinki na
duniya.Koda kuyangar tazo
nan a jawabinta sai hankalin Basma
ya dugunzuma
ainun ta rasa abin dake mata dadi a
duniya.Daga
wannan rana Basma ta tsinci kanta
a cikin sabuwar
rayuwa irin wadda bata taba
tsintar kanta a ciki ba
domin rayuwa ce wadda babu
matsalar ci da sha ga
makwanci wanda ma yafi na
wadansu sarakan,kuma
babu abinda takeyi da kanta komai
saidai kuyangi
suyi mata,abinda ya daurewa
Basma kai shine ganin
yadda sauran kuyangin suke
rayuwa a wannan tsibiri
a cikin daji haka ba tare da wata
rayuwa ba domin a
ganinta babu rayuwar da tafi dadi
face ta zama a
cikin gari tare da al'umma koda
kuwa dadin da
mutum zaiji a irin wadannan gidaje
na bokaye babu
kamarsa a duniya.Koda Basma tazo
nan a jawabinta
sai idanunta suka ciko da kwallah
hawaye ya zubo
mata,nan ta kamu da tsananin
bakin ciki gami da
takaici taji tayi nadamar kaddarar
data hadata da
Boka Salmara a tafarkin barikanci.A
kwana a tashi,a
ranar da Basma ta sami kwanaki
sittin daidai a
wannan kayataccen gida na daji,sai
ta wayi gari a
cikin tashin zuciya har da
kumallo.Nan da nan ta fita
daga cikin haiyacinta har ta fadi
kasa a lokacin da
taji jiri ya kwasheta kuma kanta ya
kamu da ciwo
cikin hanzari kuma a guje kuyangin
suka rugo da
gudu suka dauketa suka kaita can
cikin turakarta
suka kwantar da ita a kan
gado.Shugabar kuyangin
wata tsohuwa tasa aka rinka gasa
gashin Basma
sannan ta kama tsintsiyar
hannunta ta rike tana
nazari irin na likitoci.A daidai
wannan lokaci ne
Basma ta farfado daga dogon
suman da tayi,koda ta
bude idanunta saitayi arba da
wannan tsohuwa
zaune a gabanta ta kura mata
idanu tana yi mata
murmushi.Kawai sai tsohuwar ta
bude baki tace yake
Basma muna ta yaki murna saboda
kin sami juna
biyu tare da shugabanmu Boka
Salmara kafin
ajalinsa ya cika.Tabbas abinda zaki
haifa zai zamo
babban jarumi abin kwatance
kuma shine kadai zai
iya zuwa TASKAR AJALI ya dauko
dukiyar da
mahaifinsa ya tara wato Boka
Salmara.....
TASKAR AJALI!!!
Littafi Na Daya (1)
Part D
Ya tara wato Boka Salmara.Yake
Basma kiyi sani
cewa duk mahalukin daya mallaki
wannan dukiya ta
Boka Salmara zai iya amfani da ita
wajen mulkar
wannan duniya gaba
dayanta,domin gaba dayan
attajirai da sarakai sai sun zamo
almajirai masu yin
bara a gabansa.Akwai matsaloli
guda biyu a gaba ga
Jarumi ko Jarumar da zaki
haifa.Matsala ta farko
itace dole ne a baiwa dan naki ko
yar taki horon
yaki mai tsananin gaske yadda zai
iya tsare taswirar
da zaki danka masa guda biyu
saboda matsafa da
masu mulki zasuyi kokarin rabata
da su.Matsala ta
biyu kuma waccan yarinya Sarila
wacce zannen
taswirar na uku ke bisa gadon
bayanta zata baro
can Jannatul Duniya a lokacin da
yarki ko danki ya
shiga duniya nemanta.Zai kasance
suna farautar
juna a wannan lokaci,ita Sarila zata
kasance
azzaluma ainun kuma karfin
damtsenta dana sihirinta
sai ya ninka na danki ko yarki
saboda albarkacin
rayuwar datayi a tsibirin Daulatul
Duniya.Burinta
shine taga danki ko yarki ta kashe
ta ta dauke
Taswirar biyun dake hannunta,ita
ma yar taki ko dan
naki burinsa ya kashe Sarila ya
kwafe taswirar dake
zane a bayanta domin ya sami
damar zuwa Taskar
Ajali.Wannan 'da naki ko ya taki ba
zai sami nasara
ba akan Sarila face da taimakon
wani bakon saurayi
wanda ba'a san daga nahiyar dazai
fito ba,shidai
wannan saurayi ya kasance
kyakkyawa abin
kwatance kuma bashi da karfin
damtse ko kadan
kuma bashi da karfin sihirin tsafi
sannan bai iya yaki
ba,asali ma bai taba rike takobi ba
saidai ya kasance
yana da wata irin baiwa ta
musamman sannan yana
da tsananin sa'a da rabo bisa duk
abinda yasa a
gabansa duk da cewa shi mutum
ne mai matukar
tsoro,wannan saurayi shine kadai
zai iya takawa
Sarila birki a cikin zaluncinta kuma
shine kadai zai
iya kare abinda zaki haifa daga
sharrin Sarila.Koda
tsohuwar tazo nan a jawabinta sai
bakin ciki ya sake
turnuke Basma hawaye ya zubo
mata tace yanzu
kenan Sarila da abinda zan haifa
zasu zamo
ABOKAN GABA har dayansu ya zamo
sanadin ajalin
daya alhalin su duka nice na shayar
dasu ina
kallonsu a matsayin 'ya'yana.Koda
gama fadin hakan
sai Basma ta kurma uban ihu
sannan ta fashe da
matsanancin kuka na bakin ciki,ita
kuwa tsohuwar
sai ta shiga rarrashinta tana mai
cewa babu yadda
zakiyi da kaddarar rayuwarki tunda
baki da ikon
sauyata.Haka dai tsohuwar
tacigaba da rarrashinta
har izuwa lokacin mai dan tsawo
sannan ta shawo
kanta ta daina kukan.Daga wannan
rana kuyangin
suka ci gaba da kula da Basma ya
zamana cewa
juna biyunta ya dada Girma har
watanni tara suka
cika,da tsakiyar dare nakuda ta zo
mata kuma a
cikin dakiku kadan ta haife
santaleliyar 'yarta.Da
kwanaki bakwai suka cika aka
radawa yarinyar suna
Yazirina,nan fa Basma da
kuyancinta suka cigaba da
renon Yazirina har takai shekaru
shida a duniya
kuma tun a sannan ne aka rinka
ganin abubuwan
al'ajabi a tare da Yazirina domin
tana iya sarrafa
komai da karfin sihirin tsafi domin
komai nauyin abu
data dauke shi da hannu sai ta
daga shi sama takai
shi inda takeso ta ajiye.Tana da
shekaru shida ne
akaga wadansu zakakuron aljanu
suna zuwa suna
bata horon yaki,tun a wannan
lokaci Basma ta sanar
da Yazirina komai dangane da
rayuwarta da kuma
gagarumin aikin dake gabanta nan
gaba idan ta cika
Budurwa.Koda Yazirina taji cewar
an sameta ne bata
hanyar aure ba sai bakin ciki ya
turnuketa yayi mata
kututu a cikin ranta domin saida ta
kwana ta yini
tana kuka baci basha.A sannan ne
taji ta tsani
Basma kuma ta tsani Boka
Salmara,kai saida ma tayi
yunkurin kashe kanta da kyar
aljanun gidan da
kuyangin dake kula da ita suka
rarrasheta ta hakura
amma duk da haka saida ta kwana
uku bata yiwa
Basma magana ba,kuma bata
zuwa,Basma na zaune
a cikin turakarta ta hada kai da
guiwa tana tunani da
kuka bisa ganin yadda yar cikinta
ta tsaneta,lokaci
guda sai kawai taji an turo kofar
dakin,koda Basma
ta dago kanta sai tafa ashe Yazirina
ce ta shigo
idanunta sunyi sharkaf da
hawaye,cikin sanyin jiki
Yazirina ta karaso gaban Basma ta
durkusa a
gabanta bisa kafafunta ta sunkui da
kanta kas
tace,yake ummina kiyi mini aikin
gafara domin nayi
babban kuskure dana nuna
kiyayyara a gareki tunda
bani da kamar ki ko inaso ko
banaso ban isa na
sauyawa tuwo suna ba.Koda jin
wannan baty sai
mamaki da farinciki suka lullube
Bsma domin bata
taba zaton cewa yarinya yar
shekara shida kamar
Yazirina zatayi irin wannan tunani
ba.Nan take
Basma ta rungume Yazirina suka
fashe da kukan
farin ciki tare.Daga wannan rana
Basma da Yazirina
suka cigaba da zama cikin farin ciki
har Yazirina ta
cika shekaru goma sha biyar a
duniya.A wannan
lokaci ne kyawun surar jikinta ya
baiyana sosai
kuma ya zamana cewa ta sami
horon yaki mai
tsanani yadda tana iya tarwatsa
gungun dakarun
yaki na aljanu ma.Wata rana da
safe sai Yazirina
taga gaba daya yanayin Basma ya
sauya,alamun
cewa hankalinta a tashe yake
domin ta kasa cin
abinci kuma idanunta sun kada
sunyi jawur alamar
cewa tasha kuka a boye.Koda ganin
haka sai
hankalin Yazirina ya dugunzuma
ainun ta dubi
Basma cikin alamun tsananin
damuwa tace yake
Ummina ina dalilin sauyin yanayi
haka a tare dake
alhalin an gaya mini cewa baki da
wata damuwa a
gidan nan.Sa'adda Basma taji
wannan tambaya saita
mike tsaye daga kan gadonta
maimakon tace wano
abu sai kawai ta kama hannunta ta
jata suka fice
daga cikin turakar suka nufi wani
bangare daban na
gidan.Wani lungu suka shiga mai
zurfin gaske kuma
yana da dan duhu.Tun daga
tasowar Yazirina kawo
izuwa girmanta ko sau daya bata
taba shiga wannan
lungu ba saboda ganin cewa gaba
dayan hadiman
gidan ma bata taba ganin wanda
™Abubakar Haleefah Physicist™
ya shiga ba don haka tun tana
yarinya taje tsoron
lungun bisa mamaki sai taga
Basma sai dada
kutsawa take cikin lungun ba tare
da wata fargabar
ba saida sukayi doguwar tafiya a
cikin lungun
tamkar bazasu isa karshensa har
saida Yazirina ta
kosa sannan suka iso wani daki
wanda bashi da
kofa.Da isarsu gaban dakin sai
Basma ta dafa garun
dakin da hannunta na hagu.Take
garun ya tsage
gida biyu ya bude musu hanya
suka shige ciki suna
shiga sai bangon ya koma ya
hada.Babu komai a
cikin wannan karamin daki face
akwatuna na gilashi
sama da guda miliyan daya,wata
kan wata,gaba daya
akwatunan a rufe suke kuma babu
kofa ko murfi a
jikinsa wanda za'ayi budewa ko a
zura hannu ciki
don dauko abindake ciki kowacce
akwatu na dauke
da abu guda daya ne jal mai
muhimmanci.Kai tsaye
Basma ta nufi wata akwatai mai
dauke da wani Allon
Katako da isarta gaban akwatin sai
ta dafata da
hannun hagu take akwatun ta dare
tamkar an yanka
tsakiyar tuffa.Ba tare da tsoron
komai ba Basma ta
zura hannunta cikin akwatun ta
dauko wannan allon
katako.faruwar hakan keda wuya
sai akwatun ya
bace bat tamkar bai taba wanzuwa
ba a wajen
Basma ta mikawa Yazarina allon ta
karba sannan ta
sake zura hannunta cikin aljihun
rigarta ta dauko
jemammiyar fata ta sake danka
mata tace wannan
abubuwa biyu dana baki ba komai
bane a jikinsu
face zanen taswirar izuwa taskar
ajali wanda
mahaifinki yabar miki gado amma
kiyi sani cewa ba
zasuyi amfani ba har sai kin tafi
farauta yar uwarki
Sarila kin kasheta kin kwafi
taswirar dake zane a kan
gadon bayanta kin hada da
wadannan guda biyu
dake hannunki.Kamar yadda na
gaya miki a baya
yanzu ne zaki shiga sabuwar
rayuwa ta biyu wato
zaki bar wannan daji ki shiga cikin
duniya domin
farautar Sarila ki sani cewa nice na
shayar da Sarila
don haka na dauketa tamkar yar
cikina don haka
bana son dayanku ta cutar da yar
uwarta.Ina rokonki
alfarma guda daya idan har akwai
hanyar da zakibi
ki kwafi taswirar dake kan gadon
bayan Sarila ba
tare da kin kasheta ba to kiyi
hakan.A yaune zamuyi
bankwana ni dake ki shiga cikin
duniya kuma bani
da tabbacin zamu sake saduwa bisa
wannan dalili
ne kika ga yanayina ya sauya gaba
daya domin tun
jiya nake ta faman shara kuka da
bakin ciki bisa
ganin cewa lokacin rabuwarmu
yazo.Koda Basma
tazo nan a jawabinta sai hawaye ya
zubowa Yazirina
ta rungume Basma suka fashe da
kuka tare.Saida
suka dan jima a kankame da juna
sannan Yazirina ta
janye jikinta daga cikin na Basma
suka dubi juna a
lokacin da hawaye ke sartu akan
kumatunta
tace,yake ummina kiyi sani cewa
babu maganar
sassauci ko tausayi ko kuma jin kai
tsakanina da yar
uwarta Sarila musamman idan
kikayi la'akari da
yanayin yadda halayenta zasu
kasance na rashin
tausayi da kuma zalunci.Duk danaji
ance sai ta
ninkani a karfin damtse dana sihirin
tsafi da kuma
iya yaki ni bazan ji tsoronta ba
kuma ba zan fasa
tunkararta ba ko da kuwa zan rasa
raina,saboda ni a
rayuwata babu mutumin dana
tsana sama da
azzalumi.Da wannan furuci nake yi
miki sallamar
karshe gami da bankwana amma
nayi alkawari
cewar bayan na cika burina na
dauko dukiyar
mahaifina dake can Taskar Ajali zan
dawo nan na
rabaki da wannan gida mu koma
cikin gari muci
gaba da rayuwa a lokacin da zan
zama sarauniyar
duniya.Koda gama fadin hakan sai
jaruma Yazirina
ta juya ta fice daga cikin wannan
daki tana waigen
mahaifiyarta ta su duka suna zubar
da
hawaye.Lokacin da Boka Matawus
Bin Ashshahab
yazo nan a labarin da yake baiwa
Sarki Ubaiyu sai
kowa dake cikin fadar ya kamu da
tsananin mamaki
gami da tsoro musamman sarki
Ubaiyu wanda
hankalinsa ya dugunzuma ainun
fiye da kowa.
08161272634
TASKAR AJALI!!!
Littafi Na Daya (1)
Part E
Hankalinsa ya tashi Ainun fiye da
kowa.Cikin
kaduwa sarki Ubaiyu ya dubi Boka
Matawus yace
yanzu ina dabara?Ka gaya mini
cewa idan har daya
daga cikin wadannan yan mata
walau Yazirina ko
Sarila ta sami nasarar zuwa Taskar
Ajali ta dauko
dukiyar Boka Salmara saita mulki
duniya gaba
dayanta.Gashi a yanzu mun kasa
kama Yazirina
kuma kace Sarila ta fita
hadari,yanzu shi kenan babu
matakin da zamu iya dauka domin
mu magance
wannan matsala.Koda jin wannan
tambaya sai Boka
Matawus yayi doguwar ajiyar
zuciya gami da sunkui
da kansa kas ya na tunani.Daga can
kuma saiya
dago kai ya dubi Sarki Ubaiyu cikin
alamun tsananin
damuwa sannan tace ya shugabana
akwai hanyoyi
guda biyu kacal wadanda za'a iya
amfani dasu
wajen magance wadannan yan
mata biyu wadanda
suke neman su zamewa duniya
ANNOBA.Koda yake
daya a cikinsu ta gari ce wato ita
Yazirina,ita kuwa
Sarila muguwa ce wadda a halin
yanzu bata iso nan
cikin duniya ba tana can tsibirin
Jannatul Duniya
amma daga yanzu zata iya baiyana
a koyaushe
kuma tana baiyana sai duniya gaba
daya ta san da
baiyanarta.Hanya ta farko da za'abi
a ga bayan
Sarila Da Yazirina shine dole ne
manyan sarakuna
guda hudu na kasashen da babu
kamarsu a wannan
nahiya su hada KARFI DA KARFE su
yake su su
kawar dasu daga doron kasa,kafin
daya daga cikinsu
ta hada taswirorin uku na zuwa
Taskar Ajali a
hannunta.Wannan sarakai hudu
kuwa ba wasu bane
face sarkin kasar Sin da Sarauniyar
Birnin Hindu sai
kuma Sarkin Misra da Sarkin
Kisra,kuma kowanne
sarki dole ne yayi aiki tare da
babban
bokansa.Hanya ta biyu da za'a iya
ganin bayan
wadannan takadiran yan mata
shine akwai wani
bakon sarauyi dan baiwa mai
tsananin sa'a da Baiwa
shine kadai zai iya hallakasu ta
hanyar hikimar ba
wai da makami ba.Koda Boka
Matawus yazo nan a
zancensa sai ran sarki Ubaiyu ya
baci bai san
sa'adda ya dakawa boka Matawus
tsawa ba,kuma ya
mike tsaye zumbur daga kan
karagarsa ta mulki ya
dubeshi a fusace yace wannan
wace irin maganar
banza kake yi mini ne hala alhalin
kasancewa ban
san a inda wannan bakon saurayi
yake ba,ban san
ta yadda zan iya shaida shi ba
kumaka gaya mini
cewa sarakunan kasashe hudu a
halin yanzu tuni
kowannensu ya baza dakarunsa
izuwa kowanne
bangare na duniya domin suyi
farautar Yazirina da
Sarila su rabasu da taswirorin zuwa
Taskar
Ajali.Kaga kenan babu dayansu da
zai yarda a hada
kai saboda son kai da son zuciya
gami da kwadayin
duniya.Lokacin da sarki Ubaiyu
yazo nan a
jawabinsa sai Boka Matawus yace
ubangiji Kartus ya
huci zuciyarka ya shugabana kayi
sani cewa wuya
itake sawa ayi gudun dole idan
lokaci yayi halinsa
ya zamana cewa kowa yaji a jikinsa
to dole ne a
nemi mafita.A wannan lokaci ne
wadannan sarakuna
hudu zasu nemi hadin kan junansu
na dole domin
magance wannan matsala amma
ba yanzu ba ni
yanzu shawarar da zan baka itace
duk yadda zaka yi
domin ka mallaki wannan bakon
saurayi da zai
baiyana ya kasance yana tare dakai
domin idan daya
daga cikin wadannan manyan
sarakuna hudu ya
sami taswirar zuwa Taskar Ajali har
yaje ya debo
dukiyar Boka Salmara to gaba daya
ku sauran
sarakunan duniya sai kun zama
bayinsa.
TURKASHI SAI MUN HADU A CIKIN
LITTAFI NA BIYU
DON JIN CIGABAN WANNAN LABARI.





KU KASANCE DA HAUSA CITY