TASKAR AJALI!!!
Littafi Na Biyu (2)
Part A
KODA jin wannan batu sai idanun
Sarki Ubaiyu suka
zazzaro ya dubi Boka Matawus
cikin razana da
firgita yace waishin a kan wane
dalili zamu zamo
bawan wanda ya mallaki wannan
dukiya dake Taskar
Ajali?Koda jin wannan tambaya sai
Boka Matawus
yayi murmushi yace,yanzu kayi
tambaya mai
matukar muhimmanci ya
shugabana kayi sani cewa
daga ranar da aka sami mahalukin
daya debo
waccan dukiya ta Boka Salmara
dake can Taskar
Ajali ya kawota kasarsa to daga
wannan rana sauran
kasashen duniya zasu shiga cikin
fari,fatara da
munin talauci saboda babu wata
kasa da za'a iyayin
noma a kanta face kasar garin da
aka ajiye wannan
dukiya.Babu inda za'a iya siye da
siyarwa face
wannan kasa,kai hatta abinci saidai
a rinka
fataucinsa daga birnin da aka ajiye
wannan dukiya
ana kai shi izuwa sauran kasashen
duniya kuma
inda duniyar zata taru domin ta
kwace dukiyar daga
hannun mai ita ba zata iya ba,kaga
kenan dole ne
sauran sarakuna su zamo almajirai
a gaban mai
wannan dukiya domin su tsira daga
yunwa da
talauci su da jama'arsu.Ka sani
cewa ko akan hanya
yan fashi basu isa su iya kwace irin
dukiyar garin da
aka ajiye wannan dukiya ba ta
Boka Salmara.A
takaice dai duk sarkin da ya sami
nasarar debo
wannan dukiya sai ya zamo
kadagaran bakin tulu
kuma saiya zama kangarau
maganin gagararru.Koda
Boka Matawus yazo nan a
jawabinsa sai sarki
Ubaiyu yaja dogon numfashi cikin
ajiyar zuciya gami
da karayar zuciya ya dago kai ya
dubi Boka Matawus
yace na baka ragamar nemo
wannan bakon saurayi
dan baiwa da zai baiyana kuma
sarkin yaki da
dakarunsa ne zasu taimaka maka
wajen yin wannan
aiki,kudi ko nawa ake bukata zan
bayar dasu don
ganin wannan aiki ya cika.Ni kam
na cire raina daga
kan tunanin mallakar dukiyar Boka
Salmara amma
inason lallai na mallaki wannan
saurayi dan baiwa
domin ya kawar mini da duk wani
mahaluki mai son
yaje ya debo wannan dukiya ya
janyowa duniya
gagarumar annoba wacce take
daidai da GOBARA
DAGA KOGI wacce bata da
magani.Koda jin wannan
batu sai fuskar boka Matawus ta
fadada da
murmushi yace tabbas yanzu kayi
tunani da shawara
mafi alheri a garemu baki daya ya
shugabana.Gama
fadin hakan keda wuya sai Boka
Matawus ya dubi
sarkin yaki yayi masa wata inkiya a
lokacin daya
juya ya nufi kofar fita daga cikin
fadar.Cikin hanzari
sarki yaki da mukarrabansa suka
mike tsaye da
sauri suka takewa Boka Matawus
baya,wannan shine
abinda ya faru a fadar sarki Ubaiyu
na birnin
Yamein.
*Al'amarin Jaruma Yazirina da
Barawo Muhajid kuwa
bayan ta dafa kafadarsa sun bace
bat daga wannan
wuri inda ta fafata da dakarun
sumamen,basu
baiyana a ko ina ba sai wata
unguwar daban dake
nesa sosai da inda akayi gumurzu
kuma agefe
hanya suka bayyana inda mutane
ke
wucewa.Baiyanarsu keda wuya sai
Yazirina tayi sauri
ta dauko mayafi daga cikin jakarta
ta guzuri ta
lullube jikinta yadda idanunta
kadai ake gani,kawai
sai ta dubi Mujahid a lokacin da
taga har yanzu
jikinsa bai daina bari ba domin gani
yake kamar a
ko yaushe shugaban wadannan
dakarun sumamen
zai iya baiyana tsulum a gabansa,ta
dafa shi tace kai
matsoracin banza kwantar da
hankalinka kayi sani
cewa babu wani makiyi da zai
riskemu anan yanzu
ka nemo mana gidan da zamu
kwana domin ni bana
son na kara yin magana da kowa
kuma ban son aga
fuskata.Koda jin haka sai Mujahid
yayi murmushi
yace kada ki damu ya shugabata zo
muje wani wuri
dake can gaba kadan na san ida
zamu sami mai
kyau.Koda gama fadin hakan sai
Mujahid ya wuce
gaba ba tare da fargabar komai ba
kuwa Yazirina ta
bishi a baya kai kace miji da mata
ne.Yar gajeriyar
tafiya sukayi suka iso kofar wani
gida mai tsananin
shiru tamkar babu kowa a
cikinsa,da zuwansu sai
mujahid ya kwankwasa kofar gidan
har sau
bakwai,cikin alamun fushi Yazirina
ta dubi Mujahid
tace wannan wane irin shashancin
banza ne haka
zakayi ta kwankwasa kofar gidan
mutane haka har
sau bakwai ko kuwa kurame ne a
cikin gidan.Koda
jin wannan tambaya sai Mujahid
yayi murmushi yace
dadi na da dan adam kenan ya cika
garaje da
mantuwa,ashe har kin manta ke da
bakin ki kince
babu inda ban sani ba a cikin
garin,wannan
kwankwasa kofar da kikaga nayi
har sau bakwai to
inkiya ce na yiwa mai gidan domin
ya gano wanda
yazo.Ai kuwa kafin mujahid ya
gama rufe bakinsa
tuni sunji karar zare sakatu uku
dake jikin kofar
sannan kuma sai sukaji an sanya
kuba a cikin kofar
an murde har sau uku sannan aka
turo kofar gidan
ta wangame sai ga wani dan
gajeran mutum mai
katon ciki ya fito.Daga shi sai
gajeran wando a
jikinsa iya guiwa sai wani mayafi
daya rataya a
kafadarsa gashi baki ne sosai
fuskarsa babu gemu
kuma kansa yasha askin kwarya
molo.A hannunsa
na hagu akwai dan karamin tulu na
giya yana
kwankwada kuma a cikin maye
yake don haka baima
lura da Yazirina ba wacce ke tsaye
a gefe daya
lullube cikin mayafi.Koda gajeran
mutumin ya dubi
Mujahid saiya bushe da dariya irin
ta yan giya
sannan yace kai shegen duniya
lallai yau ma dawa
tayi nama kenan,ina akaje akayi
aiki mai riba haka
har da akazo neman hayar gidana
mai tsaada..?Koda
jin wannan tambaya sai Mujahid ya
doki kafadar
mutumin yace kai Andalu tsohon
kwallon
duniya,dubi bayana da kyau ka
gani tare nake
da..Kafin Mujahid ya karasa abinda
yakeson fadi sai
Yazirina ta tari numfashinsa tace ni
matarsa ce daki
nake son ka bamu mafi kyau a cikin
wannan
gida.Koda Andalu yaji sautin
zazzakar muryar
Yazirina sai ya bangaje Mujahid
daga gabansa ya
kura mata idanu duk da cewa gaba
dayan jikinta da
fuskarta a lullube yake sannan ya
juya ya dubi
Mujahid yace wai kai wane irin yaro
ne DAN BAIWA
haka mai tsananin sa'a da
™Abubakar Haleefah Physicist™
rabo,ba'a taba kama ka ba a wajen
yin sata ko ayi
maka rauni yanzu gashi ka auro
dalleliyar mace
wacce muryarta kadai ta isa ta
debe kewa koda tafi
kowace mace muni a duniya.To
gaskiya dakin daya
rage babu kowa a gidan nan shine
mafi tsada sai
kun bani dinare dubu uku,kafin
Andalu ya gama rufe
bakinsa tuni Yazirina ta bude jakar
Guzurinta ta fiddo
da kullin dinare guda,sannan tace
kaimu dakin naga
yanayinsa.Batare da wata
gardamar ba kuwa sai
Andalu ya ratsa ya baiwa su
Yazirina hanya suka
wuce cikin sannan ya janyo kofar
gidan ya rufe ya
maida sakatun kuma yasa kuba ya
dada kulleta yana
mai murda kubar har sau uku
kamar yadda yayi a
farko.Yazirina na shiga cikin gidan
ta tsinci kanta a
cikin wani babban falo,ashe
mutane ne da yawa a
zazzaune maza da mata ana ta
shaye shaye na
giya,lemo iri iri wasu kuwa hayakin
taba suke ta
faman busawa,kallo daya zaka
yiwa gaba dayan
mutanen gidan ka gane cewa
dukkaninsu yan bariki
ne muma dukkanin matan karuwai
ne babu
mutuniyar kirki gaba daya a
cikinsu.A gefe daya
kuma teburin yan caca ne suna
tayin cacar
tasu,daga can bangaren yamma
kuma sai suka
hango wasu majiya karfi mutum
biyu zaune a kan
wani tebur sun hada hannaye suna
gwada yar kwanji
jama'a sun kewaye su suna yi musu
tafi da shewa
kowannensu ya dage iya karfinsa
domin yaga ya
sami nasarar danna hannun dan
uwansa izuwa
kasa.Koda Yazirina ta dubi mafi
girman surar karfi
daga kartin biyu sai taji bata yarda
dashi
musamman datayi la'akari da irin
kallon da yayi
musu ita da Mujahid amma sai ta
basar suka wuce
ta gabansu suna bin Andalu a baya
yayin da suka
hau kan wata matattakalar bene
suka hau can sama
inda dakunan gidan suke burjik har
suka iso kofar
wani daki dake can kuryar
karshe.Take Andalu ya
zaro wata kuba dake cikin aljihunsa
ya mikawa
Mujahid,Mujahid na karbar kubar
saiya zurata cikin
kofar ya kunna kai cikin murna.Ita
kuwa Yazirina
saita waigo tana mai lekawa kasan
benen,akawai sai
taga ahe gaba dayan mutanen
dake kasan benen
sun tsayar da duk abinda sukeyi
sun daga
kawunansu sama suna
kallonsu.Koda ganin Haka sai
Yazirina tayi tsaki tace nifa babu
abinda na tsana
sama da a rinka kallona,kuma babu
abinda nafi so
sama da sirri,kai Andalu na wane
kudin gaba dayan
dakunan gidan nan kuma nawane
kudin duk giyar da
aka sha a yau da sigari zan biyaka
duka yanzu
amma inason ka sallami gaba
dayan mutanen dake
cikin gidan nan su fice ya kasance
daga ni sai
angona domin yaune zamuyi daren
farko na
AMARCINMU.Koda jin wannan batu
sai mamaki ya
kama Mujahid shi kuwa Andalu
tsoro ne ya kama
shi jikinsa ya hau tsuma ya dubi
Yazirina cikin
alamun tsananin firgici yace kiyi
mini rai yake
wannan amarya kiyi sani cewa
mutanen dake cikin
gidan nan a yanzu sune mafi
RASHIN IMANI a garin
nan,idan naje musu da wannan
bukta taki zasu iya
cutar dani kuma keda angon naki
ma ba zaku tsira
da rayuwarku ba.Koda jin haka sai
Yazirina tayi
tsaki tace matsala daya ce kawai
dole ne na kara
asarar kudin da zan biyaka na
barnar da za'ayi maka
a yanzu,tana gama fadin hakan
saita sauko kasa da
sauri daga kan matattakalar benen
a lokacin da
Andalu da Mujahid sukaji cikisu ya
duri ruwa don
sun tabbatar da cewar tashin
hankali za'ayi.Koda
Yazirina ta gama saukowa kasan
matattakalar saita
dubi gaba daya mutanen dake cikin
falon tace
inason kowa ya fice daga cikin
gidan nan yanzun
nan domin na karbe shi haya gaba
daya,wanda duk
ya kara dakika dari da ashirin a
cikin gidan nan
saidai ya fita a karye.Koda jin
wannan batu sai gaba
dayan mutanen suka bushe da
dariya suka rinka
yiwa Yazirina kallon
mahaukaciya.Al'amarin daya
fusata Yazirina kenan jikinta ya
kama tsuma a
lokacin dataji zuciyarta ta kama
tafarfasa kamar zata
kone amma sai ta dake ta tsaya cak
a inda
take.Koda ganin haka sai wannan
narkeken kato
wanda yayi gasar karfi da wani
dazu wato wanda ya
kura mata idanun nan ya mike
tsaye daga kan
kujerar da yake zaune ya
tunkarota.Kan Yazirina na
sunkuye ko dagowa bata yi bare ta
kalleshi har ya
iso daf da ita.Ai kuwa sai ya
yunkura cikin
shammace ya kawo mata wawan
naushi ta gefen
fuskarta,naushi ne irin wanda duk
wanda aka yiwa
shi sai an karya masa kashi,cikin
zafin nama ta
kauce katon ya naushi iska.Kafin
yayi wani yunkuri
ta kama hannun nasa da
hannayenta biyu ta daka
akan cinyarta.Take sautin karyewar
hannun nasa ya
cika falon gidan ya kurma uban
ihun sakamakon
tsananin zafi da zugin da yaji ya
durkushe
kasa.Koda ganin abinda ya faru sai
gaba dayan
sauran mazajen dake gidan suka
zare MAKAMANSU
na yaki suka rugo da gudu suka
afkawa Yazirina da
nufin su gididdibata.Wohoho!abin
mamaki baya
karewa a duniya lokacin da
wadannan mazaje suka
afkawa Yazirina ita kadai sai aka
kacame da
masifaffan yaki ya zamana cewa
suna kai mata SARA
DA SUKA tana kauce dukkan hare
haren nasu ba
tare data rike wani makami
ba.Saita rinka gwabza
musu naushi da bugu tana bazar
dasu kasa kuma
ko mutum yaje kasan bata kyaleshi
face ta take
masa kafa ko hannu ya karye nan
take,komai girman
kato da hannu daya take surarsa ta
dokashi a kas ya
kasa mikewa tsaye.Nanfa ihun
mazaje ya cika gidan
a lokacin data rinka hada musu JINI
da MAJINA
kuma tana kakkaryasu.Koda sauran
karuwai sukaga
irin wannan mumunar barnar da
Yazirina keyi sai
suka firgice suka ruga izuwa kofar
gidan domin su
bude su fice domin sun manta ma
cewa tuni Andalu
ya rufe kofar.Ai kuwa suna ganin
kofar a rufe sai
suka dimauce wasun su basu san
sa'adda suka far
fitsari ba a tsaye wasu kuwa kuka
suka kamayi
saboda tsoron kada Yazirina ta
kakkaryasu kamar
yadda ta karya mazajen gidan.Duk
wannan abu dake
faruwa Andalu da Mujahid
™Abubakar Haleefah Physicist™
nacan sama bene sunki yarda su
sauko kasan
kawai sun zuba na mukiya suna
kallon ikon
Allah,shidai Andalu saboda tsananin
mamaki da
tsoro ma tuni wandonsa ya dade
da jikewa da fitsari
kuma daidai da dakika daya jikinsa
bai daina
karkarwa ba.A hakanne ya dubi
Mujahid yace me
yasa tun farko baka gaya mini
cewa matarka aljana
bace ba mutum ba,da tun a sannan
zan gudu na
bar muku gidan ungo kudinku da
kuka biyani dai
kuyi min rai.Koda jin wannan batu
sai Mujahid yaji
dariya ta kwace masa sannan ya
dubi Andalu yace
kai matata mutum ce kamar kai ba
aljana bace
amma ta musamman ce.Andalu
yace kai koda
mutum ce ina ganin akwai aljanu a
jikinta dubi fa
yadda ta ragargaza komai da kowa
dake cikin gidan
nan,a daidai wannan lokaci ne
gidan yayi tsit baka
jin sautin komai face nishi da koke
koken mazajen
dake kwance a kas.Wadanda gaba
dayansu karyayyu
ne su kuwa sauran matan gaba
dayansu sun cure a
waje daya suna ta kyarma kamar
ace kyat su tsure
da gudawa,gaba daya tebura da
kujerun dake falon
sun kakkarye,tulunan giya sun
farfashe ko ina yayi
kaca kaca kuma babu mahalukin da
yake tsaye a
falon face Jaruma Yazirina kuma
duk wannan dauki
ba dadi da akayi lullubin da
Yazirina tayi bai kwance
ba bare aga fuskarta ko surar
jikinta.Koda Yazirina
taga ta sami wannan nasara sai ta
dubi gaba dayan
karuwan tace kowacce ta dauki
saurayinta ta kaishi
daki tayi jinyarsa bana son mutum
daya ya fita daga
cikin gidan nan har izuwa tsawon
kwanakin da
zanyi.Tana gama fadin hakan sai ta
juya ta hau
matattakalar benen ta isa Inda
Andalu ke tsaye kawai
sai ta fiddo kulli uku manya na
dinare ta cilla masa
ya cafe tace kasa a gyara komai na
gidan nan kamar
wani abu bai faru ba.Kasa tsaro ya
kasance bashiga
ba fita,duk abinda ake bukata na
dangane da abinci
da sauran kayan ciye ciye dana
shaye shaye a kawo
wanda zai ishi kowa har tsawon
kwanaki bakwai da
zanyi a garin nan.Daga yau nice
shugaba a gidan
nan babu abinda za'a zartar saida
izinina,aikata
sabanin hakan ranka ne
fansarsa.Koda gama fadin
hakan sai Yazirina ta dubi Mujahid
tayi masa
murmushi tace Angona mu kara
cikin dakinmu nan
take Yazirina da Mujahid suka shige
cikin wannan
daki na musamman suka banko
kofa.A sannan ne
matan suka fara taimakon mazajen
da Yazirina ta
kakkarya suna tashinsu tsaye suna
shigar dasu cikin
dakunan gidan kuma suka shiga
gyara musu karayar
jikinsu,shi kuwa Andalu tuni ya
kirawo hadimansa
duka yaja musu kunne akan kada
su kuskura su
fitar da labarin abinda ya faru
yanzu a cikin wannan
gidan sannan ya basu kudi suka je
suka siyo
abubuwan da aka lalata a gidan
aka mayar dasu
tamkar wani abu bai taba faruwa
ba,kuma suka je
kasuwa suka siyo kayan abinci da
ababan sha isasu
gami da tulunan giya da kararen
sigari.Lokacin da
Yazirina suka shiga cikin wannan
daki na
musamman sai suka tsinci kansu a
ciki wani dan
kayataccen falo wanda ke dauke da
jan kilishi mai
taushi wanda aka shimfida a kasa
gami da jajayen
kujeru da kuma jajayen labulaye.A
takaice dai komai
dake cikin falon launin ja gareshi
akwai dakunan
barci guda biyu a cikin falon sai
kuma kewaye guda
daya.Yazirina taje ta zauna akan
doguwar kujera
tana mai sauke jakar guzurinta a
kusa da ita sannan
ta dubi Mujahid fuskarta a murtuke
tace zaka kwana
a cikin dakin ni kuma nan falon
zanyi barcina.Koda
jin wannan batu sai Mujahid ya
dubeta cikin alamun
tsoro yace haba ya shugabata kin
sani cewa yanzu
kin kara gaiyato mana abokan
gaba sakamakon
kakkarya mazajen gidan nan da
kikayi kira tara
musu gajiya.Ni gaskiya tsoro nakeji
nayi nesa dake
domin bazan iya kare kaina
ba.Kafin Mujahid ya
gama rufe bakinsa sai Yazirina ta
tari numfashinsa
tana mai daka masa tsawa tace
kada ka raina mini
hankali mana,dacan wanene yake
kareka daga
dukkan irin hadarin da kake shiga a
lokacin da kake
yawon satarka?Mujahid ya gyada
kai yace ai wannan
karon an turo nine na sato abinda
yafi komai hadari
a duniya wato Taswirar zuwa
kogon Taskar Ajali
kuma masu farautar wannan
Taswira guda uku
manyan bokaye ne da manyan
sarakuna ababen
tsoro.Koda jin wannan batu sai
Yazirina ta bushe da
dariya sannan tace ni kuwa ko
kadan bana
shakkarsu amma ina shakkar wata
mace yar uwata
guda daya wadda a koyaushe zata
iya baiyana a
cikin wannan duniya ana kiranta da
suna JARUMA
SARILA.Cikin tsananin alamun
mamaki Mujahid ya
dubi yazirina yace yanz kina nufin
kice akwai wata
jaruma wadda ta fiki jarumtaka da
hadari a cikin
jaruman duniya?Yazirina ta gyada
kai tace kwarai
kuwa kuma baiyanarta a cikin
duniya daidai yake da
baiyanar GOBARA DAGA KOGI wacce
babu abinda
zai iya kasheta,inda ace itace ta
shigo wannan gida
yau dinnan da tuni ta kashe kowa
saboda batada
tausayi ko kadan,zata rinka
farautata kamar yadda
mai fama da kishi ke neman ruwan
sha ba don
komai ba sai domin ta rabani da
taswirar zuwa
kogon Taskar Ajali guda biyu dake
hannuna.Koda jin
wannan batu sai mamaki ya sake
turnuke Mujahid
yace au dama daya Taswirar ma ta
biyu na
hannunki.?
Nima dai na tsaya anan saboda
tsananin Al'ajabi da
mamakîn Jarumtakar Jaruma
YAZIRINA.